Yadda aka kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a tekun maliya

- Marubuci, Thomas Mackintosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Rundunar sojin Amurka ta ce an harbo wani jirgin yaƙin ƙasar a kan tekun maliya a wani abu da ake gani harin kuskure ne.
A cewar shalkwatar tsaron ƙasar, ma'aikatan jirgin yaƙin sun fice daga cikin jirgin samfurin F/A 18 Hornet lafiya, sai dai ɗaya daga cikinsu ya samu raunuka.
Lamarin ya faru ne bayan Amurka ta ƙaddamar da wasu hare-hare ta sama kan wani wurin ajiyar makamai masu linzami da kuma kadarorin rundunar tsaro a Sanaa, babban birnin Yemen, waɗanda ƴan bindigan Houthi da ke da goyon bayan Iran ke aiki da su.
Shalkwatar tsaron Amurka ta ƙara da cewa ta kuma kai hari kan jirage maras matuƙa da dama na ƴan Houthi da kuma makami masu linzami da ke kai hari kan jiragen ruwa da ke kan tekun maliya.
A cikin wata sanarwa, shalkwatar tsaron Amurka ta tabbatar da 'harin kuskuren' a kan tekun maliya.
''Jirgin ruwan yaƙin Amurka samfurin USS Gettysburg, wanda ke cikin jiragen ruwan da ke dakon jiragen sama mai suna USS Harry S Truman, ya harbi jirgin saman yaƙin samfurin F/A 18 da ke kokarin tashi daga kan jirgin ruwan da ya yi dakon su.
Ba a tabbatar ko jirgin saman da aka harbo na cikin waɗanda ake amfani da su a Yemen ba.
Tun da farko, shalkwatar tsaron ta ce harin da aka kai a Sanaa, an yi su ne domin daƙilewa da kuma ƙasƙantar da ayyukan ƴan bindigan Houthi, kamar harin da suke kai wa kan jiragen yaƙin rundunar sojin ruwan Amurka da kuma manyan jiragen ruwan dakon kaya a kudanci tekun maliya da Bab al Mandeb da kuma tekun gulf na Aden.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rundunar sojin Amurka ta kuma ce ta kai hari kan jirage marasa matuƙa na Houthi, da kuma makami mai linzami da ke hari kan jiragen ruwa a kan tekun maliya ta hanyar amfani da kayan yaƙin sojojinta na sama da na ruwa, ciki har da jirage ƙirar F/A 18.
Ƴan bindigar Houthi, wata ƙungiyar ƴantawayen da ke da goyon bayan Iran da ke da iko da arewa maso yammacin Yemen, sun fara kai hari kan Isra'ila da kuma jiragen ƙasashen waje jim kaɗan bayan fara yaƙin Gaza a watan Oktoban 2023, a cewarsu suna hakan ne domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.
Tun watan Nuwamban 2023, harin makami mai linzami na ƴan Houthi ya nutsar da manyan jiragen ruwa biyu a tekun maliya tare da lalata wasu. Suna ikirarin cewa suna kai hari ne kawai kan jiragen da ke da alaƙa da Israila, da Amurka ko kuma Birtaniya, a lokuta da dama kuma hakan ba gaskiya ba ne.
A watan Disamban bara, Birtaniya da Amurka da wasu ƙasashe 12 sun ƙaddamar da wani shiri domin kare jiragen da ke bi ta tekun maliya daga hare haren.

Asalin hoton, Reuters
A ranar asabar, sojijin Isra'ila sun ce sun yi rashin nasara a ƙoƙarin su na kakkaɓo wani makami mai linzami da Yemen ta harbo inda makamin ya faɗa wani wurin shaƙatawa a birnin Tel Aviv.
Asibitin tafi-da-gidanka na Israila mai suna Magen David Adom ya ce ya yi wa mutane 16 magani wanɗanda suka samu raunuka daga ɓaraguzan gilashi daga tagogin da suka fashe a gine-ginen da ke kusa.
Ma'aikatan asibitin sun kuma ce sun bai wa ƙarin mutane 14 magani waɗanda suka samu raunuka a hanyarsu ta zuwa yankunan da ke da kariya.
Wani mai magana da yawun Houthi ya ce ƙungiyarsu ta kai hari kan wani wurin sojoji ta hanyar amfani da makami mai linzami mai gudun gaske.
A farkon makon nan, Israila ta ƙaddamar da hare hare da dama kan abin da ta ce sansanin dakarun Houthi ne, inda ta harbo tashoshin ruwa da kuma kayan samar da makamashi a Sanaa, babban birnin Yemen.
Kafar talibijin ta ƴan Houthi mai suna Al-Masirah ta ruwaito cewa mutane tara sun mutu a tashar jirgin ruwa na Salif da kuma tashar Ras Issa.
Ƴan bindigan Houthi sun sha alwashin ci gaba da kai hare harensu har sai yaƙin da akeyi a Gaza ya zo ƙarshe. Amurka ta ce harinta na baya bayanan yana daga cikin ƙudurinta na kare kanta da kuma ƙawayenta.











