Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda neman waraka ta hanyar kaho ya koma na zamani
Likitoci da kwararru tuni suka fara zamanantar da sana’o’in gargajiya na ƙasar Hausa ko ma a ƙasashen Afirka da suka haɗa da yin kaho.
A baya dai mutane kan je wurin wanzamai domin a yi musu kaho inda kuma wanzaman kan yi amfani da aska su tsaga wurin da ciwo yake sannan kuma su kafa kahon dabba.
To amma yanzu maimakon kahon dabba, yanzu suna amfani da wasu ‘yan kofunan roba waɗanda ba sa barin taɓo sannan kuma ba sa ɗauke da kwayar cutuka kamar dai yadda masu sana’ar suke faɗa.
Ahmad Babanyaro Shamsudeen – kwararren mai kahon Hijama ne a wani asibitin yin kohon da ke Abuja kuma ga abin da ya shaida wa BBC dangane da bambancin kahon zamanin da da wanda suke yi.