Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda TikTok ke tunzura matasan Larabawa son kudi
Mohamed Ghadour yana shafe sa’a hudu a kullum da wayarsa yana hada sabbin hotunan bidiyo na TikTok.
Ya ce abin ba a cewa komai, domin a duk wata yana samun abin da ya kama daga dala 1000 zuwa 3000.
Kodayake manhajar TikTok ba ita kadai ba ce hanyar samun kudinsa, to amma tana da muhimmanci sosai a wannan fanni a wurinsa.
Ya ce akwai mutane da yawa da ya sani da suke samun har kusan dala dubu 10 daga manhajar ta yada hotunan bidiyo.
Mohamed ya ce shi da sauran masu amfani da TikTok kamarsa suna samun kudi ne ta hanyar tsarin nan na asusun da masu manhajar ke biyan wadanda suka fi sanya hotunan bidiyo da yawa (Creator Fund).
Inda suke hada guiwa da masu kamfanoni da ke tallata kayansu ko ayyukansu ta shafin.
Ya ce yi wa wani kamfani bidiyo na tallata hajarsa kan sama mishi kusan kashi 60 cikin dari na kudin kayan a duk lokacin da ya yi.
Duk da cewa masu bibiyar abubuwan da Mohamed ke sanyawa yawanci suna bin shafinsa ne saboda bidiyo da yake yi na harkokin ilimi,
kan yadda za a tallata abu ta intanet, inda yake da mabiya sama da rabin miliyan, kowannensu yana da buri daya ne kawai, burin kuwa shi ne yadda zai yi kudi da sauri.
Kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna yawan mutanen da ba su da aiki a kasashen Larabawa ya kai kusan miliyan 14.3 a 2021, kuma yawancinsu matasa ne.
Yadda ake yin wayoyi masu kyamara iri-iri da kuma manhajoji irin su Tik Tok, wadanda za ka iya yin siddabaru da hoto iri daban-daban, yadda kake so, kuma ka yada su.
Wannan wata dama ce ga mutane da yawa ta yin fice da kuma samun kudi, wadda ba za su iya bari ta wuce su ba.
A ‘yan shekarun nan aikin masu kirkirar abubuwa da kuma tasiri a shafukan sada zumunta da muhawara sun zama wasu fitattun ayyuka masu zaman kansu.
Wasu ‘yan kalilan din masu amfani da shafukan sada zumunta kan samu kudade sosai fiye da yawancin masu ayyuka na yau da kullum da aka sani.
Mai shekara 30, Mohamed, wanda dan Masar ne da ke zaune a Saudi Arabia, sa’ana ne, to amma yana samun kusan ninki 10 na abin da nake samu a lokacin ina dan-jarida a kasashen Larabawa.
‘’Za ka iya samun dala dubu 10 a wata daya ta hanyar Tik Tok, idan kana so.
Ya danganta ne ga yawan mabiyanka da kuma irin bidiyon da kake yi,’’ in ji wani fitacce a TikTok, Ismael Elabras.
Ismael – wanda inkiyarsa ita ce "Elkhal", ko "Kawu" a Larabci, yana da mabiya kusan miliyan daya.
Yayin da Ismael mai shekara 50, dan kasar Lebanon, wanda mai tasiri ne da fadi a ji a shafukan sada zumunta da muhawara, yake samun kudi ta hanyar sanya hotuna a TikTok, kamar Mohamed, to amma shi yana samun karin kudinsa ta wata hanyar daban.
Shi Ismael, yana kuma yin bidiyo da sauran abubuwa domin amfanin wadanda ke neman aiki da kaura zuwa wata kasa da kuma masu neman tallafin karatu.
Ismael yana samun karin kudi daga masu kiransa su tattauna da shi bayan sun kalli bidiyonsa, domin ya ba su shawara ko karin bayani.
Ya ce idan ya yi haka to zai iya samun sama da albashinsa na wata a cikin ‘yan kwanaki.
'‘Ka sayar da ilimi da kwarewar da kake da su domin samun kudi. Abu ne na cude-ni-in-cude-ka,’’ in ji shi.
To amma fa ba kullum ake kwana a gado ba.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Fada wa tarko
Ba kodayaushe ba ne amfanin TikTok a kasashen Larabawa ke kai fitattu a shafukan sada zumunta da muhawara ga nasara da samun arziki, a wani lokaci abin yakan kai wasu har ga gidan yari.
An daure wasu mata biyu ‘yan Masar masu sanya hotunan bidiyo a TikTok, a gidan yari, bayan da kotu ta same su da laifin safarar mutane.
