Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Musulmai 10 da suka riƙe muƙamai a ƙasashen Yamma
A ranar Alhamis ne aka rantsar da magajin garin birnin New York, Zohran Momdani a hukumance domin jan ragamar al'amuran gudanar da birnin.
Mista Momdani ya kasance ɗaya daga cikin fitattun musulmai da suka riƙe muƙamai a ƙasashen yamma, wani abu da ke ci gaba da ɗaukar hankali.
Wasu mutane na alaƙanta hakan da samun karɓuwa da Addinin Masulunci ke yi a ƙasashen, yayin da wasu kuma ke alaƙanta hakan da yancin addini da ƙasashen ke bayarwa.
Baya da Zohran Momdani akwai wasu musulmai da suka riƙe muƙamai a ƙasashen yamma.
A cikin wannan muƙala mun zaƙulo wasu musulmai da suka samu zarafin riƙe muƙamai a ƙasashen yamma.
Zohran Momdani
A ranar 1 ga watan Janairun 2026 ne aka rantsar da Zohran Mamdani a matsayin Magajin garin New York.
Ya kafa tarihin zama Musulmi na farko da ya riƙe ofishin sannan kuma mafi ƙarancin shekaru da ya riƙe kujerar a cikin fiye da shekara 100.
A watan Nuwamba ne dai matashin mai shekara 34 ya kafa tarihi inda ya lashe zaɓen zama Magajin garin na birnin New York.
An haifi Mamdani a Kampala, Uganda. Ya koma New York tare da iyalinsa yana da shekara bakwai.
Ya yi karatu a makarantar fasaha ta Bronx sannan ya yi digiri kan nazarin ƙasashen Afirka da ake kira "African Studies" a makaratar Bowdoin, inda ya taimaka kafa kungiyar "ɗalibai da ke neman adalci ga Falasdinu".
Wannan matashin ɗan siyasa mai ra'ayin cigaba wanda ya zama Musulmi na farko kuma ɗan Kudancin Asiya na farko da zai mulki birnin yana alfahari da asalinsa.
Ilhan Omar
Ilhan Omar ta kafa tarihi a watan Nuwamban 2018 lokacin da ta zama Musulma mace ta farko da suka lashe kujerun majalisar wakilai a tarihin Amurka.
Ƴar asalin Somaliya ta kasance mamba a jam'iyyar Democrat kuma ta dace da irin siyasar kawo sauyi da jam'iyyar ke cewa tana yi.
Ilhan ta kasance ɗaya daga cikin matan da suka yi fice wajen adawa da manufofin shugabannin Amurka musamman kan batun Falasɗinawa.
Matashiyar mai shekara .... na da farin jini tsakanin matasa da mata a fadin duniya.
Takan nuna goyon baya ga dokokin 'yancin ɗan'adam, ciki har da na zubar da ciki da kuma goyon bayan masu zuwa ci-rani.
Rashida Tlaib
Kamar dai Ilhan, ita ma Rashida a lokaci guda suka zama ƴan majalisa a Amurka, bayan laashe zaɓe a 2018.
Duka matan biyu na matukar sukar yadda Isra'ila take muzguna wa Falasdinawa, kuma su kadai ne 'yan majalisar da suka fito karara suka nuna goyon baya ga kungiyar Falasdinawan da ke jagorantar kaurace wa Isra'ila.
Wannan ya kuma sa Tlaib da Omar sun zamo 'yan majalisun Amurka na farko da aka hana shiga Isra'ila.
Hakan ya sha banban da takwarorinsu 72 da suka shafe wata guda suna wata ziyara a Isra'ila wacce masu neman kamun-kafa suka shirya kuma suka dauki nauyi.
Ba'amurkiyar ƴar asalin Falasɗinu ta samu nasarar kasancewa ƴar majalisar wakilai daga jihar Machigan.
Asalin iyayenta ƴan ci-rani ne, inda suka haifeta a Detroit a shekarar1976, kuma ta kasance ƴar fari cikin ƴan'uwan 14 da iyayenta suka haifa.
A shekarar 1998 ne ta kammala karatu a Jami'ar Wayne State University, bayan ta karanta fannin kimiyyar siyasa.
Sadiq Khan
Sir Sadiq Aman Khan ya kasance magajin garin birnin London tun 2016.
