Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Zohran Mamdani, Musulmi na farko Magajin garin birnin New York?
- Marubuci, Nada Tawfik and Rachel Hagan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, New York City & London
- Lokacin karatu: Minti 6
A ranar 1 ga watan Janairun nan na sabuwar shekarar 2026 aka rantsar da Zohran Mamdani a matsayin Magajin garin New York, inda ya kafa tarihin zama Musulmi na farko da ya riƙe ofishin sannan kuma mafi ƙarancin shekaru da ya riƙe kujerar a fiye da ƙarni.
Ya kasance Magajin garin na New York na 111 kuma alƙalin alƙalan birnin, Letitia James ce ta jagorancin bikin rantsarwar a farkon daren ranar 1 ga sabuwar shekarar 2026.
A watan Nuwamba ne dai matashin mai shekaru 34 ya kafa tarihi inda ya lashe zaɓen zama Magajin garin na birnin New York.
Zaɓen bana ya jawo hankalin jama'a sosai. Mamdani, mai shekaru 34, wanda dan majalisar dokoki ne a jihar New York inda ya fara shekarar ba tare da sanin jama'a sosai ba, amma daga baya ya zama sananne.
Wannan nasara tana nuna sabon salo ga masu ra'ayin cigaba, kuma tana nuna sauyin tunanin siyasa a birnin.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga jama'a ka da su zabi Mamdani, maimakon haka ya mara baya ga tsohon gwamna Andrew Cuomo wanda ya tsaya takara a matsayin mai zaman kansa bayan ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na Democrat.
"Ko kuna son Andrew Cuomo ko ba ku son shi, ba ku da wani zabin da ya fi shi. Ku zabe shi, ku yi fatan zai yi aiki mai kyau," Trump ya rubuta a shafinsa na Truth Social a daren Litinin. "Shi zai iya wannan aikin, Mamdani ba zai iya ba!"
Cuomo, wanda ya taɓa taka rawar gani a siyasar jihar, ya ce game da goyon bayan da Trump yake nuna masa, "Ba komai bane illa kawai saboda yana adawa da Mamdani ne."
Trump ma ya ƙi marawa dan takarar Republican Curtis Sliwa baya, wanda ya zo na uku, inda ya ce: "idan har kuka zaɓi Curtis Sliwa tamkar Mamdani kuka zaɓa."
Tarihin Mamdani
An haifi Mamdani a Kampala, Uganda. Ya koma New York tare da iyalinsa yana da shekara bakwai. Ya yi karatu a makarantar fasaha ta Bronx sannan ya yi digiri kan nazarin ƙasashen Afirka da ake kira "African Studies" a makaratar Bowdoin, inda ya taimaka kafa kungiyar "ɗalibai da ke neman adalci ga Falasdinu".
Wannan matashin ɗan siyasa mai ra'ayin cigaba wanda zai zama Musulmi na farko kuma dan Kudancin Asiya na farko da zai mulki birnin yana alfahari da asalinsa.
Ya wallafa wani bidiyon yaƙin neman zaɓe gaba ɗaya a harshen Urdu tare da hotunan fina-finan Bollywood, sannan kuma ya sake yin haka a wani bidiyo inda yake magana da harshen Spanish.
Mamdani da matarsa Rama Duwaji, ƴar shekara 27 wadda ƙwararriya a fasahar zamani kuma 'yar asalin kasar Siriya da ke zaune a Brooklyn, sun haɗu ne a manhajar haɗuwar masoya ta Hinge.
Mahaifiyarsa, Mira Nair, sananniyar daraktar fina-finai ce, mahaifinsa kuma Farfesa Mahmood Mamdani, malami ne a jami'ar Columbia. Duka biyun sun yi karatu a Harvard.
Mamdani ya kasance yana yawan gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar al'umma kuma jagora.
A bayaninsa na majalisar jiha, ya ce: "Rayuwa ta kai ni wurare daban-daban da suka haɗa da harkar fim da waƙa da rubutu – amma kuma yanayin al'umma ne ya sa abubuwan da ke faruwa a duniya ba su dame ni ba, sai dai su motsa ni in yi aiki."
Kafin ya shiga siyasa, ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga masu gidaje, yana taimakawa talakawa masu gidaje a Queens su kare kansu daga fitar da su daga gidajensu.
Ya kuma bayyana addininsa a matsayin Musulunci a fili cikin yaƙin neman zaɓensa. Yana ziyartar masallatai akai-akai kuma ya fitar da wani bidiyon yaƙin neman zaɓe a harshen Urdu game da tsadar rayuwa a birnin.
"Babu wani dan takara da yake wakiltar dukkan matsalolin da nake matukar damuwa da su a halin yanzu, sai dai Zohran," in ji Jagpreet Singh, daraktan siyasa na kungiyar DRUM mai fafutukar adalci, a hirarsa da BBC.
