Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa sarakuna ke kai wa gwamnoni gaisuwar sallah?
Manyan masarautun ƙasar Hausa kan gudanar da hawa iri daban-daban a lokacin bikin sallah.
Daya daga cikin irin waɗannan hawa mafi shahara shi ne wanda, a yanzu, sarki kan kai wa gwamna gaisuwa, wanda misali a Kano akan kira Hawan Nasarawa, a Zaria da Katsina kuma akan kira su da Hawan bariki.
Sai dai irin wannan hawa na da tarihi mai tsawo a faɗin ƙasar ta Hausa.
Sarkin Dawakin Tsakar Gida na Masarautar Katsina, Hassan Usman Kabir ya ce “wannan al’ada ce da ta samo asali tun a lokacin Turawan mulkin -allaka.”
Shi kuwa Nasir Wada Khalil, masani kan al’adar masarauta a kasar Hausa ya ce hawan Nasarawa ‘hawa ne na mubaya’a ga hukuma.’
To sai dai ba a lokaci guda ne aka fara gudanar da irin wannan hawa ba.
Za mu duba asalin wannan hawa a masarautu biyu na kasar Hausa - Kano da Katsina.
Hawan Nasarawa
An fara hawan Nasarawa ne a tsakanin shekarun 1903 zuwa 1918, lokacin Sarkin Kano Abbas, kamar yadda wani masanin tarihin Masarautar Kano, Muhammad Fatihu ya tabbatar wa BBC.
A wannan lokaci babban Baturen yankin shi ne Dakta Featherstone Cargill, wanda shi ne ya raba Kano zuwa gundumomi.
Fatihu ya ce a lokacin hawan Nasarawa sarki kan fito ta kofar kudu, daga nan sai ya tafi gidan sarki da ke a unguwar Nasarawa, sannan ya nufi gidan gwamna.
Bayan ya fito daga gidan gwamna yakan bi ta titin Lodge Road, sai ya bi ta Bank Road, ya shiga unguwannin Sabon Gari, da Fagge, sai ya bulla ta Kofar Mata, ya kuma shiga ta Kofar Fatalwa.
Haka nan wani masanin al’ada na Masarautar Kano, Nasir Wada Khalil ya ce sunan Hawan Nasarawa an samo shi ne daga kalmar ‘Nasara’, wadda ke nufin Bature.
Kasancewar a lokacin hawan sarki kan je unguwar ta Nasarawa ne domin ganawa da gwamna ya kai masa gaisuwa tare da tattauna abubuwan da suka shafi harkar mulki.
Hawan Bariki (Katsina)
Hassan Kabir Usman shi ne Sarkin Dawakin Tsakar Gida na Masarautar Katsina, ya tabbatar wa BBC cewa an fara yin Hawan Bariki ne a Katsina a lokacin sarki na farko daga gidan Sulluɓawa, wato Sarki Muhammad Dikko.
Kuma an fara hawan ne a lokacin wani Baturen Razdan da ake kira Mr Palmer.
Duk da cewa Turawan mulkin-mallaka sun fara isa Katsina ne a 1903, lokacin Sarki Abubakar na gidan Dallazawa, babu jituwa mai karfi tsakanin Masarautar Katsina da Turawan mulkin-mallaka har sai bayan naɗa Sarki Muhammad Dikko.
A wannan lokaci Sarki Dikko kan tara hakiman ƙasar Katsina domin kai wa Turawa gaisuwar sallah a unguwar Modoji, wadda aka fi sani da G.R.A a yanzu.
Modoji ta kasance uguwa ce da ke wajen gari, inda sarki ke ajiye dawaki, sai dai daga baya an mayar da Turawa da ma’aikatansu can da zama.
A duk lokacin da sarki da hakimai suka kai ziyara, Baturen Razdan (Resident officer) kan yi musu jawabi kan ayyukan da yake so a gudanar na tafiyar da kasa.
Tun daga wancan lokaci ne duk sarakunan da suka biyo baya, wato Usman Nagogo, da Kabir Usman, da kuma sarki mai ci a yanzu Abdulmumin Kabir, kan kai irin wannan ziyara.
Bayan samun ƴancin kan Najeriya, sarki a Katsina kan kai ziyara ne gidan gwamna, wanda har yanzu yake a unguwar ta Modoji, wadda a yanzu ake kira G.R.A.
Yanzu haka an kwashe shekaru 115 kenan tun bayan fara wannan al’ada a ƙasar ta Katsina.
End of Karin labaran da za ku so ku karanta:
Tarihi dai ya nuna cewa gabanin zuwan Turawa sarakai a kasar Hausa kan je Sokoto ne domin kai wa Sarkin Musulmi gaisuwa a kowace sallah, sannan su yi hawa.
Sai dai bayan zuwan Turawa an rage karfin iko da Sokoto take da shi, wannan ne dalilin da ya sanya sarakuna suka fara yin hawa a masarautunsu.
Daga baya kuma Turawa sun ga dacewar cewa bayan yin hawan sallah, ya kamata su rinka zuwa suna gaishe su, domin ‘talakawa su san cewa sarakunan a karkashinsu suke,’ kamar yadda Muhammad Fatihu ya bayyana.