Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Duk wanda ya zaɓi Tinubu tsakani da Allah ba ya da-na-sani'
Yayin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cika shekara biyu a kan mulkin Najeriya, wasu makusantan shugaban sun kafe a kan cewa lalle an samu cigaba duk da irin kukan da 'yan kasar ke yi na tsananin rayuwa.
Wani na hannun daman shugaban kuma jigo a jam'iyyar ta APC, Alhaji Ibrahim Masari, ya ce duk wanda ya zabi shugaban tsakaninsa da Allah ba ya da-na-sani.
A wata tattaunawa da BBC, Masari ya ce Shugaba Tinubu ya cimma nasarori da dama, kama daga kan tsaro da tattalin arziki.
Ya ce daya daga cikin nasarorin da shugaban ya samu ita ce cire tallafin man fetur, abin da wasu ke yi wa kallon koma-baya, sai dai a zahiri ya haifar da gagarumin cigaba ta hanyar samar da karin kudaden da matakan gwamnatocin kasar ke samu, wanda hakan ya taimaka wajen samar da ayyukan raya kasa ga jama'a da tafiyar da gwamnati.
''Cire tallafin mai da aka yi babu shakka abu ne maras dadi kuma hukunci ne wanda aka dauka mai nauyi wanda shugabannin kasa sun so su dauki wannan hukunci suka kasa yi sai shi ya yi saboda irin ta'adin da ake yi ta kudaden kasar da suke zurarewa ta wannan fanni na tallafin mai da ake bayarwa ta tallafin wutar lantarki.''
Masari ya kara bayani da cewa : ''Kuma na tabbatar da cewa inda za ka yi magana da gwamnoninmu na Najeriya, yanzu za su ce maka lalle tsakani ga Allah cire tallafin man, sai dai gwamnan da bai son ya yi aiki amma maganar kudade dai da suke samu daga gwamnatin tarayya ya ishe su su je su yi aiki a jihohinsu.''
Dangane da wahalhalun da ake cewa cire tallafin ya haifar a kasar sai ya ce :
Ba a taba yin gyara ba a sha wahala ba. Hukunci ne ba abu ba ne mai sauki amma dai na tabbatar maka cewa daga baya, ko yanzu ma ya fara biyowa baya.''
Ya ce : ''Yanayi ne talaka na Najeriya muna bada hakuri cewa in Allah ya yarda kamar yanda iyayenmu Hausawa ke cewa bayan wuya sai dadi da karfin ikon Allah, wannan dadin yana nan zuwa kuma a kusa yake ba wai da nisan nesa ba.''
Jigon ya kara da cewa : ''Ina ganin ko ba ka son mai girma shugaban kasar tarayyar Najeriya na yanzu, Bola Ahmed Tinubu, ya yi abubuwa masu tarin yawa kuma an samu cigaba iri-iri a kasar.''
Hadimin na Shugaba Tinubu ya ce aikin gwamnati aiki ne na dorawa, idan wannan gwamnati ta yi iya yinta wata ta gaba ta zo sai ta dora ta ci gaba daga inda ta baya ta tsaya.
''Idan ma Bola Ahmed Tinubu ya gama iya shekarun da zai yi mulki ba zai iya wadata najeriya da dukkan abin da suke so ba, amma in aka dora dan-ba din na tafiya ta gaskiya to ina tabbatar da cewa ko da wani ya zo ba zai iya kaucewa daga wannan tubali da harsashin da aka dora Najeriya a kanshi ba,'' in ji shi.
Dangane da alkawarin inganta harkar tsaro da gwamnatin ta yi wa al'ummar Najeriya kuwa inda a yanzu wasu ke ganin kusan gwamnatin ta kasa magance matsalar sai ma kusan karuwa take yi, hadimin na Tinubu ya ce, idan aka dubi yankin arewa masu yammacin kasar misali jihar Kaduna - yankin Birnin Gwari da kuma yankunan jihar Katsina, ''duk kiyayyarka da wannan gwamnati ba ta yadda za ka zo ka ce gara jiya da yau.'' Ya ce.
''Daga wannan kadan-kadan cigaban da ake samu wata rana in Allah Ya yarda za a ga karshen matsalar tsraon gaba daya,'' in ji shi.
Game da yadda wasu 'yan siyasa ke ta tururuwa suna komawa jam'iyyar APC mai mulki daga wasu jam'iyyu, Alhaji Masar, ya kawar da zargin barazana da wasu ke cewa ana yi wa 'yan siyasar ne suke sauya sheka.
Ya ce hakan na faruwa ne saboda cigaban da ya ce jam'iyyar APC a karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kawo.
Haka kuma Masari ya musanta zargin da wasu ke yi cewa Shugaba Tinubu na nuna bambanci - yana fifita 'yan kabilarsa ta Yarabawa wajen nada su manyan mukamai masu maiko fiye da sauran kabilun kasar musamman 'yan arewa da ake ganin sun ba shi kuri'u masu yawa a lokacin zabe.
Jigon na APC ya bayar da misalin wasu 'yan arewacin kasar da ke rike da mukamai manya kamar babban mai ba shugaban kasar shawara a kan harkar tsaro Mallam Nuhu Ribadu da ministocin tsaro -babba da karami da shugaban sojoji da ya ce duka 'yan arewa ne.
Bugu da kari ya kuma yi nuni da ma'aikatar gona da ya ce tana daga cikin wadanda aka fi ware wa kudi mai yawa domin bunkasa harkar samar da abinci -abin da ya ce wannan zai fi amfanar arewacin kasar ne.