Ko ya halatta Trump ya karɓi kyautar jirgin alfarma daga Qatar?

    • Marubuci, Jake Horton, Tom Edgington and Joshua Cheetham
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai zama tamkar "sakarai" idan ya mayar da hannun kyauta baya dangane da kyautar jirgin da ƙasar Qatar ta ba shi mai ƙimar dala miliyan 400.

To sai dai ƴan jam'iyyar hamayya sun bayyana karɓar kyautar da "abin da ya saɓa doka", wani abu da fadar White House ta musanta - kuma hakan ya janyo suka daga magoya bayan Donald Trump.

Sashen BBC Verify mai bincike ya yi nazari kan abin da doka ta ce ga shugabanni su karɓi kyautuka.

Bayani kan jirgin

A ranar Lahadi ne kafafen watsa labaran Amurka suka rawaito cewa gwamnatin Amurka na shirin karɓar babban jirgi sama ƙirar Boeing daga gidan sarautar Qatar - inda suke cewa za a sake ƙawata jirgin domin kasancewa jirgin shugaban ƙasar na Amurka.

Daga baya kuma sai Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa "Ma'aikatar tsaron Amurka ta samu kyautar jirgi ƙirar 747 domin maye gurbin jirgin shugaban ƙasa wanda ya kwashe shekaru 40..."

Jirgin wanda aka ɗauki hotonsa a wurin shaƙatawa na Palm Beach a Florida a watan Fabrairu inda Trump ya je duba shi.

Yanzu haka jirgin na da ɗaki guda uku da wurin shaƙatawa da ofis, kamar yadda takardun jirgin na 2015 suka nuna.

Wani jami'i daga Qatar ya shaida wa CNN cewa ma'aikatar tsaron Qatar ce ta bai wa ma'aikatar tsaron Amurka jirgin domin sake masa fasali ya dace da jirgin shugaban ƙasar Amurka.

Sai dai kuma masana na cewa sake wa jirgin fasali domin dacewa da shugabannin Amurka ka iya ɗaukar shekaru kuma abin da hakan ke nufi shi ne sai bayan zangon mulkin Trump ne jirgin za a kammala sake wa jirgin fasali.

Trump ya ce jirgin zai shiga jerin ɗakinsa na kayan shugaban ƙasa bayan ya bar ofis inda ya ce ba zai ci gaba da amfani da jirgin ba bayan kammala wa'adin mulkin nasa.

Shin ko kyautar ta halatta a dokance?

Manyan ƴan jam'iyyar Democrat sun yi iƙrarin cewa karɓar kyautar bai halatta ba a dokance.

Ɗan majalisar dattawa Adam Schiff ya karanto wani tsagi na kundin tsarin mulkin Amurka da ya ce bai dace mutumin da ya kasance zaɓaɓɓe ba ya karɓi "kowace irin kyauta..." daga wani shugaba na wata ƙasar waje ba tare da amincewar ƴan majalisa ba.

Frank Cogliano, farfesa a sashen nazarin tarihin Amurka a jami'ar Edinburgh, ya ce wannan saɗarar "an yi ta ne domin daƙile amfani da rashawa da cin hanci da manufar juya akalar gwamnati."

"Zancen gaskiya wannan tamkar ƙure ƙarfin kundin tsarin mulki ne saboda ba mu taɓa ganin kyauta mai girman wannan ba, ko mai kama da wannan", in ji Farfesa Andrew Moran, ƙwararre kan kundin tsarin mulki da shari'a a jami'ar London Metropolitan University.

A yanzu haka bisa doka, jami'an ƙasar Amurka na karɓar kyautar da ba ta gaza $480 ba.

Duk da cewa Donald Trump ya ce jirgin zai tafi "dakin" ajiyar kayansa, ƙwararru na cewa hakan na nufin zai ajiye jirgin a gidan tarihinsa ne idan ya kammala wa'adinsa.

Tsaffin shugabannin ƙasa na da ɗakin adana kaya da ke taskace takardu da kuma gidan tarihi da jama'a ke ɗaukar nauyi.

Ƙwararrun da Sashen BBC Verify ya yi magana da su, sun ce za a iya bai wa gwamnati jirgin ba shugaban ƙasar da ke kai ba - kafin daga bisani ya miƙa shi zuwa gidan adana tarihi, wanda hakan ba lallai ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulki ba.