Ya kamata Sule Lamido ya zubar da makamansa — PDP

Lokacin karatu: Minti 3

Sabon shugabancin babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ya yi watsi da wa'adin kwanaki goma da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, ya bayar na a rushe shugabancin jam'iyyar.

Tsohon gwamnan dai ya buƙaci jam'iyyar PDP ta warware rikicin cikin gida da ya yi mata katutu wanda ya haɗa da rushe babban taronta da ta gudanar a birnin Ibadan, da kuma abin da aka cimma.

A cewar shugabancin jam'iyyar ta PDP, bai kamata a ce tsohon gwamnan na Jigawa, da ake yi wa kallon dattijo a jam'iyyar da ya ba da gudummawa wajen ci gabanta, ya dawo yana neman cindunduniyarta ba, don haka akwai bukatar ya mayar da wukarsa cikin kube, ya zo a sasanta.

Alhaji Umar Sani, jigo ne a jam'iyyar ta PDP, kuma mai taimakawa shugaban jama'iyyar na kasa Tanimu Turaki, ya shaida wa BBC cewa, a matsayinsa na babba kuma wanda ya san siyasa kana ya san yadda ake tafiyar da jam'iyya, to ya ajiye komai ya dawo ayi tafiya tare.

Ya ce," A yanzu jam'iyyarmu ta PDP, bata bukatar komai sai hadin kai duk wasu rigingimu ya kamata a jinginesu don a samu aka kai ga gaci."

"Abin da Sule Lamido da wasu ke so jam'iyya ta yi ba zai yiwu ba domin duk abin da ya kamata ayi an yi don haka babu mayar da hannun agogo baya."In ji shi.

Alhaji Umar Sani,ya ce," Duk abin da ya kamata mu yi kai hatta shi shugaban jam'iyya sai da ya nemi su gana da Sule Lamido don a fahimci juna amma hakan bai yiwu ba, don haka babu wani da za ayi kuma."

To sai dai duk da wannan kira da jagororin jam'iyyar ta PDP ke yi, wasu makusantan tsohon gwamnan na Jigawa Sule Lamido, sun ce ko a jikinsu, domin tun farko, rashin bin ka'ida ne ya sa suka ja daga.

Babandi Ibrahim Gumel, shi ne shugaban jam'iyyar PDP na Jihar Jigawa, kuma na hannun daman Sule Lamiɗo, ya shaida wa BBC cewa,akwai karya doka akan shugabanci domin haka kawai sai wani ya zo ya ce shi ne shugaba.

Ya ce," A yanzu fa wa'adin shugabannin jam'iyyar ta PDP su Damagum bai kare ba, kuma basu rubuta cewa sun ajiye mukamansu ba, to amma wasu sun je suna cewa su ne shugabanni a ina aka taba yin haka? a ka'ida sai ranar 8 ga watan Disambar 2025, wa'adin su Damagum zai kare, kuma idan wa'adin ya cika, to a ka'ida jam'iyyar PDP bata da shugabanci."

Makusancin Sule Lamido, y ace," Mu ba mu da wata manufa, kawai dai a rinka bin tsari da abin da doka kuma ta ce."

Wannan dai ba shi ne iya rikicin cikin gidan da jam'iyyar ta PDP ke fama da shi ba, akwai kuma na bangaren Wike, inda har ta kai ga wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar suka kafa na su shugabancin, suna ja da na Tanimu Turaki da aka zaba a baya bayan nan, ko da yake duk da irin wannan rikitata-rikita, wasu 'ya'yan jam'iyyar na nanata cewa PDP na da hanyoyin gyara al'amiuranta.

Kodayake masana na hasashen cewa idan jam'iyyar ba ta magance matsalolinta ba, akwai yiwuwar ta fuskanci ƙalubale a zaɓukan shekarar 2027 da ke tafe.