Yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa a wasu ƙauyukan jihar Zamfara

Duk da ikirarin da gwamnatin Najeriya ke yi na cewar tana samun nasarori wajen yaki da matsalar tsaron da ake fama da ita a sassan ƙasar, har yanzu ana ci gaba da samun kai hare hare, musamman a arewaci.
jihohin da lamarin ya fi ƙamari dai su ne Kaduna, Sokoto , Zamfara, da Katsina.
Hari na baya bayan nan dai shi ne wanda ƴan bindigar suka kai wani gari da ake kira Maguru da ke jihar Zamfara inda suka kashe mutum biyar, da kuma sace mutum biyar.
Yan bindiga dai sun kai harin ne garin Maguru da ke yankin ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a daren Assabar zuwa Safiyar Lahadi Lahadi duk a ƙarshen makon nan.
Wani mazaunin garin na Maguru ya shiadawa BBC cewar ƴan bidigar sun kuma yi awon gaba da shanu da dama na jama'ar garin.
Ya ƙara da cewa “Gaba ɗaya sun kore dabbobin garin nan, mutane sun watse, mata da yara suna ta ficewa, mu kaɗai ne yanzu muka rage a wannan gari muna jira Allah ya kawo mana ɗauki'' inji shi.
''A wancan satin da ya gabata ma sun zo sun satar mana shanu, da sati ya sake dawowa wasu yara da suka tafi unguwa suka ci karo da su suka tambaya ko a tare su, muka ce su ƙayale su, tunda ba su yi mana komai ba, sai wasu daga cikin yaran namu suka harbe su, wanda shi yasa ƴan bindigar suka dawo suka shigo garin suka kashe mutum yara hudu, wasu kuma suka samu raunuka'' a cewarsa
Haka kuma ya ce sun debe shanu da tumaki, wanda basu san adadinsu ba, haka kuma babu jami’an tsaro a yankin, sai dai sun dauki makaman da zasu kare kawunansu daga harin yan bindiga.
Rudunar ƴan sandan jihar Zamfara ta bakin kakkakinta ASP Yazid Abubakar, ta ce suna bincike kan satar mutanen da waɗanda aka halaka a yankin na Magurun.
Sai dai ta tabbatar da sace shanun da tumakai a yankin, wanda da zarar sun kammala biciken da suke za su yi ƙarin bayani.
Matsakar tsaro ka iya janyo ƙarancin abinci a Sokoto
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Haka zalika a chan jihar Sokoto ma da ke fama da makamanciyar wannan mastalar ta rashin tsaro, wata ƙungiya ce mai zaman kanta ta Justice for Peace (wato Rundunar Adalci da Hausa) ta yi wani gargaɗi cewar akwai yiwuwar a fuskanci matsalar ƙarancin abinci a jihar da ke maƙwabtaka da Zamfara, idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
A cikin wani rahoto da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi, ta ce kusan kashi 70 bisa ɗari na mazauna ƙauyukkan a shiyyar gabashin Sokoto da ke kan gaba wajen samar da abinci a jiharsun ƙauracewa matsugunansu na asali saboda irin hare-haren da 'yan bindiga ke kai musu babu ƙauƙautawa.
Alhaji Basharu Altine Guyawa Isa, shi ne shugaban ƙungiyar a jihar ta Sokoto ya shidawa BBC cewar ƙanann hukumomi takwas ne a yankin, kuma sun shafe shekaru fiye da shekaru 10 zuwa 11 suna fama da matsalar tsaron.
Sun hada da yankin gabashin sabon birni da Isa, da wani sashe na ƙannan hukumomin Rabbah, da Wurno, da Gwaranyo da wani sashen Gada.
Ya ce ''yanzu babu kashi 70 cikin ɗari na mazauna wannan yanki, saboda wannan mastala, inda da yawa daga cikinsu suka koma jamhuriyyar Nijar, wasunsu na Tudun Sunnah, da Yar Basira, da kuma Dama, da Bangi, wasu kuma na zaune a cikin garin Sokoto, kuma yankin gabashin Sokoto, ne ke samar da kashi tamain cikin ɗari na kayan abincin da ake samarwa a jihar.
Ya ja hankalin gwamnatin jihar ta Sokoto cewar akwai buƙatar ta ɗauki wasu matakai don tunkarar barazanar ƙarancin abincin da za a fuskanta a jihar sakamakon wannan matsalar.
Matsalar tsaron da ake fama da ita a arewacin Najeriya dai ta haifar da gagarumin koma baya ga bangarori da dama, daga ciki har da noma, wanda aka san yankin da shi.











