Isra'ila ta ƙaddamar da matakin farko na farmakin mamaye Gaza

Wasu mutane na guduwa bayan wani hari ya faɗa kan wani gini da ke bayansu

Asalin hoton, AFP via Getty Images

    • Marubuci, Yolande Knell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East Correspondent
    • Marubuci, David Gritten & Gabriela Pomeroy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 6

Jami'ai a birnin Gaza sun ce Falasdinawa na ficewa daga sassan birnin bayan da sojojin Isra'ila suka ƙaddamar da matakin farko na farmakin da suke kai wa ta ƙasa.

Sojojin Isra'ila sun kafa wani sansani a wajen birnin - inda Falasɗinawa sama da miliyan ɗaya ke zama - bayan shafe kwanaki ana kai hare-haren bama-bamai da manyan bindigogi.

Hakan ya sa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya sabunta kiraye-kirayen a tsagaita wuta cikin gaggawa "don guje wa mutuwa da ɓarna".

Isra'ila na son nuna alamun cewa tana ci gaba da shirinta na ƙwace iko da birnin Gaza baki ɗaya duk da sukar da ta ke fuskanta daga ƙasashen duniya.

Ɗaruruwan Falasɗinawa a yankunan Zeitoun da Sabra na birnin Gaza sun yi gudun hijira zuwa yankin arewa maso yammacin birnin.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ya ce tuni dakarun ƙasar suka fara aiki a yankunan Zeitoun da Jabalia domin share fagen kai farmakin, wanda ministan tsaron Isra'ila, Isreal Katz ya amince da shi a ranar Talata, wanda kuma za a gabatar wa majalisar ministocin tsaro nan gaba a cikin wannan makon.

Kimanin dakarun ko-ta-kwana guda 60,000 ne aka fara kira daga yanzu zuwa farkon watan Satumba don tabbatar da an samu isassun sojojin da za su gudanar da aikin.

Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce yana bayar da gajeren wa'adin ƙwace abin da ya bayyana a matsayin "yakunan ƙarshe da ke ƙarƙashin ikon ƴan ta'adda'' a Gaza.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta zargi shugaban na Isra'ila da ci gaba da "yaƙar fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a cikin birnin Gaza" tare da sukar abin da ta kira nuna halin ko-in-kula kan sabon daftarin yarjejeniyar tsagaita da masu shiga tsakani na yankin suka gabatar.

Har yanzu Isra'ila ba ta mayar da martani a hukumance kan daftarin ba.

Ana tunanin za a bai wa Falasɗinawa da ke birnin Gaza umarnin ficewa kuma su nufi yankin kudancin Gaza a daidai lokacin da ake shirye-shiryen ƙaddamar da shirin Isra'ila na mamaye yankin.

Da yawa daga cikin ƙawayen Isra'ila sun yi Alla- wadai da shirin nata, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi gargaɗi a ranar Laraba cewa "wannan lamari babu abin da zai haifar illa bala'i kan al'ummomin biyu da kuma haɗarin jefa yankin gaba ɗaya cikin wani yanayi na yaƙin dindindin".

Ƙungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) ta ce ci gaba da gudanar da abubuwan da ke haifar da gudun hijira da kuma ƙaruwar tashe-tashen hankula "na iya ƙara ta'azzara mawuyacin halin da al'ummar Gaza miliyan 2.1 ke ciki''.

Gwamnatin Isra'ila ta bayyana aniyarta ta mamaye yankin zirin Gaza baki ɗaya bayan tattaunawar kai tsaye da ƙungiyar Hamas kan batun tsagaita wuta da kuma yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su ta wargaje a watan jiya.

Da yake magana a wani taron manema labarai, mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila, Birgediya Janar Effie Defrin, ya ce Hamas ta "sha kashi" bayan yaƙin watanni 22.

Ya ƙara da cewa "Za mu zurfafa ɓarnar da mu ka yi wa Hamas a birnin Gaza, wadda ita ce cibiyar gudanarwa ta fannin shugabanci da kuma sojin wannan ƙungiyar ta ƴan ta'adda'' .

Ya kuma ƙara da cewa "Za mu zurfafa lalata kayayyakin ayyukan ta'addanci a sama da ƙasa da kuma yanke dogaro da al'ummar ke yi kan Hamas."

Amma Defrin ya ce IDF "ba za ta jira" kafin ƙaddamar da aikin ba.

