Amurka ta nemi Ukraine ta tattauna da Rasha don tsayar da yaki

Asalin hoton, Getty Images
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada matsayin gwamnatin kasarta na cewa ya rage ga Ukraine ta yanke shawara kan ko za ta shiga tattaunawa da Rasha.
A lokacin da ta kai ziyara babban birnin Ukraine din Kyiv, Linda Thomas-Greenfield ta ce wuka da nama na hannun Ukraine.
Ta ce, ''ina ganin shugaban kasar Ukraine din ya fadi matsayinsa lokacin da ya ce a shirye yake ya samu diflomasiyya da Rashawan, amma kuma dole su mutunta iyakar Ukraine, dole su bi dokokin Majalisar Dinkin Duniya, kuma dole n esu fitar da sojojinsu daga kasar nan.’’
‘’Kuma kasashen duniya na tare da Ukraine. Dole ne Ukraine ta kasance a kan gaba, amma dai lalle muna goyon bayan yunkurinsu,‘’ in ji jakadiyar
Jakadiyar tana magana ne kan wasu rahotanni da aka gani kwanan nan, cewa jami'an Amurka na karfafa wa gwamnatin Ukraine guiwa kan ta nuna a shirye take ta zauna tattaunawa da Moscow.
Ta kuma jaddada cewa Ukraine ba za ta taba zama nasara ga Rash aba, kuma ta ce wajibi ne Moscow ta fuskanci shari’a.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gwmnatin Ukraine ta kafe cewa za ta yi magana ne da wanda zai maye gurbin Shugaba Putin kawai, kuma har sai sojan Rasha na karshe ya fice daga Ukraine.
Ms Thomas-Greenfield ta kuma sanar da tallafin dala miliyan 25 ga iyalan da yakin ya fi yi wa ta’annati yayin da ake shirin shiga lokacin hunturu.
Ita dai gwamnatin Amurkar ba ta musanta rahotannin da ke cewa ta tattauna da jami'an gwamnatin Rasha ba domin hana barkewar rikicin nukiliya a Ukraine.
Haka kuma ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta tabbatar cewa nan gaba kadan za ta koma tattaunawa da Moscow kan rage makaman nukiliya.
Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya tabbatar da cewa har yanzu kofa a bude take ta tattaunawa tsakaninsu da Rasha.
Ya kuwa bayyana hakan ne yayin da Fadar Gwamnatin Amurka ta ki musanta rahoton cewa Mista Sullivan na jagorantar tattaunawa da Rasha domin hana amfani da makaman kare-dangi a yakin na Ukraine.
Da yake magana a New York, Mista Sullivan ya ce muradun Amurka ne ta ci gaba da tattaunawa da Kremlin.
Amma kuma ya ce idon jami’ansu a bude yake kan wanda za su tattauna da shi.
Mujallar Wall Street Journal ta ruwaito cewa Mista Sullivan ya yi ganawa ta sirri da takwaransa na Rasha da Sakataren kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya
Nikolai Patrushev da kuma babban mai bai wa gwamnatin Rasha shawara kan harkokin waje Yuri Ushakov, a watannin da suka gabata.
Manyan jami’ai sun gaya wa mujallar cewa mutanen sun tattauna yadda za a kare yakin ya fada matakin amfani da makaman nukiliya, amma kuma bas u yi magana kan kawo karshen yakin na Ukraine ba.
Mai magana da yawun majalisar tsaro na Amurka Adrienne Watson ta ki tabbatar da maganar inda ta gaya wa mujallar cewa mutane kan yi ikirarin abubuwa da dama.
Yayin da shi kuwa kakakin gwamnatin Rasha Dmitry Peskov ya zargi jaridun kasashen yamma da da wallafa tarin labaran karya.
Sai dai kuma sakatariyar hulda da ‘yan jaridu ta Fadar Gwamnatin Amurka a ranar Litinin ta ce Amurka na da ‘yancin da za ta tattauna da Rasha.
A makon da ya gabata jaridar Washington ta ruwaito cewa manyan jami’an Amurka na kira ga Ukraine ta nuna cewa a shirye take ta tattauna da Rasha, kuma ta yi watsi da abin da take nunawa a fili cewa ba za ta tattauna kawo karshen yakin ba yayin da Shugaba Putin ke kan mulki.











