Yadda za ka shirya wa tsufa tun daga shekaru 30

Hoton wasu tsofaffi biyu

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, ديفيد كوكس
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wasu ɗabi'u ko abubuwa masu sauƙi da za ka yi a lokacin da kake shekara talatin za su iya yin tasirin gaske a yanayin lafiyarka lokacin da ka kai shekara saba'in, kama daga tafiya ta minti 15 a ƙasa zuwa samun wadataccen bacci akai-akai.

Zuwa lokacin da ka kai shekara 80, ƙila za ka iya fara jin jikinka ya yi rauni, ka fara manta wasu abubuwa idan aka kwatanta da yadda kake a lokacin kana matashi.

Yanayin baccinka zai iya sauyawa ta yadda za ka fara jin bacci da wuri da yamma, sannan kuma ka tashi daga baccin da wuri, ba kamar yadda ka saba ba, sannan kuma kila ka riƙa fama da aƙalla wata cuta mai tsanani ɗaya.

Masu bincike a yau sun yi amanna fiye da a kodayaushe a baya cewa wannan hali da mutum zai shiga idan ya kai shekara tamanin abu ne da ba ta yadda zai iya kauce masa.

Shugaban cibiyar nazarin tsufa a California, (Buck Institute for Aging Research in California) Eric Verdan, ya ce: "Daga abin da muka sani yanzu mutane da dama na iya sa ran su kai shekara 90 zuwa 95 cikin ƙoshin lafiya idan sun inganta yanayin rayuwarsu

Verdan ya nuna cewa: ''Wannan ya saɓa da abin da muke gani a yau inda yawancin mutane suke rayuwa cikin ƙoshin lafiya har zuwa shekara 65 ko 70, daga na kuma sai su fara rashin lafiya mai nasaba da tsufa."

Verdan ya ƙara da cewa babu wani mataki na shekaru da za a ce ka makara don fara inganta yanayin lafiyarka ta hanyar yin sauye-sauye, walau motsa jiki ne , ko inganta abincinka ne ko rage yawan shan barasa, to amma dai sakamakon zai fi kyau idan ka fara da wuri.

Masana kimiyya sun nuna cewa shekara talatin lokaci ne da sassa daban-daban na jiki, kamar su ƙashi da tsoka, da aikin jikin za su fara nuna alamu na sauyin da ya danganci tsufa.

Hoton wani mutum na motsa jiki na gudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararru sun ce ya kamata mu yi ƙoƙarin cimma ƙololuwar lafiyar jikinmu a lokacin da muke shekaru 30 domin cin moriyar lafiyarmu idan shekarunmu sun ja
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babban malami a kan abinci da aikin jiki a Jami'ar Manchester Metropolitan, Paul Morgan, ya nuna cewa galibin 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle da sauran wasanni yanayin tsufansu yana bambanta da na yawancinmu.

Su suna da lafiyar zuciya fiye da mu da ƙarfin tsoka ko jijiyoyi da aikinsu, inda sai daga baya tsufansu ke sako kai hakan ya fara raguwa.

Ya ce a dalilin haka yawancinsu ba sa gamuwa da matsalar kasa tafiya da dogaro da kai, tsawon lokaci ko bayan sun tsufa.

Masanin ya ce kowa zai iya koyon darasi daga wannan. Ya ce domin samun damar cin moriyar tsufa cikin lafiya, ya kamata mu dage mu kai ƙololuwar da ya kamata mu kai wajen motsa jiki da rayuwa mai kyau, a lokacin da muke shekaru talatin.

Faɗuwa na ɗaya daga cikin manyan matsaloli masu haɗari ga duk mutumin da ya kai shekara 70, kuma hakan na da nasaba da kasa tafiya da raguwar motsin gaɓoɓi.

Saboda haka masanin yake ganin abu ne da ya ke da kyau mutum ya mayar da hankali wajen motsa jikin da zai inganta motsin sassan jikinsa na ƙasa ( ƙafa).

Gudu na tsawon minti 75 a mako ɗaya ko tafiya ta sassarfa ta minti 15 bayan ka ci abinci za su haifar da sakamako mai kyau da za ka fara gani da j a jikinka.

Gina ƙwaƙwalwarka

Kamar dai yadda za mu iya inganta lafiyar jikinmu - tsoka da jijiyoyi da zuciya a lokacin da m,uke shekaru 30, za mu iya yin haka ga ƙwaƙwalwarmu ma.

Kula da lafiyar baki ta hanyar zuwa asibiti ana duba bakinka akai-akai, da goge haƙoranka yanda ya dace da kauce wa shan taba da rage shan abubuwa masu zaƙi ka iya yin tasiri sosai - wajen inganta aikin ƙwaƙwalwarka.

'Ya'yan itace

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawanci an yi amanna cewa cin 'ya'yan itace ko abincin da ba shi da kayan zaki sosai jigo ne wajen rayuwa cikin ƙoshin lafiya

A lokacin da ka kai shekaru talatin zuwa sama daga na ya kamata ka fara rage yawan barasar da kake sha, idan kana ta'ammali da ita, kasancewar shan giya na iya haifar da sauyi a aikin da ya shafi ƙwayoyin halitta na gado, wanda hakan ke sa tsufa da wuri.

Barasa na daga cikin manyan abubuwan da ke hana mutum bacci, kuma Verdan ya ce tsayar da wani lokaci ɗaya na bacci na da muhimmanci wajen motsewar ƙwaƙwalwa da ke da nasaba da tsufa, kuma hakan na rage haɗarin kaumuwa da cutar mantuwa, idan mutum ya tsufa.

Hakan na buƙatar ka tabbatar ka tsayar da wani lokaci ɗaya na kwanciya da kuma tashi daga bacci a kullum, domin a lokacin bacci na gyara ƙwayoyin halitta na jiki.

To amma kuma samun bacci wadatacce da daddare ba lalle ba ne musamman ga waɗanda suke da ƙananan yara a shekara talati.

Saboda haka yana da kyau tun kana shekaru talatin ka bayar da muhimmanci kan cin abincin da ya dace.

Verdan ya ce abu mafi kyau da ya dace mu yi kuma da rana, domin amfanin jikinmu shi ne ma ba i wa jikinmu damar hutu - a lokacin da ba ma cin abinci - misali ta hanyar azumi lokaci zuwa lokaci.

Masanin ya ce: ''A lokacin da kake azumi, hakan na sa jikinka ya kawar da kai daga narkar da abinci, ya koma gyara, shi ya sa nake gaya wa mutane lokacin da kake cin abinci gini kake, idan kana azumi kuma kana gyara jikin.''

Cin 'ya'yan itace da ganyayyaki maimakon abincin gwamngwani zai sa ka ga bambanci sosai.

Hoton wani mutuun na motsa jiki da tattabaru

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararru sun ce bin hanyoyi na inganta lafiya a lokacin da kake shekaru 30, hakan zai iya rage sauye-sauyen da jikinka zai yi da ka iya haifar maka da rashin lafiya gaba a rayuwa

Masana na gani zaɓin irin rayuwar da muka yi a lokacin da muka kama hanyar zama manya - wato shekara talatin hakan na iya yin tasiri sosai a kan yadda tsufanmu zai kasance.

Bin tsarin rayuwa mai kyau a lokacin da mutum yake shekaru talatin, yana rage masa haɗarin kamuwa da cutukan zuciya, da dakushewar ƙwaƙwalwa da raunin jiki- har ya kai wasu shekaru masu yawa.