Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan wasan Liverpool da Real Madrid
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 8
Liverpool za ta karɓi bakuncin Real Madrid a wasa na huɗu na cikin rukuni a gasar Zakarun Turai ta Champions League a filin wasa na Anfield ranar Talata. Me kuke son sani kan fafatawar?
Biyu daga cikin manyan ƙungiyoyin nahiyar Turai da ke da ɗumbin tarihi a babbar gasar zakarun Turai, waɗanda ke da kofin 21 tsakaninsu.
Ƙungiyar Sifaniya mai Champions League 15 za ta je Anfield, bayan doke Valencia 4-0 a La Liga ranar Lahadi, kuma ita ce ta ɗaya a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Liverpool mai kofin zakarun Turai shida ta ɗan yi fama da kalubale, wadda ta yi rashin nasara shida daga wasa takwas baya a dukkan karawa.
Sai dai kuma ta yi nasara a kan Aston Villa ranar Asabar a Premier League da ci 2-0, tana kuma ta uku a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.
A kadawalin gasar Champions League, bayan karawa uku-uku a cikin rukuni, Real Madrid na a matsayi na biyar da maki tara, ita kuwa Liverpool tana a matsayi na 10.
Wasan ƙarshe da suka fuskanci juna
Liverpool ce ta doke Real Madrid 2-0 a Anfield a wasa na biyar a bara, inda Alexis Mac Allister da kuma Cody Gakpo suka ci mata ƙwallayen.
A karawar ce Kylian Mbappe da kuma Mohamed Salah kowanne ya ɓarar da fenariti, kuma a wasan ne ƙungiyar Anfield ta kawo karshen rashin nasara takwas a hannun Real Madrid, kenan da canjaras ɗaya aka doke ta bakwai.
Ƙungiyar da ke buga Premier League ta yi nasarar cin Real Madrid 1-0 a wasan karshe a European Cup a 1981.
Sai dai ƙungiyar Sifaniya ta doke Liverpool karo biyu a wasan karshe a Champions League a kakar 2018 da ci 3-1 da kuma 2022 da yin nasara 1-0, inda Vinicius Junior ya ci ƙwallon a Stade de France.
Wasa biyu kadai Liverpool ta yi rashin nasara daga karawa 15 baya a cikin rukuni a Champions League tsakaninta da ƙungiyoyin Sifaniya da cin wasa bakwai da canjaras shida har da lashe biyar baya a jere.
A bana ne Liverpool ta doke Athletico Madrid 3-2 a wasan farko a cikin rukuni a bana, kana karo na uku a jere da ta ci wata ƙungiya daga Sifaniya a jere.
Wasa biyu Real Madrid ta yi nasara daga tara a baya da ta fuskanci ƙungiyoyin Ingila da canjaras uku da rashin nasara huɗu - har da wanda Arsenal ta doke Real Madrid 3-0 da 2-1 a kwata fainal a Champions League.
Ƙungiyar Liverpool
Wannan shi ne karo na 17 da Liverpool ke buga Champions League da kai wa zagayen karshe karo biyu daga wasa biyar baya ga ɗaukar kofin a 2005 da kuma 2019 mai shida jimilla.
Ƙungiyar da ke Merseyside ita ce ta ɗaya a kan teburi a sabon fasalin da aka sauya na Champions League da cin wasa bakwai da rashin nasara ɗaya, amma sai Paris St Germain ta yi waje da ita a zagaye na biyu.
Ƙungiyar Real Madrid
Real Madrid tana buga Champions League karo na 30, tarihin da take da shi a yawan buga gasar iri ɗaya da na Barcelona - haka kuma Real ta kai zagayen kwata fainal a wasannin sau 29.
A bara a karkashin Carlo Ancelotti tana ta 11 a teburi, bayan cin wasa biyar da rashin nasara uku, sai Arsenal ta yi waje da ita a kwata fainal da ci 5-1 gida da waje.
Wasu alƙalumma da ya kamata ku sani kan wasan
Liverpool ta ci ƙwallo 498 a European Cup da guda 299 a Champions League.
Liverpool ta lashe wasa 14 a zagayen ƴan 16 a karawar rukuni da rashin nasara biyu da doke Eintracht Frankfurt 5-1 a wasa na uku a cikin rukuni.
