Kotu ta ba da belin yaran da gwamnatin Najeriya ta gurfanar kan zanga-zanga

Babbar kotun tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta bayar da belin mutum 67 cikin 76 da gwamnatin ƙasar ta zarga da cin amanar ƙasa sakamakon zanga-zangar da suka gudanar a watan Agusta.
Kotun ƙarƙashin Mai Shari'a Obiora Egwuatu ta saka wa kowannensu sharaɗin naira miliyan 10, da kuma gabatar da mutumin da zai tsaya wa kowa, wanda ta ce dole ne ya kasance ma'aikacin gwamnati mai matakin albashi na 15.
Sai dai mutum 27 cikin waɗanda aka gurfanar a kotun ƙananan yara ne da shekarunsu ba su kai 18 ba, har da ma mai shekara 14, kamar yadda BBC ta gani a takardun kotun.
An tura manyan cikinsu zuwa gidan yari, an kuma aika da yaran wani gidan kula da kangararrun yara har zuwa ranar 25 ga watan Janairu, inda za a ci gaba da shari'ar.
An kama waɗanda ake zargin ne a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a faɗin Najeriya tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.
An kama su ne a garuruwan Kano, da Katsina, da Gombe, da Abuja, da Jos, da Kaduna.
Ana tsaka da sauraron ƙarar ne kuma yara huɗu daga cikin waɗanda ake zargin suka yanke jiki suka faɗi, abin da ya sa dole alƙalin ta dakata domin a duba su.
Daga nan sai aka fara kiran su ɗaya bayan ɗaya ana karanta musu laifukan da ake zargin su da aikatawa cikin harshen Ingilishi, inda tafinta ke fassara musu da Hausa.
Sai dai sun musanta aikata laifukan.
Wasu masu fafutika da suka zanta da BBC a harabar kotun sun ce an tsare wasu daga cikin yaran tun daga watan Agusta - kwana 80 kenan.
Daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi musu akwai cewa "sanyawa tare da ɗaga tutar Rasha, suna rera waƙoƙin juyin juya-hali tare da kira ga Rasha ta kawo ɗauki a Najeriya".
A farkon watan nan ne gwamnatin ta gurfanar da mutum 10 a gaban kotu, waɗanda ta zarga da jagorantar zanga-zangar. Daga baya kotun ta ba da belinsu kan naira miliyan 10 kowannensu, yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar tasu.
'Tauye haƙƙin 'yanƙasa'
Da take mayar da martani game da kamen masu zanga-zangar, ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty a Najeriya ta yi tir da kama mutanen, tana mai cewa kama su ya saɓa wa dokokin kare haƙƙi na ƙasa da ƙasa.
"Yunƙurin gwamnatin Bola Tinubu na gurfanar da ƙananan yara kan zargin cin amanar ƙasa na nuna halin yin watsi da tanadin doka," in ji Amnesty cikin wata sanarwa a shafukan sada zumunta.
"Jefa ƙananan yaran cikin mawuyacin hali kawai saboda sun shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa ɗaya ne daga cikin yunƙurin tauye 'yancin yin taro.
"Wajibi ne Bola Tinubu ya sake su nan take kuma ba tare da wani sharaɗi ba."
Ƙungiyar ta ƙara da cewa jami'an tsaro sun kama 12 'yan ƙasa da shekara 16 a jihar Katsina "kawai don sun fito titi a ranar zanga-zangar".











