Gobarar Singa: 'Ni da ƴan'uwana ba mu cire ko tsinke ba'

Lokacin karatu: Minti 4

Tsaye a kusa da ƙonannun kantuna, yayin da hayaƙi ke tashi a bayan shi, Shafi'u Adam ya shaida wa BBC cewa shi da ƴan'uwansa sun rasa dukkanin abin da suke da shi a gobarar kasuwar Singa.

"Tun daga kan tantunana har kan rumfunan da nake da su, ni da ƙannaina, babu abin da muka fitar a cikinsu."

Shafi'u na cikin ƴan kasuwa sama da 1,000 waɗanda ke cikin jimamim ɓarnar da gobara ta yi musu a kasuwar Singa da ke tsakiyar birnin Kano.

Kano ita ce jihar da ta fi yawan al'umma a arewacin Najeriya kuma jiha mai daɗaɗɗen tarihin hada-hadar kasuwanci a yammacin Afirka.

Ƴan kasuwa daga sassa da dama na Najeriya da ƙasashe masu maƙwaftaka ke saye da sayarwa a kasuwannin birnin a kowace rana, kuma Singa na daga cikin kasuwannin da suka fi shahara.

Duk da cewa har yanzu ba a ƙididdige ba, amma ana da yaƙinin cewa an tafka gagarumar hasara a gobarar, wadda ta fara ci daga ranar Asabar har zuwa Litinin.

Ko a ranar Litinin, lokacin da wakilin BBC ya ziyarci kasuwar, hayaƙi na tashi a wasu sassan kasuwar, inda wutar ba ta gama mutuwa ba.

Za ka iya ganin kayan da suka ƙone sun yi baƙi ƙirin, baya ga haka nan kuma akwai ababen hawa kamar babura da kekunan hawa waɗanda su ma wutar ta ƙone ƙurmus.

Ɓangaren da gobarar ta ƙone da ake yi wa laƙabi da Gidan Gilas, shi ne wurin da ake sayar da kayan abinci da sauran kayan masarufi.

'Ba mu san iyakar asarar da aka tafka ba'

Shafi'u ya shaida wa BBC cewa a yanzu sai dai a yi ƙiyasi, amma babu wanda ya san iyakar asarar da aka tafka.

"Duk mutumin da zai ce maka ga iyakar ƙimar dukiyar da aka rasa, sai dai kawai shaci-faɗi, babbu wanda zai iya tantance iyakar miliyoyi ko biloliyoyin da wannan wuta ta halaka," in ji shi.

Shugaban kasuwar, Junaidu Zakari ya shaida wa BBC cewa gabarar ta shafi ƴan kasuwa sama da 1,000 da ke hada-hada a kasuwar.

"Akwai dukiya mai ɗimbin yawa a kasuwar nan, aƙalla sama da shago dubu sun taɓu a cikin wannan kasuwa."

Jami'in yaɗa labaran kasuwar ya ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe hudu na ranar Asabar.

'Mun zata za mu iya kashe wutar'

Jamilu Abdullahi, wanda shi ne shugaban ɓangaren ƴan taliya na kasuwar ya shaida wa BBC cewa sun yi yunƙurin kashe gobarar a lokacin da ta fara, sai dai abin ya fi ƙarfinsu.

"Wutar ta tashi ne daga waje ɗan ƙalilan, muna ganin za mu iya kashe ta da hannu, amma a ƙarshe sai muka ga ta tashi sosai, ta wuce misaltuwa."

"Wutar nan ta fara ci ne daga sama, kuma ana zargin fanel na sola (farantin tatsar hasken rana) ne ya tayar da wannan wuta, kuma aƙalla yau kusan kwana hudu ke nan wutar tana ci.

Har yanzu dai hukumomi ba su sanar da abin da ya yi sanadiyyar tashin gobarar ba. Amma gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf wanda ya kai ziyara a kasuwar ranar Lahadi ya bayyana cewa za a gudanar da bincike.

Ya buƙaci gwamnatin tarayya ta kai ɗauki ta hanyar amfani da ƴan kwana-kwana, ta sama da ta ƙasa.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura mataimakinsa Kashim Shettima domin zuwa Kano ya yi wa ƴan kasuwar jaje.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa Shettima ya gana da ƴan kasuwa a lokacin ziyarar tasa da ya kai a Kano ranar Litinin.

A lokutan hunturu, wanda ke farawa daga ƙarshen shekara zuwa farkon sabuwar shekara ana yawan samun faruwar gobara a arewacin Najeriya sanadiyyar kaɗawar iska.