Tarihin da aka kafa a gasar Firemiya ta kakar wasan 2023/2024

Za a kammala gasar Premier League ranar Lahadi 19 ga watan Mayu da wasa 10 a filaye daban daban a kuma lokaci daya.

Wannan ita ce ɗaya daga babbar gasar tamaula ta Ingila da ba a taba yin irinta ba a tarihi - ga jerin wasu abubuwan tarihin da aka yi.

Cin ƙwallaye:

Kawo yanzu an zura ƙwallo 1,209 kwawo yanzu, kakar da aka fi zurawa a raga ita ce ta 2022/23, wadda a wasa 380 aka ci 1,084 a raga.

Sai dai a kakar 1992/93 wadda aka yi wasa 462, an ci kwallo 1,222, kenan saura kwallo 14 ake bukata a wasan karshe ranar Lahadiya zama an doke tarihin yawan zura kwallaye a raga a wasan.

Erling Haaland ne kan gaba a yawan cin kwallaye:

Dan wasan Manchester City, Erling Haaland shi ne kan gaba a cin kwallaye a bana, wanda yake da 27 a raga.

A bara shi ne ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ya zura kwallaye da yawa a raga mai 36 jimilla.

  • Erling Haaland Manchester City 27
  • Cole Palmer 20 Chelsea 22
  • Alexander Isak Newcastle United 20
  • Ollie Watkins Aston Villa 19
  • Dominic Solanke Bournemouth 19
  • Mohamed Salah Liverpool 18
  • Heung-min Son Tottenham 17
  • Phil Foden Manchester City 17
  • Bukayo Saka Arsenal 16
  • Jarrod Bowen West Ham United 16

Wadanda ke kan gaba a cin kwallo a 2022/23

  • Erling Haaland Manchester City 36
  • Harry Kane Tottenham 30
  • Ivan Toney Brentford 20
  • Mohamed Salah Liverpool 19
  • Callum Wilson Newcastle United 18
  • Marcus Rashford Manchester United 17
  • Martin Odegaard Arsenal 15
  • Ollie Watkins Aston Villa 15
  • Gabriel Martinelli Arsenal 15

Semenyo, Bournemouth

Cin kwallaye na kayatar da wasan tamaula, kuma a kakar nan an ci wasa a karawar da ake tsammani kungiya za ta yi rashin nasara, amma daga baya ta lashe fafatawar, inda aka yi haka har sau 62.

Karon farko da aka samu wannan kwazon tun da aka fara gasar Premier League a tarihin wasannin daga 2008/08.

An kuma farke kwallo a wasa sau 223, karo na biyu a wannan kwazon a gasar ta Premier League tun bayan 237 da aka yi a 1993/94.

Aston Villa da Liverpool

Raba kwallo tsakanin 'yan wasa kan taimaka wa kungiya wajen mamaye gasa, yana kuma nuna kwazo da kwarewar ƴan kwallo da kociyan dake jan ragama.

An bayar da ƙwallo zuwa abokin wasa kamar yadda ya kamata kaso 83 cikin 100, wato passing, wannan ita ce bajinta ta farko daga kaka 16 tun daga 2008/09.

Aston Villa ta zama ƙungiya ta takwas daga Premier League a kaka uku baya da ta samu gurbin Champions League, ba cikin wadanda suka saba zuwa wasannin ba.

Yadda aka yi neman lashe Premier League

A karo na uku kenan a jere ake fayyace wadda za ta lashe Premier League a ranar karshen gasar, kuma karo na 10 a tarihi.

Makin da yake raba ƙungiya ta daya da ta biyu baya wuce 1.51, sai dai tun daga 1992/93 ba a samu tazarar maki mafi karanci ba tsakayin ta daya da ta biyun teburin.

Ƙungiyoyi bakwai ne suka ja ragamar teburin Premier League a kakar nan.

Kwanakin da ƙungiya ta yi a saman teburin Premier a kakar 23/24

  • Liverpool kwana 87
  • Arsenal kwana 76
  • Man City kwana 76
  • Tottenham kwana 26
  • Brighton kwana 7
  • Newcastle kwana 7
  • West Ham kwana 2

An samu matasa da yawa da suka fara buga Premier League a bana

Ƴan wasan waje ke bayar da gudunmuwa da yawa a gasar Premier League, sai dai wannan karon a samu matasa 61 da suka fara yin kakar bana da su, karo na uku da aka samu da yawa kenan.

