Tsohon ɗan wasan Man United Forlan zai fara buga gasar ATP Tennis

A

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon ɗan wasan Manchester United Diego Forlan zai fara wasansa na kwallon Tennis a matsayin kwararren ɗan wasan a wasan mutum biyu da za a yi a watan gobe a Uruguay.

Mai shekara 45 ɗin, wanda ya yi murabus a 2019, zai buga wasan ne tare da takwaransa na Argentina Federico Coria a gasar Uruguay Open a Montevideo.

Forlan wanda ke da sha'awar wasan Tennis tun yana yarinta, yana buga ITF Masters - ajin shekara 45 zuwa sama.

Amma wasan da za a yi a watan gobe na ATP zai buƙaci Forlan ya mallakin katin manyan 'yan wasa masu buga gasa.

Takwaransa Coria shi ne na 101 cikin jadawalin 'yan wasan Tennis, inda ya kai matsayi na 49 a 2023.

Forlan ya koma Manchester United a 2002 ya buga wasa 98 kafin daga baya ya koma Villarreal da ke La Liga.

A Spain, ya lashe kyautar wanda ya fi kowa cin kwallaye Golden Shoe - har sau biyu.

Dan wasan gaban ya ci kwallon da ta fi kowacce a gasar Kofin Duniya ta 2010 wanda aka yi a Afrika ta Kudu, lokacin da Uruguay ta kammala gasar a ta uku, ya kuma taimaka wa ƙasarsa ta lashe gasar Copa America a 2011.