'Iyayen yaran da suka bata a Najeriya na cikin mawuyacin hali'

Wata mata

Asalin hoton, getty image

Lokacin karatu: Minti 2

Iyayen yaran da suka bata a Najeriya na cikin mawuyacin hali saboda batan 'ya'yansu da kawo yanzu wasu ma ba a san inda suke ba.

Shugaban iyayen yaran da suka bata wadanda ake zargi an sace su a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, kwamared Ismail Ibrahim Muhd , ya shaida wa BBC irin halin da iyayen yaran ke ciki.

Ya ce, a yanzu haka iyayen yaran wasu sun kamu da hawan jinni, wasu kuma sun kamu da ciwon zuciya kai wasu da yawa ma a cikinsu sun mutu saboda bacin ran rashin ganin 'ya'yansu.

Kwamared Isma'il Ibrahim Muhamed, ya ce," Akwai wasu iyayen yaran da suka bata da suka sayar da gidajensu ko filayensu sun kai wa malamai domin ayi musu addu'a, amma kuma har yanzu ba labari."

Ya ce," Iyayen yaran nan suna bukatar gwamnati ta tallafa musu saboda duk yawancin wadanda aka sacewa yaran nan ba su da karfi talakawa ne,akwai wasunsu ma da sun gamu da tabin hankali saboda batan yaransu, a don haka yana da kyau gwamnati ta nemi iyayen yaran nan a taimaka musu, sannan kuma gwamnatin ta mayar da hankali wajen neman yaran nan."

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa ICRC ta ce kusan mutum dubu 24 ne suka bata a Najeriya.

Ofishin kungiyar da ke kula da kididdigar batan mutane ya ce kusan kashi 59 na mutanen da suka bata yara ne kanana da kuma matasa.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ICRC ta ce iyalai sama da dubu 13 har yanzu na neman yan' uwansu dubu 23,659 da suka bata a sassan Najeriya.

ICRC ta ce ta yi imanin adadin ya fi haka, kuma jihar Borno ce ta fi yawan wadanda suka bata da take da kashi 67 cikin 100 daga yawan wadanda suka bata a Najeriya

kungiyar ta ce yawan wadanda suka bata a duniya an kiyasta sun kai mutum 284,400

Kuma a 2024 kadai, mutum dubu 94 aka bayar da rahoton sun bata a duniya.

Kungiyar ICRC ta ce batan mutane baya ga tashin hankali da ya jefa iyalai ya kuma kara jefa su cikin wahalhalun tattalin arziki.

ICRC ta ce kusan kashi 80 cikin 100 na mutanen da suka bata suna da alaka kai tsaye da rikici na makami akwai kuma wadanda ake sacewa ana fataucinsu.

A Najeriya dai kusan yankunan kasar na fama da kalubalen tsaro na 'yanbindiga masu satar mutane domin kudin fansa da kuma wadanda ke fataucin yara domin biyan wata bukata, wani abin da ke kara haifar da girman matsalar.