Haka kuma ta yi nasara 15 a Anfield da cin ƙwallo biyu ko fiye da haka a karawa 14 baya - haka kuma ba ta yi canjaras ba a fafatawa 29 baya a gasar tun bayan tashi 1-1 da Midtjylland cikin Disambar 2020.
Ita kuwa Real Madrid tana daga ƙungiyar biyar da ta lashe dukkan wasa uku na cikin rukuni a kakar nan.
Jude Bellingham ya buga wasa 49 a Champions League mai shekara 22 da kwana 128 days, watakila ya zama matashin da zai yi karawa 50 a gasar, tarihin da Iker Casillas ke rike da shi mai shekara 22 da kwana 155.
Kylian Mbappe ya ci ƙwallo biyar a Champions League a bana, irin yawan wadda Harry Kane ya zura a raga mai taka leda a Bayern Munich, bayan wasa uku-uku a rukuni.
Wannan shi ne karo na 10 daga wasa 11 a zakarun Turai da Liverpool za ta fuskanci ƙungiya daga Sifaniya kuma na shida a jere a Champions League da ta kara da wadda take daga birnin Madrid.
Ta yi nasara huɗu da canjaras da rashin nasara ɗaya daga wasa shida da ta fuskanci ƙungiya daga Sifaniya a wasan da aka yi a Anfield.
Liverpool na bukatar cin ƙwallo biyu nan gaba domin su cika 500 da ta zura a raga a gasar zakarun Turai a tarihi.
Mohamed Salah zai buga wasa na 200 a Anfield, yana bukatar cin ƙwallo biyu nan gaba su zama 50, zai zama na farko daga Afirka mai wannan ƙwazon.
Dominik Szoboszlai da Virgil van Dijk sun buga wa Liverpool dukkan wasa uku a Champions League a kakar nan da kuma su aka tashi dukkan karawar.
Conor Bradley ba zai yi wa Liverpool wasan da za ta fafata da PSV Eindhoven na gaba ba a gasar zakarun turai da zarar ya karɓi katin gargaɗi.
Watakila Ibrahima Konate ya buga wasa na 50 a gasar zakarun Turai a tarihinsa na taka leda.
Ita kuwa Real Madrid ta yi nasara uku a Champions League a bana, bayan doke Marseille 2-1 a gida da cin Kairat Almaty 5-0 da yin nasara 1-0 a kan Juventus 1-0 a Santiago Bernabeu.
Xabi Alonso zai zama mai horarwa na uku da zai je Anfield karo na biyu a jere a gasar zakarun Turai da ƙungiyu biyu da ban-da ban, wato Bayern Leverkusen da kuma Real Madrid.
Kenan ya bi sahun tarihin Ronald Koeman (Benfica a 2005-06 da kuma PSV Eindhoven a 2006-07) sai kuma Eric Gerets (Galatasaray a 2006-07 da kuma Marseille a 2007-08).
Wannan shi ne karo na 63 da Real Madrid za ta fuskanci ƙungiya daga Ingila da yin nasara 26 da canjaras 16 da rashin nasara 20.
Liverpool da Real Madrid ne kadai da suka kara sau uku a wasan karshe a gasar zakarun Turai a 1981 da 2018 da kuma 2022.
Alexander Arnold zai fuskanci tsohuwar ƙungiyarsa
Wataƙila Trent Alexander-Arnold ya fuskanci tsohuwar ƙungiyarsa Liverpool ranar Talata a Anfield a karon farko tun bayan da ya koma Real Madrid kan fara kakar nan.
Ɗan wasan tawagar Ingila ya ce a koda yaushe akwai ƙaunar Liverpool a zuciyarsa, ƙungiyar da ya fara tun yana ɗan yaro - ya kuma ce magoya baya ba za su harzuka shi ba.
Wanda aka haifa a Liverpool ya fara tun daga makarantar horar tamaula ta Liverpool ta masa - ya kuma lashe Premier League da Champions League da Club World Cup kafin ya koma taka leda a Sifaniya.
