Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gobarar daji na yaɗuwa a Canada
Gobarar daji ta lashe sassa da dama na dajin yammacin Canada kuma ta doshi biranen Arewacin Alberta da kuma British Columbia.
Masu kashe gobara sun ce lokacin da ake yawan samun tashin gobarar dajin ya kunno kai kuma sun yi hasashen cewa lamarin zai ƙazance a bana.
Wata gobarar da ta tashi a Alberta ta riƙa ci har ta kai kusa da garin Fort McMurray mai albarkar mai.
Dubban mutane ne aka umarta da yin ƙaura daga gidajen su a garin Fort McMurray na Arewacin Canada saboda mummunar gibarar dajin dake shirin afkawa garin.
Hukumomi sun buƙaci jama’ar larduna huɗu na yankin su yi ƙaura kafin yammacin yau domin samun damar gudanar da ayyukan gaggawa na kare yankin daga gobarar dajin.
Fort McMurray gari ne dake cikin dausayin gandun daji, kuma a ƙarƙashin ƙasar wajen akwai albarkar mai, ga kuma tsananin zafin rana da aka yi fama dashi a yankin, lamarin da ya busar da gandun daji da tsirrai.
A lokacin wani taron manema labarai, Josee St-Onge, jami’in kashe gobarar daji na yankin ya bayar da bayanin halin da ake ciki.
Ya ce: "Yawan gobarar da ake samu ya ƙaru a arewa maso gabas, saboda tsananin zafin da ke gangarwa daga kudu maso yamma. Gobarar tana ƙazancewa sosai. Hayaƙi ya turnuƙe sama ta yadda ko hazo ba a iya gani. A yanzu haka ma an janye jami’an kwana-kwana daga wajen da wutar ke ci saboda kare rayuwar su. Za mu ci gaba da ƙoƙarin kashe wutar ta amfani da kayan aiki na sama, kamar jiragen sama da zasu taimaka domin cimma nasarar aikin cikin sauki."
A shekarar da ta gabata ma Canada ta yi fama da gobarar dajin, kuma hukumomi sun ce itace mafi muni a tarihi.