Haneen Hossam ta tafi gidan yari na tsawon shekara uku, yayin da Mawada al-Adham za ta yi shekara shida a gidan sarka a kan laifin, wanda dukkaninsu sun musanta.
Masu rajin kare hakkin dan-Adam sun ce an daure matan ne, a bisa irin kuntatawar da hukumomin Masar ke yi.
Hukumomin na harar mata masu tasiri a shafukan intanet, a kan tuhumar da ta keta-haddin ‘yancinsu na sirri da damar bayyana ra’ayi da kuma rashin nuna bambanci.
Ba dukkanin kalamai ba ne na samun makudan kudade a TikTok za a iya tantancewa.
Shimaa, ‘yar Moroko mai shekara 19, wadda fitacciya ce a shafukan sada zumunta da muhawara, ta ce ba ta samun kudi sosai daga hotunan bidiyo na kai tsaye da take sanyawa a TikTok.
Kodayake ta ki bayyana yawan kudin da take samu, ta ce ta fi samun kudi ta shafinta na YouTube, a kan na TikTok.
Ta ce tana amfani da shafinta na TikTok ne domin jan mabiya zuwa sauran shafukanta na intanet.
Kamar dai a sauran shafukan sada zumunta da muhawara, yawan mabiyanka yawan kudin da za ka iya samu.
To amma a nan TikTok ya bambanta, domin ba ka bukatar miliyoyin mabiya kafin ka samu kudi.
Ana daukar masu shafin da yake da mabiya tsakanin dubu 50 da dubu 150 a matsayin kananan masu tasiri.
Kuma idan kana daga cikin irin wadannan to kafin ka samu kudi kai tsaye daga TikTok, na bidiyon da kake sanyawa, sai ya kasance mutane akalla dubu 100 sun kalli bidiyon a cikin kwana 30.
Duk da cewa TikTok na yada bidiyo ga dukkanin masu amfani da shafin, ba dukkanin masu bibiyar shafin mutum ba ne, ke sa ya samu wannan damar ba.
Tarin mabiya matasa
Ismael da Mohamed, sun ce akwai kuma wata sabuwar hanyar ta samun kudi a tsakanin matasa masu amfani da shafin na TikTok, inda suke neman wasu fitattu su taimaka wajen yada abubuwan da suke yi.
A kwanan nan wata matashiya mawakiya ‘yar Syria, Fia Younan ta samu taimakon kusan dala dubu 25 daga masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara, domin ta nadi wakarta.
To amma Ramy Assaf, mai bincike a fannin arzikin da ake samu ta harkokin intanet a Jami’ar Soas, da ke London (School of Oriental and African Studies Soas), ya ce galibi ana kambama yawan mutanen da ke samun kudi ta TikTok.
Kuma yawan kudin da ake cewa ko kuma suke cewa suna samu ba lalle ne ya zama gaskiya ba.
Ya kara da cewa, "Kashi daya cikin dari na masu amfani da TikTok ne suke samun makudan kudade.
Amma kashi 99 cikin dari ba sa samun wadannan kudade da yawa, saboda ba su da mabiya.''
Saboda haka, kamfanoni ba sa amfani da su wajen tallata hajojinsu, a don haka ba a aika musu da wani tallafi ko wani kudi na amfani da shafin, in ji masanin.
Fitattun masu amfani da shafin ne kawai suke samun kudi, a cewar malamin.
Duk da cewa Shimaa tana da mabiya miliyan 1.2 a TikTo, to amma ta ce kudaden da take samu ba masu yawa ne cancan ba.
Babu wasu alkaluma takamaimai na yawan masu amfani da TikTok a kasashen Larabawa.
To amma kakakin wani kamfani a Gabas ta Tsakiya ya ce sama da mutum miliyan dubu biyu suna da manhajar a fadin duniya.
Masu kamfanin manhajar TikTok, wato ByteDance, sun bayyana cewa kashi 41 cikin dari na masu amfani da manhajar tasu ‘yan tsakanin shekara 16 zuwa 24 ne.
Wanda wannan kashi, shi ne ya kunshi kusan kashi 30 cikin dari na yawan mutanen kasashen Larabawa.
A watan Fabrairu na 2020, manhajar TikTok ta samu kusan dala miliyan 50.4 daga kudaden da masu amfani da shafin ke kashewa, kamar yadda kididdigar shafin Statista (mai bincike) ta nuna.
A yanzu dai babban wanda ya fi cin ribar amfani da TikTok shi ne ByteDance, wato kamfanin da ke da manhajar.
Kamfanin ya ce kudin da yake samu ya ninka biyu zuwa dala biliyan 34.3 a shekarar da ta wuce.