Real Madrid ta yi bikin lashe La Liga na bana na 36 jimilla

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid da magoya baya sun yi bikin lashe La Liga na bana na 36 jimilla a katafaren filin da ake kira Plaza de Cibeles.
Ƴan wasan sun taru a hedikwatar Comunidad de Madrid daga nan suka nufi katafaren filin da ake kira Madrid fountain, wurin da dubban magoya baya suka taru.
A nan ne aka yi wa ƴan wasa tarbar girma da isarsu wurin a wata farar mota katuwa da aka tanada don yin bikin lashe La Liga na bana na 36 jimilla.
Da isarsu wurin aka fara kida nan da nan fili ya dauki sowa da kuwa, inda magoya baya suma suka barke da tafi a lokacin da Real ta yi wasa 29 a jere ba a doke ta ba.
Filin da aka yi bikin an kawata shi abin gwanin ban sha'awa, an kuma daura kyallaye da yawa har da wanda yake dauke da sakon "Campeones 36" da kuma "Gracias madridistas".
Daga nan ƴan wasa suka sauko daka bas din da suke ciki, inda suka je kan dandamalin da aka tanada, domin taya juna murna.
Bayan nan aka shiga jawabai, inda ƴan wasa suka godewa magoya baya kan yadda suke bibiyar kungiyar sauda kafa.
Real Madrid za ta buga wasan karshe da Borussia Dortmund a Champions League ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.











