Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa wasu matasan Larabawa suke amfani da maganin ƙarfin maza
A wani shagon sayar da magani a unguwar Bab al-Shaaria mai ɗumbin tarihi da ke tsakiyar birnin Alkahira, mai sayar da maganin gargajiya al-Habashi ya baje-kolin abin da ya kira 'magungunana masu ban mamaki'.
Mista Habashi ya yi suna sakamakon sayar da maganin ƙarfin maza a babban birnin na Masar. A tsawon shekara biyu da suka gabata, ya ga sauyi a abin da kwastamominsa suke so.
"Akasarin maza a halin yanzu suna neman maganin ƙarfin maza daga kamfanonin ƙasashen yamma," in ji shi.
Kamar yadda bincike da dama ya nuna, matasan Larabawa na yawan amfani da magunguna kamar su sildenafil da vardenafil da kuma tadalafil.
Duk da hujjojin da ake da su, abin mamaki shi ne akasarin matasan da BBC ta yi magana da su a kan titunan Masar da Bahrain sun musanta amfani da magungunan ƙara ƙarfin maza ko kuma saninsu.
Wasu ma sun ƙi amincewa su yi magana a kan lamarin tun da farko inda suke ganin yin magana a kan batun ya saɓa wa al'ada.
Wani bincike da aka gudanar a 2012 ya nuna cewa Saudiyya ce ke kan gaba wajen amfani da maganin ƙara ƙarfin maza, yayin da Masar take biye mata.
Al-Riyadh, jaridar kasar Saudiyya, ta wallafa rahoton da ya yi ƙiyasin cewa 'yan ƙasar suna kashe dala biliyan 1.5 a duk shekara domin sayen maganin ƙarfin maza.
Maganin ƙarfin maza da 'yan ƙasar ke sha ya ninka na waɗanda 'yan ƙasar Rasha ke sha sau goma, kuma yawan mutanen Rasha ya ninka na Saudiyya sau biyar.
A baya-bayan nan, sakamakon wani bincike daga 'the Arab Journal of Urology' ya nuna cewa kashi 40 cikin 100 na matasan Saudiyya suna amfani da magungunan ƙarfin maza a wani mataki na rayuwarsu.
Kamar yadda ƙididdiga ta nuna a 2021, a duk shekara ana sayar da maganin ƙarfin maza a ƙasar na dala miliyan 127 wanda ya yi daidai da kashi 2.8 na abin da shagunan sayar da magani na Masar suke sayarwa.
Ƙarfin mazakuta
Babu makawa wasu mazan suna da buƙata mai ƙarfi.
A 2014, an soma ganin wani maganin ƙara ƙarfin mazakuta da ake kira Al-Fankoush a shagunan Masar inda yake kama da cakuleti. Ana sayar da Al-Fankoush a kan dala 0.05.
Jim kaɗan bayan da aka kawo shi kasuwa, sai aka dakatar da rarraba Al-Fankoush, haka kuma aka kama wanda ke haɗa maganin bayan wasu kafafen watsa labarai na ƙasar sun bayar da rahoton cewa ana sayar wa yara.
An fi sanin dattawa da amfani da maganin ƙara ƙarfin maza. A Yemen, bayanan da aka samu daga ma'aikatar lafiya ta ƙasar sun nuna cewa mazan da ke tsakanin shekara 20 zuwa 45 ne suka fi amfani da su.
Rahotanni daga ƙasar sun nuna cewa amfani da Viagra da Cialis a matsayin magungunan da ake amfani da su a wurin dabdala sun zama wasu abubuwan da aka saba da su a tsakanin matasan maza tun bayan soma yaƙin basasa tsakanin ƴan tawayen Houthi da kuma dakarun haɗin gwiwa da Saudiyya ke jagoranta.
Mohamed Sfazi, wanda Farfesa ne a ɓangaren haihuwa a Tunisia, ya bayyana wa BBC a yayin wata tattaunawa cewa irin waɗannan magunguna ba wai suna tayar da sha'awa ba ne, kuma an yi su ne domin magance matsalolin da waɗanda suka manyanta suke fama da su.
Haka kuma wani masani a ɓangaren saduwa a Gabas Ta Tsakiya ya bayyana cewa a halin yanzu matasan Larabawa suna komawa amfani da magungunan ƙara ƙarfin maza.
"Dalilin shi ne watakila wata babbar matsala da Larabawan ke fuskanta," kamar yadda Shereen El Feki, wata ƴar jaridar Masar da Birtaniya kuma marubuciyar littafin 'Sex and the Citadel: Intimate Life in a Changing Arab World', ta bayyana.
A yayin da take mayar da martani kan wani babban bincike kan daidaiton jinsi da aka gudanar a Gabas Ta Tsakiya wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar da goyon baya, Ms El Feki ta bayyana cewa "Kusan duka mazan da muka tunkara sun bayyana fargaba kan abin da zai faru a gaba da kuma yadda za su samar wa iyalansu abinci.
Maza da dama sun koka kan yadda ake buƙatar maza su zama maza inda wasu matan suke cewa "yadda wasu mazan ba maza ba ne a yanzu".