Matar da za a jefe a Sudan ta rasa mai cetonta

Mace dauke da ruwa a Sudan

Asalin hoton, Getty Images

Duk wani kokari na kare wata mata ‘yar Sudan daga aiwatar mata da hukuncin kisa ta hanyar rajamu wato jefewa bayan samunta da laifin zina na gamuwa da cikas saboda rashin ministoci a gwamnatin kasar.

Sojoji ne ke tafiyar da mulkin kasar ta Sudan tun bayan da suka yi juyin mulki shekara daya da ta gabata.

Masu fafutuka sun ce ba a yi wa matar mai shekara 20 adalci ba a shari’ar saboda haka suke neman da a sake ta.

Wani jami’in gwamnati ya yarda cewa shari’ar kamar wasa ce kawai, amma kuma ya kara bayani da cewa : ‘’Ba mu da minista da zai shiga maganar domin a sake ta.’’

Matashiyar matar wadda suka rabu da mijinta a shekara ta 2020 ta koma gidansu ne inda take zaune da iyayenta, inda mijin nata ya zarge ta da laifin zina bayan shekara daya.

A watan Yuni ne na wannan shekara ta 2022 wata kotu a birnin Kosti na jihar White Nile ta same ta da laifi.

Yanzu dai kotu ta saurari karar da ta daukaka a kan hukuncin kuma ana jiran a ji yadda hukuncin zai kasance.

Sulaima Ishaq, wadda ke shugabantar sashen kula da batutuwan cin zarafin mata a ma’aikatar jin dadi da walwalar jama’a ta kasar ta gaya wa BBC cewa, tana ta gaya wa jami’ai a babban birnin kasar Khartoum cewa an yi kura-kurai a shari’ar.

To amma rashin wani minista na gwamnati ya sa maganarta ba ta samu shiga inda ya kamata a saurare ta ba domin daukar mataki.

Kungiyoyin kare hakkin dan-Adam sun ce matar wadda iyayenta ba su yarda a bayyana sunanta ba, ba a ba ta damar samun lauyan da zai kare ta ba a lokacin da take tsare.

Kuma ba ta san laifin da aka tuhume ta da shi ba ta amsa laifin,’’ in ji Mossaad Mohamed Ali, babban darektan Cibiyar tabbatar da adalci da zaman lafita ta Afirka (ACJPS).

 Lauyar matar, Intisar Abdala, ta gaya wa BBC cewa, tana fatan da daukaka karar da suka yi, kotun za ta yi abin da ya dace, ta saki matar.

Yarinya na rike da kwali mai dauke da rubutun da ke suka kan hukuncin

Asalin hoton, Siha

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga a Khartoum kan hukuncin rajamu
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Har yanzu Sudan tana yanke hukunci kamar yadda Allah Ya ambata a Al Qurani kan laifukan da suka shafi sata da zina.

 A dokokin Sudan hukunce-hukuncen sun hada da bulala da datse hannu da kafa da ratayewa da kuma rajamu, wato jefewa da duwatsu.

 Alkawarin da gwamnati ta yi a 2015 na janye hukuncin rajamu, wato jefewa da dutse bai tabbata ba in ji kungiyoyin kare hakkin dan-Adam.

 "Hatta ‘yan siyasa masu tsananin ra’ayin rikau ma ba sa goyon bayan hukuncin jefewa," in ji Sulaima Ishaq kamar yadda ta sheda wa BBC.

Ta kara bayani da cewa, "To amma abubuwa na daukar dogon lokaci kafin su sauya a nan, kafin daga bisani su kai ga kotuna, to kuma mata ne za su ci gaba da wahala."

 Hala Al-Karib, darektar yanki ta kungiyar kare hakkin mata ta yankin kuryar gabashin Afirka (Strategic Initiative for Women in the Horn of Africa (Siha) ) ta ce ana nuna bambanci wajen amfani da dokokin zina a kan mata a Sudan.

 Mata ta karshe da aka sani wadda aka yanke wa hukuncin rajamu a kan laifin zina, wata matashiya ce mai suna Intisar El Sherif Abdalla.

 A 2012 aka sake ta tare da ‘yarta mai wata hudu sakamakon fafutuka da kiraye-kirayen kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Amnesty International da kuma kungiyar ta Siha.

