Abin da Amurka za ta koya daga kasar da ta fi matasan 'yan majalisa a duniya

Maren Grøthe na murmushi

Asalin hoton, Maren Grøthe

Bayanan hoto, Maren Grøthe ta ci zaben majalisar dokokin Norway tana shekara 20

Jagororin Amurka tsofaffi ne kuma a kullum kara tsufa suke yi. A wani sabon mataki na kokarin duba wasu kasashe na waje domin gano hanyoyin da za a iya gyara matsalolin da ke tattare da tsarin siyasar Amurka, mun duba kasar Norway wadda ita ce kasar da ta fi matasan ‘yan majalisar dokoki a duniya.

Shugaba Joe Biden na jam’iyyar Democrat mai shekara 79, shi ne mafi tsufa a tarihin Amurka da ya hau wannan kujera. Sannan Babban Abokin hamayyarsa Donald Trump shi kuma yana da shekara 76.

Idan muka duba majalisar dokokin Amurkar kuwa ba a taba samun masu matsakaitan shekaru da suka yi yawa kamar na yanzu ba a cikin shekara ashirin.

Wadanda aka haifa bayan yakin duniya na biyu su suka fi yawa yayin da masu shekara tsakanin 26 zuwa 41 kusan kashi shida ne kawai cikin dari a ciki.

Zaben rabin wa’adi da za a yi a wannan watan na Nuwamba da ke tafe zai sauya fasalin majalisun dokokin Amurkar, to amma duk da haka tsoffin mambobin za su ci gaba da kasance a ciki. Masana sun ce matsalar da ta janyo hakan ita ce ta tsari.

Ana bayar da fifiko wajen rabon mukami a majalisar dokokin ta Amurka, ga wadanda suka fi dadewa. A duk lokacin da za a nada wani shugaba na kwamiti ko wani jagoranci ko bayar da wani aiki mai tsoka, ana duba wanda ya fi dadewa ne a majalisar.

Suna da matsayi da fice ma na bai wa wanda yake kan kujera samun sauki wajen sake cin zabe.

Wani abu kuma da yake kara dagula al.’amura shi ne, yawan shekarun da aka gindaya.

Dole ne shekarunka su kasance sun kai 25 kafin ka tsaya takarar kujerar majalisar wakilai a Amurka, yayin da majalisar dattawa kuwa sai mutum ya kai akalla shekara 30 kafin ya yi takara.

Baya ga wannan tarnaki matasan da suke da burin neman wadannan mukamai suna fuskantar matsala ta rashin wadatattun kudade.

Domin ba su da isasshiyar dukiya da za su nemi matsayi kasancewar watakila suna fama da tsadar rayuwa ta kula da yara ko kuma bashin da aka ba su na karatu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu na ganin rashin samun wakilci na matasa yana gagarumin tasiri a dumukuradiyyar Amurka.

Kamar yadda Amanda Litman, wata mai fafutukar ganin matasa ‘yan kasa da shekara 40 masu ra’ayin kawo sauyi na Takara ta ce.

Ta ce rashin ci-gaban da ake samu a kan bautuwan da suka shafi matasa kamar matsalar yawan ta’annati da bindiga da sauyin yanayi, sun sa shakku da nuna rashin sha’awa ko ma ja da baya daga harkokin siyasa ga matasa.

Norway it ace kasar da a duk duniya ta fi matasan ‘yan siyasa, kamar yadda bayanai suka nuna ( data published by the Inter-Parliamentary Union (IPU).

Kashi 13.6 na yawan ‘yan siyasar kasar ta Turai ‘yan kasa da shekara talatin ne

A Amurka kuwa ko kashi daya wannan rukunin bai samu ba, domin alkaluman sun nuna kashi 0.23 cikin dari na ‘yan kasa da shekara 30 din a majalisar wakilai.

Ba a ma maganar majalisar dattawa wadda ita ko babu ma, domin kamar yadda muka ce a baya kafin mutum ya yi takararta ma sai ya kasance yana da akalla shekara 30.

Haka abin yake ma a masu tsaka-tsakin shekaru, inda majalisar dattawan Birtaniya ce da kuma ta dattawa ta Canada su ne suka fi ‘yan majalisar dattawan Amurka tsufa.

Tsaka-tsakin shekarun ‘yan majalisar Norway shekara 18 ne idan aka kwatanta.

Maren Grøthe ta zama mafi karancin shekaru a siyasar kasa ta Norway bayan da aka zabe ta a majalisar dokokin kasar tana da sheklara 20 a bara.

An haife ta ‘yan watanni kafin harin da aka kai Amurka na 11 ga watan Satumba a 2001.

Ta kasance daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin kasar su 23 da suke kasa da shekara 30.

A hirarta da BBC ta ce, ‘’Ina jin dadin aikin sosai. Aiki ne da yake tattare da dawainiya, kuma ina jin wannan dawainiya kullum.’’

Tsaka-tsakin shekaru a majalisar dokokin ta kasar Norway 46, kuma haka yake tun karshen shekarun 1990.

Saboda yayin da ake samun karuwar matasan da suke shiga majalisar, suna kuma kara dadewa suna aiki. Wanda ya fi yawan shekaru a majalisar shi ne mai shekara 77.

Daya daga cikin masu binciken da suka tattara bayanan wannan rahoto na ‘yan majalisun dokokin kasashen na duniya , (IPU) Jonny Lang, yana da muhimmanci sosai a ce majalisu sun kasance kamar kasar da suke wakilta.

Kuma samun ra’ayi da fahimtar matasa a majalisa kan sa a samu tsare-tsare da manunfofi masu kyau.

