An yi rana mafi tsananin zafi a tsawon shekara 60 a China

Birnin Beijing na shan zafi mafi tsanani da aka taɓa gani a watan Yuni cikin sama da shekara 60, inda yanayi ya kai tsananin da zai iya tafasa ruwa, da maki 41.1 a ma'aunin selsiyas, a cewar hukumomin kula da yanayi na China.

Birnin na fuskantar dogon yanayin zafi mai tsanani, kuma lamarin zai ci gaba har zuwa ƙarshen watan Yuni.

Jami'ai sun ce Alhamis ce, rana mafi tsananin zafi a watan Yuni, tun da aka fara taskace bayanai cikin 1961 a ƙasar.

Tsawon watanni da dama an fuskanci zafi mai tsanani a ƙasar China bana, abin da ya janyo fargabar samun ƙarancin makamashi.

A watan jiya Shanghai, birni mafi girma a ƙasar, da yawan mutane kimanin miliyan 25 a gaɓar tekun gabashi, ya fuskanci rana mafi zafi cikin watan Mayu a tsawon ƙarni.

Akwai mutane sama da miliyan 21 da ke zaune a Beijing, babban birnin ƙasar a ɓangaren arewa.

A ranar Alhamis, wata tashar bin diddigin yanayi a birnin, ta ba da rahoton cewa zafi ya kai maki 41.8 a ma’aunin salsiyas.

Tun da farko, hukumomi sun ankaras da mutane cewa, rana za ta buɗe ta yi launin ruwan goro, wannan shi ne gargaɗin yanayi na kusa da mafi tsananin zafi, inda suka ce yanayin zai iya kai wa salsiyas 39 cikin ‘yan kwanakin nan har zuwa Asabar.

Ofishin kula da yanayi na ƙasa ya sake yin jan hankali a makon jiya game da yiwuwar samun matsanancin zafi - mako biyu kafin yadda zafin ya saba zuwa a shekarun baya.

Hukumomi a Beijing da Tianjin da kuma sauran birane a arewaci da gabashin China, sun shawarci mutane su dakatar da fita waje zuwa aiki a lokacin da rana ta take.

Kuma su nemi taimakon jami'an lafiya matuƙar suka fuskanci larurorin da akan yi fama da su a yanayin matsanancin zafi.

Wasu kuma sun gargaɗi mutane da cibiyoyin kasuwanci a kan su taƙaita amfani da lantarki.

A makon jiya, Hukumar kula da Makamashi ta Ƙasa ta aiwatar da atisayen ko-ta-kwana irinsa na farko a yankin gabashin China, inda ta kwatanta halin da za a iya shiga a lokacin da aka samu ƙaruwar wutar lantarki, da kuma a lokacin da aka samu gagarumar ɗaukewar lantarki.

Yanayin na iya kasancewa "akasari mai tsanani" bisa la'akari da harkokin tsaron babban layin lantarki, a cewar hukumar.

A birnin Tianjin na gaɓar ruwa, ƙarin buƙatun lantarki don kunna na'urar sanyaya ɗaki, ya ƙara nauyi a babban layin lantarki da kashi 23% bara.

Ma'aikata a ofishin samar da lantarki sun riƙa sintiri a hanyoyin ƙarƙashin ƙasa don tabbatar da ganin wayoyin lantarki suna aiki yadda ya kamata, a cewar jami'ai.

An kuma samu ƙaruwar yanayin zafi da aƙalla salsiyas biyu a yankuna da yawa na nahiyar Asiya a lokacin zafin watan Afrilu.

Masana sun bayyana cewa yankin na fuskantar "zafi mafi tsanani a tarihi".

Ƙasashen Thailand da tsibirin Laos da Bangladesh da kuma Indiya duk sun samu yanayin zafin da ya kai salsiyas 45 a watan Afrilu.

Tsananin zafin dai ya haddasa mace-mace da rashin lafiyar da ke kai wa ga kwantar da mutane a asibiti cikin wasu ƙasashe. An kuma samu narkewar kwalta a kan tituna, har lamarin ma ya shafi sauran ababen more rayuwa.

Zafin na ɗaya daga cikin iftila'i mafi muni da aka gani a duniya, inda yake haddasa mutuwar dubbai duk shekara.