 To amma kuma Al-Karib ta ce za a iya samun wasu matan da aka yanke musu irin wannan hukunci kuma maganarsu ta wuce ba tare da an sani ba.

 Ta kara da cewa kungiyoyin kare hakkin mata da dan-Adam a Sudan ba su da kudi da kayan aiki sosai saboda haka zai iya kasancewa akwai mata da yawa da suka shiga irin wannan hali ba a ma sani ba.

Hayaki ya turneke a lokacin zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanga-zanga ta barke bayan juyin mulki a watan Oktoba na 2021

A karkashin gwamnatin rikon-kwarya da ta biyo bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a 2019, an yi wa dokar yadda mata za su sanya tufafi da mu’amulla a waje gyara.

Sai dai kuma ‘yar jarida Zeinab Mohammed Salih, ‘yar kasar ta Sudan ta ce ‘yan Hisbah da ke bi titi-titi suna tabbatar mat ana bin dokar sun sake dawowa bakin aiki bayan juyin mulkin da aka yi shekara daya da ta wuce.

 Akwai ma rahotannin da ke cewa sojojin da suka kwace mulki sun sake dauko hayar masu biyayya da hambararren shugaban kasar al Bashir.

 Hala Al-Kirab ta ce, ‘’Muna da fatan cewa gwamnatin rikon-kwarya za ta yi sauye-sauye a dokokin Sudan, wadanda suke ci gaba da dora laifi a kan mata da ‘yan mata, wanda hakan ke sa ana nuna musu wariya da bambanci, amma kuma mu ba mu san hakan ba.’’

A 2021, Sudan ma ta zama daga cikin kasashen da suka rattaba hannu a kan dokar Majalisar Dinkin Duniya da ta haramta azabtarwa.

 Mossaad Mohamed Ali ta kungiyar kare hakkin mata (ACJPS). Ta ce, ‘’ rajamu wadda ita ce mafi tsananin azabtarwa na karkashin wannan doka."

 Kungiyoyin kare hakkin mat ana duniya da na cikin kasar na kira da a saki matar, tare da suka ga wannan hukunci na rajamu.

 Lauya Intisar Abdala ce kadai aka bai wa dama ta ziyarci matar mai shekara 20, wadda ke tsare tsawon watanni a kurkuku na mata a jihar White Nile.

Ta ce, ‘’Ba wani abu da ya samu matashiyar matar, to amma kai ka san cewa tana cikin damuwa sosai.’’

 Ta kara da cewa, ‘’ Matashiyar ‘yar talakawa ce da ta fito daga gid ana masu al’ada da addini kuma manoma, kuma duk da haka iyayenta bas u yi watsi da it aba.

 ‘’Muna jiran daukaka karar da muka yi a kotu, to amma ba wanda zai iya fadan lokacin da za a yi hukuncin. Jira kadai za mu iya yi yanzu,’’ in ji ta.

 Wadanda suke fafutukar ganin na saki matar sun ce za su so ganin kungiyoyi da kasashen duniya sun matsa lamba don a sake ta.

 Hala Al-Karib, ta ce "Muna fargabar cewa kotun daukaka karar ba za ta yi hukuncin da zai yi wa matashiyar dadi ba.

Muna samun cetar mata ne daga irin wadannan dokoki idan kasashen duniya suka shigo cikin maganar tare da matsa lamba a kan gwamnatin Sudan don haka dole ne a samu irin wannan hadin kan ma a wannan karon.

 Mai fafutukar ta kara da cewa,’’ Wannan hukunci zai iya bai wa duniya mamaki, to amma mu bai zo mana da mamaki ba.’’

 BBC ta nemi jin karin bayani daga ainahin kotun ta Kosti da ta yi hukuncin amma ba ta samu wani bayani ba

 Haka kuma ba ta yadda za a ji ta bakin ministan shari’a domin ba wanda aka nada a kan mukamin.

 Kakakin ofishin jakadancin Sudan a London, ya gaya wa BBC cewa, ‘’ Muna sane da wannan shari’a, kuma mu dai a wurinmu mun san cewa hukuncin kotun ba shi ne na karshe ba.

Mun tuntubi jami’an ma’aikatar shari’a a Sudan a kan lamarin, kuma muna jiran amsarsu.’’