Alƙawura da Mamdani ya yi wa New York
Mamdani ya ce masu zabe a birnin da ya fi tsada a Amurka, suna son jam'iyyar Democrat ta mayar da hankali kan rage tsadar rayuwa.
"Wannan birnin ne inda mutum daya cikin huɗu ke rayuwa cikin talauci, inda rabin miliyan na yara ke kwanciya da yunwa kowace dare," in ji shi a wani taro da BBC ta halarta.
Ya gabatar da shawarwari kamar:
- Samar da sufurin manyan motoci kyauta a duk fadin birnin New York.
- Dokokin hana ƙara kuɗaɗen haya da sa ido kan masu gidajen haya da ke karya dokoki.
- Buɗe shagunan abinci mallakar birni da farashi mai sauƙi.
- Kula da yara daga ƴan makonni 6 har zuwa shekara 5 kyauta.
- Ninka ginin gidajen haya masu sauƙi sau uku, musamman wadanda ƙungiyoyin ma'aikata suka gina.
Masu suka suna tambaya kan ƙwarewarsa
Cuomo da wasu sun bayyana Mamdani a matsayin wanda bai da ƙwarewa kuma mai tsatsauran ra'ayi sosai a birni mai kasafin kuɗi na dala biliyan 115 da ma'aikata sama da 300,000.
Cuomo, wanda manyan masu bada tallafi suka goyo wa bayan, ciki har da Bill Clinton, ya ce ƙwarewa tana da muhimmanci. Ya ce: "Ƙwarewa da iya aikin da sanin yadda ake gudanar da aiki da sanin yadda ake mu'amala da Trump da sanin yadda ake mu'amala da Washington da sanin yadda ake mu'amala da majalisar jihar, su ne abubuwan asali da ya kamata an ce ana da ƙwarewa a kai.
Amma Trip Yang, wani masani kan siyasa, ya ce "ƙwarewa" ba lallai ne ta zama abu mai canza wasa a wannan zamani na siyasa ba. Kuma ko Mamdani ya ci ko bai ci ba, Mr Yang yana ganin yaƙin neman zabensa ya yi abin da mutane ba su zata ba.
"Zohran yana samun goyon baya daga dubban masu sa kai, da ɗaruruwan dubban masu bada gudummawa na musamman. Ba kasafai ake ganin irin wannan sha'awar masu sa kai da al'umma a yaƙin neman zaben Democrat na gida a New York ba," in ji shi.
"Ya kasance yana fahimtar mu. Yana cikin mu. Ya fito daga al'ummarmu wato al'ummar 'yan cirani," in ji mai goyon baya Lokmani Rai.
Isra'ila da Falasɗinu
A wani taron yaƙin neman zaɓen Mamdani a Jackson Heights, inda al'umma ke da bambance-bambancen ƙabilu an ga yara suna wasa, yayin da 'yan kasuwar abinci na Latino ke sayar da ice cream da kayan ciye-ciye.
Wannan ya nuna bambancin birnin, wanda 'yan Democrat ke ganin shi ne babban abin alfahari na New York.
Amma birnin bai rasa matsalolin nuna wariyar launin fata da zaman ɗarɗar na siyasa ba.
Matsayin 'yan takara kan rikicin Isra'ila da Gaza shi ma yana cikin abin da masu zabe ke tunani.
Mamdani ya kasance yana goyon bayan Falasdinu sosai kuma ya soki Isra'ila, wanda ya sa ya sha bamban da yawancin shugabannin jam'iyyar Democrat.
Dan majalisar ya gabatar da dokar kawo karshen matsayin rangwamen haraji ga ƙungiyoyin agaji na New York da ke da alaƙa da matsugunan Isra'ila da ke karya dokokin hakkin bil'adama na duniya.
Ya kuma ce ya kamata a kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.
An tambaye shi sau da dama a jaridu ko yana goyon bayan Isra'ila a matsayin ƙasa ta Yahudawa, inda ya ce: "Ba na jin daɗin goyon bayan kowace ƙasa da ke rarraba 'yan kasa bisa addini ko wani abu, ina ganin kamar yadda muke a wannan ƙasa, daidaito ya kamata ya kasance a kowace ƙasa a duniya. Wannan shine ra'ayina."
Cuomo a gefe guda ya bayyana kansa a matsayin "mai goyon bayan Isra'ila sosai kuma yana alfahari da hakan."
A wasu fannoni, matsalolin da 'yan Democrat ke fuskanta a New York suna kama da na zaɓen gaba, kuma bayan zaben fidda gwani, za a iya nazarin sakamakon a ƙasa baki ɗaya don fahimtar matsayin jam'iyyar da yadda ya kamata ta fuskanci Trump.