Duk da karancin shekarunta, daman Grøthe ta yi shekara biyu a matasayin wakiliya a majalisar karamar hukumarta, kafin a zabe ta zuwa majalisar dokokin kasar gaba daya.

Tana gudanar da ayyuka da dama a matsayin da take a yanzu.

A kwanan nan ta yi tafiya da kwamitin majalisar dokokin zuwa Jamus, inda bayan nan ta koma kasarta inda ta je ta bude wani sabon filin wasan kwallon kafa a tsakiyar kasar ta Norway inda take da zama da saurayinta.

Alexandria Ocasio-Cortez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alexandria Ocasio-Cortez ta kasance mace mafi karancin shekaru da aka zaba a a majalisar dokokin Amurka a 2018

Ta bayyana kanta a matsayin ‘yar kasar Norway kamar kowa, wadda take rayuwa ta yau da kullum, kamar zuwa wajen liyafa da kawaye da abokai sannan kuma tana zuwa wasan hawa tsauni.

To amma tun bayan da aka zabe ta zuwa majalisar dokokin kasar tata ta Norway wadda ake kira ‘’Storting’’ kusan ba ta da lokaci saosai na irin wannan rayuwa da a da ta saba yi.

Grøthe ta yi amanna cewa zabar matasan ‘yan siyasa da yawa a wannan majalisa abu ne mai alfanu sosai, saboda ana samun wakilci na al’adu daban-daban da kuma rukunin al’umma daban-daban.

Ta ce,’’um matasa mun san irin rayuwar da muke fama da ita, sabanin yadda aka sani a baya.

Muna bukatar mu samar da tsare-tsare da manufofi da za su amfani kowa a kasar.’’

Ta ce, ‘’Wani zai iya cewa, to amma wace gudumamawa za ta bayar a siyasa wadda mai shekara 55 ba zai iya bayarwa ba yau?’’

Sai ta yi bayani da cewa , "Ina da fahimta da ilimi daban na fahimtar matashi a yau.

Kullum ana ta samun matasa da ke fama da cuta ko matsala ta damuwa.

Kuma a kwanan nan na kammala karatuna na jami’a, wanda hakan ba karamin abin mafani ba ne ga kwamitin kula da ilimi na majalisar’’ in ji ta.

Masaniyar kimiyyyar siyasa a jami’ar Bergen, Farfesa Ragnhild Louise Muriaas na ganin tsarin zaben kasar ta Norway shi ne dalilin da ya sa kasar ta kasance mai ‘yan majalisar dokoki da ke da karancin shekaru a duniya.

Za a iya zabar mutane da yawa daga jam’iyya daya a lardi daya.

Ta ce, "Wannan na nufin mutumin da ya fi yawan shekaru wanda kuma aka fi sani ka iya zama dan takarar da ya fi girma, amma kuma a zabi matar da take matashiya wadda ma ba a santa ba sosai a cikin jerin’yan takarar, kuma tabbatar na zabe ta ta ci.’’

A Faransa da Birtaniya da kuma Amurka, ana bin tsarin wanda ya yin asara shi ke tafiya da komai – wuka da nama, saboda haka ne jam’iyyu suke ganin ba za su bari ‘yan takara matasa da ba su da kwarewa ba su fi yawa.

Wato suna gudun kada wata jam'iyya ta hamayya ta yi musu sakiyar da ba ruwa.

Matsan 'yan siyasa a Norway

Asalin hoton, HANDOUT

Bayanan hoto, Shekarunsu kasa da 30, amma duk sun ci zabe a Norway

Masaniyar ta kara da cewa reshen matasa na jam'iyyu ma na taka muhimmiyar rawa.

Ta ce wannan bangare na matasa yana da tasiri sosai, yawanci za ka ga suna da ra'ayi wanda ya sha babban ma da na uwar jam'iyya.

Akwai kuma wasu matsaloli da za su iya kasancewa in ji Muriaas.

Tana duba yadda ko ana ganin matasan 'yan siyasa na saurin ficewa daga fagen siyasa ne shi ya sa ba a ba su dama a wasu kasashen kamar Amurka.

Sannan rashin aiki da kuma kwarewa ma ana ganin wannan wata matsala ce, ga wanda za a zaba.

Ba a yi la'akari da tsarin da ake amfani da shi na kasar Norway a Amurka ba, amma wasu masu bincike a jami'ar Tufts, na ganin wasu abubuwan da ke tasowa a shekarun nan ka iya sa a samu yawaitar shigar matasa a mukamai na mulkin siyasa.

Masu nazarin na ganin cewa duk da cewa ba lalle ba ne jam'iyyu suna da wata dabara ko tsari na musamman na matasa ba, to amma kungiyoyin matasa musamman na jam'iyyar Republican sun yi fice tare da samun kudade wajen tafiyarwa.

Haka kuma masanan na ganin a yadda ake bullo da sabbin tsare-tsare na harkar zabe, inda ake zabe bisa fifikon mai kada kuri'a, wannan ma zai iya amfanar matasan 'yan siyasa.

To amma saboda masu fada-a-ji, wadanda ke uwa da makarbiya a jam'iyyu yawanci sukan danne matasan 'yan takara, akwai bukatar a karfafa wa matasan guiwa tare da shigar da su siyasar sosai da kuma ba su tallafin kudi su yi takara, in ji Sara Suzuki.

Yanzu dai a zaben da za a yi na 'yan majalisar dokoki na Amurka, wato na rabin wa'adi a watan Nuwamba, a karon farko akwai 'yan takara biyu matasa wadanda aka haifa na rukunin shekarun 1990 zuwa 2000, daga jam'iyyar Republican da kuma Democrat.

Idan har suka yi nasara to za su yi waje da tsofaffin zuma da suka mamaye tare da kasancewa a majalisa shekara da shekaru.