Ya kasance mamba a jam'iyyar Labour Party da aka kallo a matsayin mai sassauci.
Sadiq Khan ya fara shiga harkar siyasar Birtaniya, a shekarar 1993 inda ya zama kansilan Wandsworth a 1994.
A shekarar 2005 akaq zaɓe shi matsayin ɗan majalisar, inda ya yi fice wajen sukar mjuradun gwamnatin Tony Blair, ciki har da mamayar Iraƙi a 2003 da kuma sabuwar dokar yaƙi da da ta'addanci.
Bayan saukar Blair, magajinsa Gordon Brown ya naɗa Khan babban sakataren ƙananan hukumomi a 2008, kafin daga baya a naɗa shi ministan sufuri.
A shekarar 2016 ne kuma ana zaɓe shi matsayin magajin garin birnin London, sannan ya yi murabus a matsayin dan majalisa.
Iyayen Khan ƴan asalin Pakistan ne, yayin da shi kuma suka haife shi a birnin London.
Mista Khan ya karanta fannin Shari'a a Jami'ar Arewacin London.
Lateefah Simon
A watan Janairun 2025 ne Lateefah Aaliyah Simon ta zama ƴar majalisa ta 12 daga jihar California.
Ƴar jam'iyyar Democrats ta kasance musulma ta farko da ta wakilci jihar California da ma yankin yammacin tsakiyar Amurka a majalisar wakilan Amurka.
Simon ta kasance mai yawan sukar hare-haren sojojin Isra'ila a Gaza, tare da sukar taimakon kuɗi da na soji da Amurka ke bai wa Isra'ilar.
An haife ta sannan ta taso a yammacin birnin San Francisco, inda ta yi karatunta na sakandire birni Washingto.
Keith Ellison
Keith Maurice Ellison fitaccen lauya ne Ba'amurke da ke riƙe da matsayin babban atoni janar jihar Minnesota.
Ellison ya kasance ɗan majalisar wakilai daga jihar Minnesota daga shekarar 2007 zuwa 2019.
A shekarar 1982 ne Mista Ellison ya karɓi musulunci, inda ya zama musulmi na farko daga jihar Minnesota da ya riƙe muƙamin ɗan majalisar wakilan Amurka.
Anas Sarwar
Anas Sarwar ya kasance shugaban jam'iyyar Labour a yankin Scotland da ke Birtaniya tgun 2021.
A baya taɓa riƙe muƙamin ɗan majalisar dokokin yankin Scotland daga 2010 zuwa 2015.
Iyayensa ƴan asalin Pakistan ne, yayain da suka haife shi a birnin Glasgow na ƙasar Scotland, inda a nan ne ya yi karatunsa.
Aydan Özoğuz
Aydan Özoğuz, Bajamushiya ƴar asalin Turkiya ta kasance mace ta farko musulma da ta samu shiga ƙunshin gwamnatin tarayyar Jamus.
A watan Disamabn 2013 ne tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ce ta naɗa Ms Özoğuz matsayin ƙaramar ministar kula da ƴan ci-rani da ƴangudun hijira.
Yanzu haka tana riƙe da muƙamin mataimakiyar shugaban majalisar zartar da dokokin gwamnatin tarayyar ƙasar.
Rachida Dati
A ƙarshen 2024, gwamnatin Faransa ƙarƙashin firaminitan ƙasar, Sébastien Lecornu ta shigar da wasu musulmai ƴan asalin Moroko.
Cikin waɗanda aka naɗa matsayin ministoci har da Rachida Dati, wadda ta samu matsayin mkinistar al'adu.
A baya ma ta riƙe muƙaman ministoci da suka haɗa da ministar shari'a karƙashin gwamnatin Nicolas Sarkozy.
Mustafa Hamed Mohamed
Mustafa Hamed Mohamed fitaccen ɗansiyasa ne a Sifaniya da ya kafa tarihin zama musulmi na farko da ya riƙe muƙamin magajin garin birnin Sifaniya.
Inda ya jagoranci gwamnatin birnin daga watan Yulin 1999 zuwa Yulin 2000.
A yanzu haka shi ne shugaban ƙawancen jam'iyyun hamayya na birnin.
Sai dai siyasarsa na cike da batutuwan da suka shafi shari'a, ciki har da kamawa da tsarewa kan abubuwan da suka shafi zargin sayen ƙuri'u a 2021 da 2024.