"Mun fara matakin farko, kuma a yanzu haka, dakarun IDF na riƙe da wajen birnin Gaza."

Ya ƙara da cewa, bataliya biyu na aiki a ƙasa a unguwar Zeitoun, inda a ƴan kwanakin nan suka gano wani ramin ƙarƙashin ƙasa da ke ɗauke da makamai, kuma bataliya ta uku na aiki a yankin Jabalia.

A cewarsa a yunƙurinsu na kiyaye fararen hula, za a gargaɗi al'ummar birnin Gaza da su fice domin kare lafiyarsu.

Kakakin hukumar tsaron farar hula ta Hamas, Mahmoud Bassal ya shaida wa kamfanin dilancin labarai na AFP cewa lamarin na da matuƙar haɗari a yankunan Zeitoun da Sabra na birnin.

Hukumar ta bayar da rahoton cewa, hare-haren da Isra'ila ta kai da kuma gobara da suka tashi sakamakon hakan sun kashe mutum 25 a faɗin yankin a ranar Laraba.

Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da yara uku da iyayensu da aka jefa wa bam a gidansu da ke yankin Badr na sansanin ƴan gudun hijira na Shati da ke yammacin birnin Gaza.

Defrin ya ce, rundunar ta IDF tana kuma yin duk mai yiwuwa don hana cutar da Isra'ilawa 50 da Hamas ke ci gaba da yin garkuwa da su a Gaza, waɗanda 20 daga cikinsu ake kyautata zaton suna raye.

Iyalan su sun bayyana fargabar cewa waɗanda ke birnin na Gaza na iya fuskantar barazana idan har aka kai farmakin ta ƙasa.

Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross (ICRC) ta yi gargaɗin cewa Falasɗinawa fararen hula da kuma waɗanda aka yi garkuwa da su na iya fuskantar bala'i idan har aka tsananta ayyyukan sojin da ake yi a Gaza.

"Bayan kwashe watanni ana tashin hankali da ya haddasa gudun hijira, mutanen Gaza sun yi matuƙar gajiya. Ba matsin lamba ne su ke buƙata ba yanzu, suna buƙatar samun sauƙi ne. Ba ƙarin tsoro da fargaba ba, amma damar su ɗan sha iska. Dole ne sun samu damar yin amfani da abubuwan da suka dace don rayuwa cikin mutunci: abinci, magunguna da kayan tsaftace jiki da muhalli, da ruwa mai tsafta, da matsuguni mai aminci, "in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa "Duk wani ƙarin tsananta ayyukan soji zai ƙara zurfafa wahalhalu, da rarraba iyalai, da kuma yin barazana ga rikicin jin ƙai da ba za a iya jurewa ba.

Har ila yau, rayukan waɗanda aka yi garkuwa da su na iya shiga cikin haɗari."

Ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa da kuma shigar da kayayyakin jin ƙai cikin gaggawa ba tare da cikas ba a faɗin Gaza.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma yi kira da a saki mutanen da ƙungiyar Hamas ta yi garkuwa da su ba tare da wani sharaɗi ba.

Masu shiga tsakani, Qatar da Masar na ƙoƙarin tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta inda suka gabatar da wani sabon daftarin tsagaita wuta na kwanaki 60 da kuma sako kusan rabin mutanen da aka yi garkuwa da su, daftarin da Hamas ta ce ta amince da shi a ranar Litinin.

Har yanzu dai Isra'ila ba ta gabatar da wani martani a hukumance ba, amma jami'an Isra'ila sun dage a ranar Talata cewa ba za su sake amincewa da duk wata ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniya ba, kuma sun buƙaci a samar da cikakkiyar yarjejeniyar da za ta sa a sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a lokaci guda.

A cewar wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito ranar Laraba, Hamas ta zargi Netanyahu da yin watsi da daftarin tsagaita wutan da masu shiga tsakani suka gabatar, kuma ta ce shi ne "mai kawo cikas ga duk wata yarjejeniya".

Sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da yaƙin Gaza ne a matsayin martani kan harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila a ranar 7 ga Oktoban 2023, inda aka kashe mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da wasu 251.

Aƙalla mutane 62,122 ne aka kashe a Gaza tun daga lokacin, a cewar ma'aikatar lafiya ta yankin.

Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomi na amfani da alƙaluman ma'aikatar a matsayin alƙaluma mafi inganci da ake samu kan waɗanda suka mutu.