Hare-haren Amurka sun kashe mutum 53 a Yemen - Houthi

Bayanan bidiyo, Yadda Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan Yemen
    • Marubuci, George Wright
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan tawayen Houthi na Yemen sun ce sabbin har-haren sama da Amurka ta ƙaddamar sun kashe mutum 53 ciki har da ƙananan yara biyar.

Ƙungiyar ƴan tawayen ta ce harin ya faɗa ne a yankin Al Jaouf da kuma Hudaydah da sanyin safiyar Litinin, kuma ma'akatar tsaron Amurka ta tabbatar da fara kai hare-haren.

A ranar Asabar Amurka ta ƙaddamar da harin da ta kira ''mai ƙarfin gaske'' a wani mataki na hana mayaƙan Houthi kai hari kan jiragen ruwa a tekun Maliya.

Washington ta ce an kashe jiga-jigai a ƙungiyar ta Houthi, amma har yanzu ƙungiyar ba ta tabbatar da hakan ba.

Jagoran Houthi, Abdul Malik al-Houthi ya ce mayaƙansa za su kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka a tekun Maliya idan har Amurkan ta ci gaba da kai wa Yemen hari.

A saƙon da ya wallafa a shafi X, kakakin ma'aikatar lafiyar Houthi, Anis al-Asbahi ya ce mutane 53 aka kashe a hare-haren kuma cikin su har da ƙananan yara biyar da mata biyu, sai kuma wasu mutum 98 suka raunata.

Wani mutum mai ƴaƴa biyu mai suna Ahmed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ''Ina zaune a Sanaa tsawon shekara 10, na saba da jin ƙarar bama-baman yaƙi. Amma tsakani da Allah ban taɓa tsintar kaina a cikin yanayi irin wannan ba.''

Mai bai wa Amurka shawara a kan tsaron ƙasa, Michael Waltz ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta ABC News cewa ''harin na ranar Asabar an kai shi ne kan jagororin Houthi da dama, kuma an kashe su.''

Ya kuma shaida wa Fox News cewa ''Mun kawar da su, kuma mun aike da saƙon gargaɗi ga Iran cewa an kai bango.''

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya sha alwashin ''ci gaba da kai harin makami mai linzami kan Houthi babu ƙaƙƙautawa.''

Su kuma mayaƙan Houthi sun ce za su cigaba da kai hari kan jiragen ruwa a tekun Maliya har sai Isra'ila ta janye takunkumin da ta sanya na hana shigar da kaya Gaza, tare da jaddada cewa mayaƙan za su mayar da martani kan harin.

Ƙungiyar ƴan tawayen mai samun goyon bayan Iran tana ganin Israila a matsayin abokiyar gabar ta, kuma ita ke da iko a arewa maso yammacin Yemen, duk da cewa ba ita ƙasashen duniya suka amince da ita a matsayin jagoran gwamnatin ƙasar ba.

Houth tace tana hakan ne domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa a yaƙin da ake yi tsakanin Hamas da Isra'ila a Gaza, kuma ta musanta zargin cewa tana kai hari ne kawai kan jiragen ruwan Amurka da Isra'ila da kuma Birtaniya.

Wani mutum yana duba yadda hari ya yi ɓarna a Sanaa babban birnin Yemen, a ranar 16 ga watan Maris ɗin 2025.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yadda hari ya y ɓarna a Sanaa, babban birnin Yemen.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da yake sanar da harin na ranar Asabar, Trump ya ce ''Za mu yi amfani da ƙarfin gaske har sai mun cimma buƙatarmu.''

"Da taimakon Iran, ƴan tawayen Houthi sun harba makami mai linzami kan jirgin Amurka da kuma kai hari kan ƙawayenmu,'' in ji Trump.

Ya ƙara da cewa ''Ayyukansu na ta'addanci da fashin ruwa da kuma rikici ya jefa rayuwar biliyoyin mutane a cikin hatsari.''

Ya kuma wallafa wani saƙo a kafar sada zumunta da ke cewa idan har ba ku daina ɓarnar da kuke yi ba, za ku ɗanɗana azabar da ba ku taɓa ganin irin ta ba.''

Sai dai Houthi ba ta razana ba a martanin da ta mayar, inda ta ce hare-haren Amurkan ba zai rage goyon bayanta ga Falaɗinawa ba.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce Amurka ba ta da ikon ƙayyade yadda Iran za ta yi hulɗa da ƙasashen duniya.

Saƙon da ya wallafa a shafin X a ranar Lahadi ya ce ''Ku kawo ƙarshen goyon bayan kisan kiyashi da Isra'ila ke yi. Ku daina kashe mutanen Yemen.

Ƙungiyar Houthi ta ɗauki alhakin wasu hare-hare biyu kan wani jirgin ruwa na dakon kayan yaƙin Amurka a tekun Maliya, tana mai cewa ramuwar gayya ce kan hare-haren Amurka. Amma babu wata shaida da za ta tabbatar da iƙirarin nata.

Amma wani jami'in gwamnatin Amurka ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa jiragen yaƙin Amurka sun harbo jirage marasa matuƙi 11 a ranar Lahadi, lokacin da suke ƙoƙarin kai hari kan jirgin ruwan Amurkan.

A ranar Lahadi, sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kiran a kawo ƙarshen duk wasu hare-haren soji a Yemen.