Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa mata da Musulmai ba sa samun albashi mai yawa a India
Mata na fuskantar nuna bambanci a wurin neman aiki, ana kuma biyan su albashin da bai taka kara ya karya ba, ko da suna da takardu da kuma ƙwarewa irin ta maza.
Rahoton Oxfam kan nuna wariya a Indiya na 2022 ya zargi '' tsanar da al'umma da kamfanonin da ke ba da aiki ke nuna musu ''ta hanyar ba su albashi dan kadan."
Baya ga mata, wani rukunin jama'a da ke fuskantar irin wannan matsala su ne Musulman kasar, da kuma tsiraru.
''Nuna bambanci wurin neman aiki shi ne lokacin da aka nuna tsana ko wariya ga wasu rukunin mutane, saboda yanayin halittarsu ko kuma inda suka fito,'' in ji Amitabh Behar shugaban Oxfam a Indiya.
Masu bincike a Oxfam sun duba yadda ake bayar da aikin gwamnati, da albashi, da lafiya da bashin noma daga 2004 zuwa 2020.
Sun kuma gano cewa a duk wata ma'aikaci namiji na samun matsakaicin albashi da ya kai rupee 4,000, da ya yi daidai da dala 50 akan mata.
Haka ma wadanda ba Musulmai ba suna karbar matsakaicin albashi da ya kai rupee 7,000, akan Musulmai da sauran tsiraru da ke karbar abinda bai wuce rupee 5,000 ba.
Indiya ta yi kaurin suna wurin muzguna wa mata, inda ake samun dubbai na zubar da cikin ‘ya’ya mata, kuma matan da dama na fara fuskantar wariya da kuntatawa tun daga haihuwa har karshen rayuwarsu.
Kamar yadda alkaluman gwamnati suka nuna, kaso 25.1 ne na ma’ikata mata, wanda ya gaza kai wa na Brazil da Rasha da China da kuma Afrika ta Kudu.
Oxfam ta ce hakan abun damuwa ne, la’akari da ci gaban tattalin arzikin da Indiya ta samu a shekarun da suka gabata.
A 'yan shekarun nan annobar korona ta ta’azzara lamarin, da kuma kullen da aka shiga, wanda ya sa ayyuka suka yi karanci, aka rika korar mata daga aiki.
Rahoton ya kuma ce mata da dama ba sa aiki saboda tarin lalurori da suka yi musu yawa gida, duk da ilimi da ƙwarewar da suke da ita.
Rahoton na Oxfam ya bayyana cewa "a farko-farkon watannin annobar Covid-19, an samu karuwar rashin aikin yi da kashi 17 a tsakanin Musulmai."
Ya kara da cewa "nuna bambanci a Indiya ya wuce tsakanin al’umma, ya kai har bangaren tattalin arziki, in ji Mr Behan, inda ya kara da cewa "gwamnati, da jam’iyyun siyasa, da masu yin dokoki, da ma kungiyoyin fararen hula dole su tashi tsaye, wurin gina sabuwar Indiya da ba bu nuna bambanci a cikinta."