Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rasha na son a haramta wa Ukraine shiga Nato
Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha ya ce za su nemi tabbacin cewa kungiyar tsaro ta Nato ta tsame Ukraine daga duk wani shirin shiga kungiyar kuma ya kasance a bisa kowane hali Ukraine ta zamo kasa ƴar ba ruwanmu a duk wata tattaunawar zaman lafiya.
Wannan na zuwa a yayin Donald Trump da Vladimir Putin ake sa ran za su tattauna a wannan mako, a tattaunawar da ake ci gaba da yi kan yiyuwar tsagaita wuta a yakin Ukraine da aka shafe shekaru uku ana yi.
Mataimakin ministan harakokin wajen na Rasha Alexander Grushko ya ce za su buƙaci tabbaci na tsaro ya kasance wani ɓangare na yarjejeniyar.
Kuma daga cikin buƙatun na Rasha, shi ne ƙasashen Nato su ƙi amincewa da Ukraine a matsayin mamba.
Amurka da Ukraine dai sun amince su samar da daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta ta wata ɗaya ga Rasha.
Kuma a wannan makon ake sa ran Donald Trump zai tattauna da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yiyuwar tsagaita wuta a yakin shekara uku na Ukraine.
Ɗaya daga cikin yankunan da ake taƙaddama a kai shi ne yankin Kursk na yammacin Rasha, inda Ukraine ta kaddamar da farmakin soji a watan Agusta tare da ƙwace wasu yankuna.
Sai dai Putin ya yi ikirarin cewa Rasha ce ke da iko da Kursk tare da cewa an fatattaki dakarun Ukraine.
Sannan Putin ya nuna shakku kan yadda za a sa ido domin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da ake son cimma a yankin gabashi da ake yaƙi.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya soki Putin da ƙoƙarin yin zagon ƙasa a ƙoƙarin bin hanyoyin diflomasiyar da ake yi na gaggauta tsagaita wuta.
Ƙasa da wata guda da rantsar da shi, Trump ya tattauna da Putin da aka ruwaito ta tsawon minti 90 kan yadda za a gaggauta tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin.
Ɓangaren da dai ake nuna shakku da alamar tambaya shi ne, a yarjejeniyar yadda za a warware batun makomar yakunan da Rasha ta mamaye na Ukraine