'Akwai buƙatar kafa doka a kan batun mutanen da suka ɓata a Najeriya'
Ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce akwai buƙatar kafa dokokin da za su taimaka wajen rage ƙunci da mawuyacin halin da dangi da iyalan mutanen da suka ɓata tsawon lokaci ke samun kansu a Najeriya.
Red Cross International ta na wannan kira ne, albarkacin Ranar Tunawa da Mutanen da suka Ɓata ta Duniya, wadda ake yi duk rana irin ta yau, 30 ga watan Agusta.
Ta ce ɓatan ɗan'uwa ko 'yar'uwa, lamari ne da kan jefa rayuwar mutumin da kuma dangi ko iyali ko iyayensa cikin wahala da fargaba da rashin tabbas, kuma Najeriya ba ta da dokokin da za su tallafa wa mutanen da 'yan'uwansu suka ɓata don rage musu tsanani da ƙuncin rayuwa.
'Yan Najeriya sama da 25,000 ne, Red Cross ta ce ta yi wa rijista a matsayin mutanen da suka ɓata a tsawon kimanin shekara 10, a cewar Aliyu Dawoɓe, mai magana da yawun ƙungiyar ba da agajin ta duniya
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tilasta ɓacewar mutane sau da yawa, ana amfani da shi a matsayin wata hanya da baza tsoro a zukatan al'umma.
Tilasta ɓatan mutane, wata matsala ce ta duniya, wadda a baya ake alaƙantawa da sojojin 'yan mulkin kama-karya amma a yanzu ana samun wannan al'amari a wuraren da ke fama da rikice-rikicen cikin gida, musamman don murƙushe abokan adawa.
Ɗaruruwan dubban mutane ne suka ɓata a lokacin rikice-rikice ko kuma lokacin gwamnatocin zalunci aƙalla a cikin ƙasashe guda 85 na duniya.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce jazaman ne a bai wa rukunin wasu mutane mafi rauni a cikin al'umma, kula ta musamman cikinsu har da nakasassu da ƙananan yara.
Ƙungiyar Red Cross ta ce ta sake haɗa mutane masu yawa da suka ɓata da dangi ko iyaye ko iyalansu, ciki har da ƙananan yara.
Kalli wannan bidiyo na sama don ganin tattaunawar Aliyu Dawoɓe.

Asalin hoton, ICRC



