Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ra'ayi Riga: Kan ficewar ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas
Lokacin karatu: Minti 1
Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan fitar ƙasashen Sahel uku wato Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, bayan kwashen fiye da shekara guda ana zaman tankiya, lamarin da ya kasance wata babbar koma-baya da kuma jefa rashin tabbas ga ɗorewar Ecowas.
Shin me hakan ke nufi ga makomar Ecowas, da ma ƙasahen AES? Yaya wannan lamari zai shafi batun tsaro da tattalin arziƙin ɗaukacin yanki?
Batutuwan da shirin ya tattaunawa kansu ke nan