Alexander Arnold ya yanke hukuncin ƙin tsawaita yarjejeniyarsa a Liverpool, hakan ya harzuka magoya bayan ƙungiyar, waɗanda suka yi masa ihu a wasan Premier League da cArsenal a watan Mayu, wanda ya ce yana son fuskantar sabon ƙalubale a wata kasar.
Liverpool tana fama da ƙalubale a kakar nan, wadda aka ci wasa shida daga takwas baya a dukkan karawa, sai dai Alexander-Arnold ya ce ba wani ɗan wasan Real Madrid da zai raina ƙungiyar mai rike da Premier League.
Mai shekara 27 ya ce "Wasan zai yi tsauri, yadda za a tarbe mu a filin zai taka rawar gani, amma dai ƙwallon kafa za a buga, kuma sana'ar da muke yi kenan.
"Koda yake ba sa samun sakamakon da suke bukata, amma har yanzu suna kan ganiya, kuma kowa yasan karawar ba za ta zo mana da sauki ba.''
Trent Alexander-Arnold ya koma Real Madrid daga Liverpool kan fara kakar bana.
Mai tsaron bayan ya buga wasa 354 a Liverpool a dukkan karawa a kaka tara a Anfield.
Sha ɗayan farko da ake sa ran za su fara buga wa Liverpool da Real Madrid tamaula
Liverpool: Mamardashvili; Bradley, Konaté, Van Dijk, Robertson; Gravenberch, Mac Allister; Salah, Wirtz, Gakpo; Ekitiké
Masu jinya: Alisson Becker da kuma Frimpong
Ba a da tabbas: Jones (groin), Isak (groin)
Ba zai buga wasan gaba da zarar ya karɓi katin gargaɗi: Bradley
Real Madrid: Courtois; Alexander-Arnold, Éder Militão, Huijsen, Carreras; Valverde, Tchouaméni; Arda Güler, Bellingham, Vinícius Júnior; Mbappé
Masu jinya: Carvajal da Rüdiger da kuma Mastantuono
Ba a da tabbas: Alaba
To sai dai Real Madrid ta bayyana ƴan wasan da ta je da su Anfield:
Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.
Masu tsare baya: Militão, Trent, Asencio, Á. Carreras, Fran García, F. Mendy da kuma Huijsen.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Arda Güler da kuma D. Ceballos.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Endrick, Mbappé, Rodrygo, Gonzalo da kuma Brahim.
Wasannin da aka buga tsakanin Liverpool da Real Madrid
Liverpool da Real Madrid sun kara sau 12, Real Madrid ta yi nasara bakwai da canjaras ɗaya, Liverpool ta ci wasa huɗu daga ciki.
Kakar 2024/2025
Champions League ranar Laraba 27 ga watan Nuwambar 2024
- Liverpool 2 - 0 Real Madrid
Kakar 2022/2023
Champions League ranar Laraba 15 ga watan Maris 2023
- Real Madrid 1 - 0 Liverpool
Champions League ranar Talata 21 ga watan Fabrairun 2023
- Liverpool 2 - 5 Real Madrid
Kakar 2021/2022
Champions League ranar Asabar 28 ga watan Mayun 2022
- Liverpool 0 - 1 Real Madrid
Kakar 2020/2021
Champions League ranar Laraba 14 ga watan Afirilun 2021
- Liverpool 0 - 0 Real Madrid
Champions League ranar Talata 6 ga watan Afirilun 2021
- Real Madrid 3 - 1 Liverpool
Kakar 2017/2018
Champions League ranar Asabar 26 ga watan Mayun 2018
- Real Madrid 3 - 1 Liverpool
Kakar 2014/2015
Champions League ranar Talata 4 ga watan Nuwamba 2014
- Real Madrid 1 - 0 Liverpool
Champions League ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2014
- Liverpool 0 - 3 Real Madrid
Kakar 2008/2009
Champions League ranar Talata 10 ga watan Maris 2009
- Liverpool 4 - 0 Real Madrid
Champions League ranar Laraba 25 ga watan Fabrairu 2009
- Real Madrid 0 - 1 Liverpool
Kakar 1980/1981
European Cup ranar Laraba 27 ga watan Mayun 1981
- Liverpool 1 - 0 Real Madrid