Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An samu tauraruwar Tiktok da laifin safarar mutane a Masar
An tsare wata tauraruwar TikTok a kasar Masar kwanaki biyu bayan ita da wata tauraruwar aka yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na lokaci mai tsawo kan samun su da aikata laifin fataucin mutane.
Haneen Hossam, mai shekara 20, ta wallafa wami faifen bidiyo a ranar Litinin inda a ciki take neman a yi mata sassauci, tana mai cewa ba ta zalunci kowa ba.
A ranar Asabar ne wata kotu a birnin Alƙahira ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekara 10 a gidan kaso a yayin da ba ta cikin kotun.
Ita kuma abokiyar tuhumar ta Mawada al-Adham, mai shekara 23, wacce ta halarci zaman kotun an yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru shida.
An zarge su da yin amfani da damar da suka samu a kan wasu 'yan mata don neman kudi ta hanyar wata manhajar yaɗa faya-fayen bidiyo ta TikTok.
Hukuncin na zuwa ne watanni biyar bayan da wata kotu ta sauya hukuncin zaman gidan kaso da ta yanke wa Hossam da Adham kan ''saba martabar iyalai'' ta hanyar faifen bidiyon da suka yaɗa a manahajar ta TikTok.
Masu rajin kare hakkin bil adama sun ce gurfanar da matan biyu wani ɓangare ne na yunkurin da gwamnatin kasar Masar ke yi na ɗaukar tsauraran matakai a kan taurarin shafukan sada zumunta mata kan tuhumar da ta saba wa 'yancin yin abubuwan da suka shafi rayuwarsu, da 'yancin fadin albarkacin baki.
Hossam, wacce daliba ce a Jami'ar Alkahira, na da mabiya 900,000 a TikTok, kuma an fara kama ta a cikin watan Afrilun shekarar 2020 bayan da ta yaɗa wani bidiyo da take yin kira ga mabiyanta mata da su shiga wani dandalin yaɗa bidiyon na daban wato Likee, tare da kwaɗaita musu cewa za su samu kudi ta hanyar yada faya-fayen bidiyo a ciki.
Daga bisani ne masu gabatar da ƙara suka tuhume ta da "saɓa wa Ka'idoji da martabar iyalai".
Adham, wacce ke da mabiya miliyan uku a TikTok kana maiya miliyan daya da dubu dari hudu a shafin Instagram, an zarge ta da aikata laifi irin na Hossam bayan wata guda, bayan da ta yaɗa abin da masu gabatar da kara suka ce faye-fayen bidiyo na ''baɗala'' wanda a ciki ta riƙa bin wasu waƙoƙi da leɓɓanta kana tana rawa sanye da tufafin ƙawa.
A cikin watan Yuli ne, wata kotun tattalin arziki ta yanke wa Hossam da Adham daurin shekara biyu a gidan kaso.
A watan Yuli kum an kuma ci tarar su fam 300,000 na kasar Masar, kwatankwacin dala ($19,140; da fam din ingila £13,800) ko wannensu.
A cikin watan Janairu ne aka sauya hukuncin a ka daukaka karar da aka yi, kuma aka sake su bayan wata guda. Amma kuma aka sake gabatar da sabuwar tuhuma kan fataucin mutane.
Kamar yadda shafin yanar gizo na kafar yada labarai mallakar kasar ya wallafa, masu gabata da karar sun zargi matan na ''amfani da 'yan matan ne ta hanyar da ta saba wa ƙa'idoji da martabar "al'ummar kasar Masar don neman abin duniya''.
Shafin intanet na Youm7 ya bayar da rahoton cewa tuhumar na da alaka da wata kungiya da Hossam ta yi wa talla a manahajar yada bidiyo ta Likee da kuma faya-fayen bidiyo da Adham ta saka a shafukan Instagram da kuma manahajar TikTok.
A ranar Lahadi ne, wata kotun hukunta masu aikata muggan laifuka ta samu Hossam da Adham da aikata laifin kana ta yanke musu hukuncin zaman gidan kaso. An kuma yanke wa wasu maza uku da suka taimaka wa matan hukuncin daurin shekara shida.
Lauya mai kare Hossam, Hani Sameh, ya ce an yanke mata dogon hukuncin zaman gidan kaso ne saboda bata bayyana a gaban kotu ba, duk da cewa "ƴanci da doka ta bata ne na kada da bayyana''.
"Za mu nemi yadda za a gyara lamarin hukuncin saboda akwai ruɗani tsakanin hukuncin da kuma ƙa'idojin da kotu ta bi wajen yanke hukincin,'' ya shaida wa Thomson Reuters Foundation.
"Muna cike da fatan za a rage tsawon hukuncin daurin ko kuma a sake ta."
Ita ma Hossam ta nuna kaɗuwarta game da hukuncin kana ta nemi afuwa daga hugaba Abdul Fattah al-Sisi a wani bidiyon da ta saka a shafin Instagram sa'oi kafin a cafke ta.
"Shekara 10! Ban aikata wani abu na rashin ɗa'a ba da zan cancanci duk wadannan. Na taba zaman gidan kaso na watanni 10 kuma ban ce komai ba bayan da aka sako ni....me yasa kuke son kusa sake tsare ni?" ta ce.
Reda Eldanbouki ta cibiyar Women's Center for Guidance and Legal Awareness, wata kungiya mai zaman kanta a Masar, ta ce hukuncin ''ya yi tsauri sosai'' kuma ya danne 'yancin mata da fadin albarkacin baki da kuma ra'ayi.