Wadanda za su buga Kofin Duniya na karshe daga Qatar 2022

Asalin hoton, Getty Images
Kasashe 32 za su fafata a karon farko a Gasar Kofin Duniya da za a fara ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.
Gasar Kofin Duniya ita ce kololuwa ga duk wani dan wasan tamaula ke mafarkin bugawa, sai dai wasu na fatan yin ban kwana daga wadda za a yi a Qatar.
'Jerin 'yan wasan da daga Qatar da kyar su sake buga Gasar Kofin duniya:
Shekaraunsu da zarar an fara gasar kofin duniya ranar 20 ga Nuwambar 2022
1. Atiba Hutchinson (Canada) - shekara 39 da wata tara da kwana 12
Atiba Hutchinson shi ne kadai daga tawagar Canada da ya buga mata Gasar 1986.
Shi ne mai yawan shekarun haihuwa da zai buga wasannin Qatar, wanda zai yi wa Canada kyaftin.
Hutchinson wanda ke wasa a Turkiya a Besiktas, shi ne kan gaba a yawan yi wa Canada tamaula mai fafatawa 97.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
2. Pepe (Portugal) - shekara 39 da wata takwas da kwana 25
Pepe na ci gaba da taka rawar gani a kungiyarsa da tawagar Portugal, wanda zai tsare mata baya a Qatar.
Duk da cewar yana da shekara 39, yana da kwarwar da zai taka rawar gani a babbar Gasar tamaula ta Duniya karo na 22 da Fifa za ta gabatar.
Pepe yana cikin 'yan wasan Portugal da suka lashe UEFA Euro 2016 da kuma 2019 UEFA Nations League.
Saboda haka idan ya lashe kofin duniya zai kara masa martaba a idon duniya a fannin tamaula.
3. Eiji Kawashima (Japan) - shekara 39 da wata takwas
Mai tsaron ragar Japan zai cika shekara 40 da haihuwa a watan Maris din 2023, kuma yana cikin gololin tawagar da ta gayyata zuwa Qatar.
Shi ne golan Japan shekara 12 yana kan gurbin, wanda ya taka rawar gani a Gasar Kofin Duniya a Rasha a 2018 - ana sa ran shi ne dai zai tsare ragar tawagar a Qatar.
Tun a gasar Rasha, shi ne kan gaba a yawan wakiltar Japan a Gasar Kofin Duniya, yanzu zai kara dorawa a wasannin Qatar.
4. Dani Alves (Brazil) - shekara 39 da wata shida da kwana 14
Dani Alves zai zama dan kasar Brazil mai yawan shekara da zai wakilce ta a gasar Kofin Duniya da za a gudanar a Qatar.
Wanda yake da tarihin a baya shi ne Djalma Santos, wanda ya buga Gasar da aka yi a 1966 yana da shekara 37.
Alves ya halarci Kofin Duniya uku, sai dai baya cikin tawagar da ta buga 2018, sakamakon jinya da ya yi.
5. Thiago Silva (Brazil) - shekara 38 da wata daya da kwana 29
Mai taka leda a Chelsea mai tsaron baya na fatan sa kwazo a Brazil a wasannin da za ta yi a Qatar.
Duk da cewar mai sa kwazo ne a wasanninsa har yanzu yana taka rawar gani a tsare bayan Brazil tare da Marquinhos da Eder Militao da kuma Gleison Bremer.
6. Cristiano Ronaldo (Portugal) - shekara 37 da wata tara da kwana 15
Kyaftin Cristiano Ronaldo zai ja ragamar tawagar Portugal a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar, zai shiga jerin wadanda suke da tarihin zuwa Gasa biyar a duniya.
'Yan kwallo uku ne suka je gasar Kofin Duniya a tarihi karo biyar da suka hada da Lothaur Matthaus da Antonio Carbajal da kuma Rafael Marquez .
Golan Italiya, Gianluigi Buffon ya je Gasar Kofin Duniya karo biyar amma a hudu a yi wasanni.
Ronaldo zai buga wasannin Qatar a matakin na daya a cin kwallaye a tawaga a duniya mai 117 jumulla.
Watakila daga wannan Gasar Ronaldo ba zai sake taka leda a Portugal ba, wadda ba ta taba lashe kofin ba.











