Amnesty International ta zargi hukumomin Najeriya da cin zarafin yara

Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'Adama ta Amnesty International, ta bukaci shugaban Najeiriya Bola Ahmed Tinubu da ya hanzarta bayar da umarnin sakin yaran nan da aka gurfanar gaban kotu, saboda zargin shiga zanga zangar tsadar rayuwa.
Malam Isa Sanusi, daraktan kungiyar a Najeriya, ya bayyana wa BBC cewar sun kuma nemi a biya diyya, saboda irin gallazawa da galabaitarwa dayaran suka fuskanta tsawon lokacin da ake tsare da su tun a cikin watan Agustan shekarar nan ta 2024.
Ya ce ''Abun takaici ne abun da muka ga an yi wa yaran nan Ranar Juma'a a Abuja, cin zarafi yara ƙanana ne, abun kunya ne kuma muna Allah wadai da cin mutuncin yara ƙanana da ita kanta doka muna ganin an yi musu haka ne don galatsi da nuna musu cewar ba su da wani gata, iyayensu masu karamin karfi ne shi yasa aka yi musu haka” in ji shi.
Haka kuma ya ce an kai su kotu ne don a tauna aya, tsakuwa ta ji tsoro amma “kai su kotu da aka ai ba yi si ka doka ba, kuma an yi ne don kar mutane su futo su nemi yancinsu idan gwamanti ta yi ba daidai, an yi ne don kawai a nuna an yi amfani da ƙarfin doka a wulakanta mai karamin ƙarfi, sannan a ci mutuncin wadannan yara a cewar Malam Isa Sanusi.
Har ila yau Malam Isa Sanusi ya ce shi kansa zargin da ake musu na taddanaci, ba a sami yaran da ko reza ba, sannan su kansu wadan a ke zargin da yunkurin kifar da gwamanti, cikin su har da wani yaro da mahaifiyarsa ta aike shi ya siyo wa ƙanwarsa da bata da lafiya magani.
“Masu ƙokarin kifar da gwamanti na can a Zamafara, da Katsina, da Sokoto, da Kaduna, waɗanda ke can suna kashe mutane, da garkuwa da mutane, suna yi wa ƴa ƴa, da matan mutane fyade, wanda su ya kamata a ce gwamanti ta mayar da hankali wajen kamawa, amma ta ɓige da kama ƙanan yaran don kawai an ga suna da rauni” in ji Daraktan ƙungiyar ta Amnesty.
Yayi kira ga gwamanti da ta yi bincike sa tabbatar da an biyasu diyyar ɓata musu suna da aka yi, sannan duk wanda ke da hannu tunda daga sanada aka kama su, har zuwa tsawon lokacin da aka kamasu, a hukunta shi.
Abinda mahukunta ke cewa:

Asalin hoton, BarauJibrin@Facebook
Yayin da shugabanin da kungiyoyin kare hakkin bil'Adama na ci gaba da yi Allah wadai da kama yaran nan ashirin da bakwai, kan zanga-zangar matsin rayuwa, mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Barau Jibrin ya ce sun fara ɗaukar matakai tare da ofishin ministan Shari’ar ƙasar wajen ganin an saki ƙanan yaran da ake tsare da su.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Barau Jibrin ɗin dai ya tabbatar da cewar rundunar yansandan Najeirya sun tura takardun tuhumar ƙananan yaran nan 27 da aka gurfanar gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a rana Juma'ar da ta gabata, daga hannun 'yan sanda zuwa ofishin ministan shari'a na kasar.
Sai dai ya ce tuni suka yi magana da ministan shari’a da Darktan gabatar da kara na ma’aikatar shari’a wanda tuni ya karɓi kundin shari’ar daga ɓangaren ƴan sandan don ganin an ɗauki matakan da suka kamata.
“Na yi magana da ministan shari’a na Najeirya kan wannan batu, wanda saboda mahimmancin maganar ya shiga aiki a ranar asabar din nan, kuma ya karbi kundin shar’ar daga hannun yan sanda, inda zai tattauna da bangaren kotun wajen ganin an saki yaran nan” in ji Barau Jibrin.
Sanata Barau jibrin din ya ce “ magana ce wadda ta ke gaban kotu dole sai an kula da doka wajen dauar mataki kan wannan batu, shi yasa ma aka sami jinkirin saka bakinmu cikin harkar shari’ar, don kauce yi wa kotu katsaladan a aikin ta” in ji shi.
Haka kuma ya ce a makon da zaa shiga suna sa rana alkalin zai sake zama don bayar da hukunci, idan suke da tabbacin cewar zaa sauƙaƙa sharudan belin da zaa bayar da yaran, wanda su ne suka fi shiga mawuyacin hali.
a jiya Juma'a ne dai ministan Shari’a na Najeriya Prince Lateef Fagbemi (SAN) a wata sanarwa da ya fitar a cikin daren ranar, ya buƙaci rundunar ƴan sandan Najeriya da ta gabatar masa da kundin shari’ar mutanen a yau Asabar 2 ga watan Nuwambar, 2024. Sannan ta mika kwafin kundin ga daraktan gabatar da ƙara na ma'aikatar shari'ar shi ma a goben.














