Rasha ta ci gaba da kai hari duk da tsagaita wuta - Zelensky

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya zargi Rasha da ci gaba da kai wa kasar sa hari duk da sanarwar dakatar da bude wuta da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi albarkacin lokacin Easter.

A wani sako da ya fitar 'yan sa'o'I kadan kafin dakatar da bude wutar, shugaban na Ukraine y ace Mista Putin ba wanda za a aminta da shi ba ne.

Mista Zelensky ya nuna cewa duk wata dakatar da bude wuta da za a yi, da za ta amsa sunanta kamata ya yi ta kai tsawon kwana 30, maimakon sa'a 30, da Shugaba Putin ya ayyana.

Shi dai Putin ya ce ya yi hakan ne bisa dalilai na jin-kai.

Yayin sanar da dakatar da bude wutar Shugaban na Rasha y ace ya umari dakarunsa su dakatar da duk wasu ayyuka na soji a Ukraine, a matsayin Dakatar da bude wuta domin lokacin Easter, har zuwa ranar Lahadi (yau Lahadi).

Ya ce dakatarwar ta tsawon sa'a 30 za ta kare ne da misalin karfe goma na dare ranar Lahadi (00:00 agogon Moscow ) said ai y ace sojin Rasha za su kasance cikin shiri ga duk wani abu da Ukraine za ta yin a saba wannan karamci.

Shugaban Zelensky ya ce Kyiv za ta mutunta wannan dakatarwar, amma kuma ya zargi Moscow tda sabawar.

Mista Zelensky, ya ce, har yanzu su abin da suke fata shi ne amsa daga Rasha kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta tsawon kwana 30.

Ya ce fada ya ci gaba a yankuna Kursk da Belgorod na Rasha, kuma ana ci gaba da amfanin da kananan jiragen yaki marassa matuka na Rasha, amma kuma ya ce e lalle wasu wuararen sun yi shiru.

Zelensky ya ce a shirye Ukraine take ta tsawaita yarjejeniyar har zuwa bayan 20 ga watan nan nan Afirilu – wanda hakan yana nufin shawarar da Amurka ta bayar tun da farko ta dakatar da bude wuta tsawon kwana 30, wadda tun da a lokacin Ukraine ta yarda da ita.

Shi ma ministan harkokin wajen Ukraine Andriy Sybiha, da yake mayar da martani kan sanarwar dakatar da bude wuta da Putin ya yi, a shafinsa na X , ya nuna takaicinsa kan dakatarwar ta sa'a 30 maimakon kwana 30.

Ya ce abin takaicin shi ne daman sun saba da dabi'arsa ta fadin kalamai sabanin abin da yake yi.

Ya kara da cewa sun san da cewa kalamansi baa bin da za a amince da su ba ne , a don haka za su duba ayyukansa ne amma ba kalamansa ba.

Rasha dai ta ce dakarunta za su mutunta dakatar da bude wutar mtaukar Ukraine ba ta saba ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka sanar da tsagaita yakin ba – wani yunkuri da aka yi na dakatarwar a lokacin bikin Kirsimeti na Kiristoci 'yan gargajiya a watan Janairu na 2023, yarjejeniyar ta wargaje bayan da dukkanin bangarorin biyu suka kasa amincewa da yarjejeniyar.

Dangane da sanarwar shugaban na Rasha kan dakatar da bude wuta, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya – ya ce yanzu ne lokacin da Putin zai nuna da gaske yake a kan zaman lafiya – ta hanyar dakatar da mummunan kutse da yake yi wa Ukraine – kamare yadda Ukraine din ta nema ba wai kawai tsawon kawan daya ba saboda Easter.

A ranar 24 ga watan Fabarairu na 2022 ne Rasha ta kaddamar da kutsenta a kan Ukraine.

An yi kiyasin dubban mutane yawancinsu sojoji – ko dai sun mutu ko kuma sun ji rauni a yakin daga dukkanin bangarorin.

Amurka na tattaunawa kai tsaye da Rasha don ganin ta kawo karshen yakin, amma kuma tana fama wajen yin wata nasara kan hakan.

A watan da ya gabata rasha ta yi watsi da shawarar dakatar da bude wuta ba tare da wani sharadi ba – wadda Amurka da Ukraine suka amince da ita.

A ranar Juma'a ne kuma Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi gargadin cewa gwamnatinsa za ta fice daga batun neman sasanta yakin in dai ba a samu wani cigaba cikin gaggawa ba kan batun.