Haka kuma ƴan wasan Ingila sun ci kwallo 359 a bana a gasar da suka zura kwallaye da yawa tun bayan 2001/02 - inda ƴan wasan Ingila shida ke cikin goman farko a yawan cin kwallaye a gasar.

Cole Palmer

Ƴan wasa 68 daga kasashen duniya ne suka buga Premier League a kakar nan, wadanda ake fara wasa da su a cikin fili tsakanin ƙungiyoyi 20 da suka kara a bana.

Tun daga sauya fasalin Premier League daga 1992//93 an samu ƴan wasa 123 daga kasashen duniya da suka buga babbar gasar tamaula ta Ingila.

Matsakaicin shekarar ƴan wasa a kakar nan ya fara daga 26 da kwana 169 kan fara - mafi karancin shekara tun daga 2008/09 kuma karo na hudu a karancin shekara a gasar.

’Yan kallo da yawa a filayen wasanni

Filayen wasa kan dauki ƴan kallo kaso 98.7 cikin 100 a Premier League ta kakar nan, wadda ta yi kan-kan-kan da tarihin kakar bara.

Daga cikin ƙungiyoyi 20 da suke buga gasar kakar nan, guda 18 kan samu ƴan kallo kaso 97 cikin 100.

Wasan Liverpool da Tottenham - Premier League

Akwai wasa 10 da aka kalli kai tsaye a talabijin da mutum miliyan uku kowanne suka gani a Burtaniya a kakar nan, kakar da aka fi kallo wadda ta haura ta ita ce 2019/20.

Jimilla mutum miliyan 37.7 suka kalli wasa kai tsaye a talabijin da kuma sharhin tamaula na BBC Match of the Day, kimanin kaso 59 cikin 100 a Burtaniya.

Yadda duniya ke bibiyar Premier League

Gasar Premier League ta zama mafi girma mai dan karen farinjina a wasan da ake bibiya a Burtaniya da kuma fadin duniya.

An nuna gasar tsakanin kasashe 189 daga mambobin majalissar dinkin duniya 193 tsakanin gida miliyan 900.

Mutum biliyan 1.87 suke bibiyar Premier League a fadin duniya, wadanda ke tafka muhawara a duk mako a kafar sada zumunta da ta sadarwa.

An samu kaso 34 cikin 100 da suke bibiyar Premier League sau da kafa a kaka ta hudu a jere kenan.

Mutane da yawa sun kalli wasa Arsenal da City a Nashville

Wasan Manchester City da Arsenal da aka buga a Premier League ranar 31 ga watan Maris ya zama kan gaba da aka fi kallo a tarihin Amurka, inda mutum miliyan 2.12 da suka kalla a kafar sadarwa ta NBC.

Wasu karin kididigar Premier League

An fara kakar bana daga 11 ga watan Agustan 2023

Wadanda suka fadi daga kakar bana

  • Burnley
  • Sheffield United

Gurbin Champions League

  • Manchester City
  • Arsenal
  • Liverpool
  • Aston Villa

Wasannin da aka buga: 370

Kwallayen da aka ci kawo yanzu: 1,209

Wanda yake kan gaba a cin kwallaye: Erling Haaland Man City 27 a raga

Fitatcen mai tsaron raga: David Raya (Wasa 16 kwallo bai shiga raga ba)

Wasan da aka ci kwallo da yawa a gida: Chelsea 6–0 Everton (15 Afirilun 2024)

Wanda aka ci kwallo da yawa a waje: Sheffield United 0–8 Newcastle United

(24 ga watan Satumbar 2023)

Wasannin da aka ci kwallaye da yawa a raga:

Sheffield United 0–8 Newcastle United (24 ga watan Satumbar 2023)

Chelsea 4–4 Manchester City (12 ga watan Nuwambar 2023)

Newcastle United 4–4 Luton Town (3 ga watan Fabrairun 2024)

Yawan cin wasa 8 a jere: Arsenal da Manchester City

Wasa 22 ba tare da rashin nasara ba a jere: Manchester City

Wasa 13 ba tare da nasara ba: Everton da Sheffield United

Wasa shida a jere da rashin nasara: Burnley da Sheffield United

Wasan da ya dauki ƴan kwallo 73,612

Manchester United 3–0 West Ham United (4 ga watan Fabrairu 2024)[1]

Wasan da bai yi mutane ba a sitadia 10,421

Bournemouth 0–0 Chelsea (17 ga wwatan Satatumba 2023)