Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alamomin cutar damuwa da yadda za ku magance ta
Sau da yawa, mutane kan shiga cikin halin damuwa da rashin walwala saboda wasu abubuwa na yau da kullum na rayuwa.
Amma idan mutum ya ci gaba da kasancewa a wannan hali na damuwa tsawon makonni ko watanni likitoci kan ce ya gamu da cutar matsananciyar damuwa.
A kan yi wa wannan cuta kallon ƙaramin abu ko kuma wasu ma su ce rashin haƙuri ne, ko rashin tawakkali ke haddasa ta ga wanda ya gamu da ita.
Sai dai masana sun ce abin da mutane ba su gane ba dangane da cutar shi ne damuwa cuta ce kamar kowace irin cuta da kan kama wani ɓangare na jikin mutum.
Haka kuma cuta ce da ke shafar ƙwaƙwalwa, da tunani wanda mai fama da ita ba shi da iko a kai.
A kwanakin baya, BBC ta tattauna da wata ƙwararriyar likitar lafiyar ƙwaƙwalwa a Abuja, Dakta Dayyaba Shaibu kan matsalar kuma ta lissafa wasu alamomi da ta ce masu cutar na fama da su.
Tsananin baƙin ciki
Babbar alama ga mai fuskantar matsananciyar damuwa ita ce tsananin baƙin ciki na babu gaira babu dalili.
Mai fama da wannan cuta ka iya tsintar kansa a kodayaushe cikin ɓacin rai da rashin walwala.
"Za ka ga kwata-kwata mai wannan cutar ya rasa farin ciki. Abin da zai sa sauran mutane farin ciki, shi zai iya ƙara masa ɓacin rai har ma ta kai mai cutar ga son ƙebewa daga jama'a," In ji Dakta Dayyaba.
Keɓewa da ƙin shiga mutane
Dakta Dayyaba ta ce bayan samun ɓacin rai ga mai cutar, wata alamar da ake gani a masu wannan cuta ita ce keɓe kai.
"Idan a baya an saba ana zama da mutum a yi hira, sai a ga yanzu ya fi son zama a ɗaki shi kaɗai, sannan zai rage walwala.
Ko fita za a yi gaba ɗaya mutanen gidan, mai cutar tsananin damuwa zai ce shi ba za shi ba a tafi a bar shi a gida," a cewarta.
Ɗaukewar barci ko yawaitarsa
Likitar ta ce yana ɗaya daga cikin alamomin matsananciyar damuwa yawan barci ko ƙarancinsa.
"Yawanci masu fama da cutar damuwa za ka ga ko dai barci ya yi musu ƙaranci ko kuma su yi ta barcin ba ƙakkautawa," In ji Dakta Dayyaba.
Rashin son cin abinci ko yawan cin sa
Yana ɗaya daga cikin alamun matsananciyar damuwa tsananin cin abinci ko rashin cin sa, inda har mutum kan ƙara ƙiba ko rage ƙiba.
Haka kuma, likitar ta ce cutar hawa-hawa ce.
"Akwai wadda ta yi tsananin da sai an daɗe ana shan magani kafin a samu sauƙi sannan akwai wadda ɗebe kewa da bayar da shawarwari kawai ke iya magance ta."
Tunanin kashe kai
Sakamakon tsananin ɓacin rai da keɓewa daga jama'a, masu fama da cutar kan yi tunanin rayuwarsu ba ta da amfani, saboda haka sai su nemi mafita - wato kashe kai.
Kisan kai al'amari ne mai sarƙaƙiya wanda ke faɗo wa mutum a tunaninsa a matsayin shi ne mafita.
Ko kuma mutum ya yi tunanin cewa shi ne zai kawo ƙarshen wahalar ko matsin da suke ciki a rayuwa.
Duk da cewa yana da wuya a fahimci dalilin da zai sa wani ya yi yuƙurin kashe kansa, mutanen da ke wannan yunƙurin kaɗai suka san me ke faruwa a cikin zukatansu.
Me ke janyo cutar tsananin damuwa?
Dakta Dayyaba ta ce cutar tsananin damuwa na iya kama kowane jinsi na mutane, sannan ana ganinta a manya da yara duka.
Sai dai ta ce an fi ganin ta a mata da matasa da suke daidai shekarun balaga.
Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce sau da yawa idan wani iftila'i ya samu mutum ne yake shiga halin tsananin damuwa, kamar rasa wani makusanci, ko kora daga wajen aiki, ko haihuwa mai cike da tangarɗa, da dai sauransu.
Dakta Ɗayyibah ta ce yanayin halittar ɗan'adam na taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan matsala.
"Wani Allah ya halicce shi da juriya. Ko da abin tashin hankali ya same shi zai daure kuma ba zai zauna masa a rai ba.
"Wani kuma ba shi da haka. Allah ya halicce shi yana da rauni kuma ba shi iya jure jarrabawa. To irinsu ne suka fi gamuwa da matsalar tsananin damuwa," a cewar likitar.
Amma ta ce wani lokaci ma haka kawai mutum kan shiga damuwa har ta zamar masa wannan cuta.
Ana warkewa daga cutar damuwa?
Dakta Dayyaba ta ce ana warkewa tsaf daga wannan cuta idan aka samu taimakon da ya dace.
"Idan aka lura wani ya fara nuna alamomin wannan cuta, abu na farko shi ne a kai shi asibiti," in ji ta.
Akwai magunguna da hanyoyin da ake bi a asibiti ga masu fama da cutar damuwa.
"Muna ba da magunguna, sannan akwai likitoci na musamman da aikinsu kawai ɗebe wa masu wannan cuta kewa, da ba su shawarwari kan yadda za su tafi da rayuwarsu."
Sannan ta ce makusantansu su riƙa jan su a jiki, da nuna musu kulawa.
"Duka waɗannan ne ke samar da kwanciyar hankali a tare da masu cutar har su samu lafiya," in ji likitar.