Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Putin ya gindaya sharuɗɗan tsagaita wuta a Ukraine
Vladmir Putin ya ce ya amince da batun tsagaita wuta a Ukraine sai dai abin tambayar har yanzu shi ne yanayin yarjejeniyar - yayin da ya kafa wasu sharuɗɗa masu tsauri na cimma zaman lafiya.
Shugaban Rasha yana mayar da martani ne kan ƙudirin tsagaita wuta na wata guda, wanda Ukraine ta amince da shi a farkon wannan makon bayan tattauwa da Amurka.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana martanin Putin game da ƙudirin a matsayin "nuna iko" inda kuma ya yi kira da a ƙara ƙaƙaba wa Rasha takunkumi.
A hannu guda, Amurka ta kara lafta takunkumai kan man fetur ɗin Rasha da iskar gas da kuma bankunan ƙasar.
Jami'an Rasha sun ce an tsara Putin zai tattauna da Steve Witkoff, wakili na musamman ga Shugaban Amurka Donald Trump game da tsagaita wutar.
Babu tabbaci kan ko an yi ganawar. A ranar Juma'a, kafar yaɗa labaran gwamnatin Rasha ta ruwaito cewa jirgin da ake tunanin Witkoff ke ciki ya bar Moscow.
Moscow da Rasha dai ba su ce komai ba game da batun.
A yammacin ranar Alhamis da kuma cikin dare, Rasha da Ukraine suka bayar da rahoton kai sabbin hare-haren jirgi mara matuƙi.
Ukraine ta ce mutum bakwai - har da yara - sun jikkata a Kharkiv da ke arewa maso gabashin Ukraine.
Rasha, a nata ɓangaren ta ruwaito tashin mummunar gobara a wata cibiyar mai da ke Tuapse a kudancin kasar.
A wani taron manema labarai a birnin Moscow da aka yi ranar Alhamis, Putin ya yi tsokaci game da shawarar tsagaita wutar inda ya ce shawara ce mai kyau kuma muna goyon bayan ta amma akwai batutuwan da suka buƙatar a tattauna.
Ya kamata tsagaita wuta ya samar da zaman lafiya mai ɗorewa tare da magance musabbabin rikicin, in ji Putin.
"Akwai bukatar mu tattauna da takwarorinmu na Amurka da ƙawayenmu," in ji shi. "Wataƙila na kira Donald Trump ta wata."
Putin ya ƙara da cewa: "Zai yi kyau ga Ukraine ta tsagaita wuta na tsawon kwana 30.
"Muna goyon bayan ta, amma akwai ɓangarorin taƙaddama."
Ɗaya daga cikin yankunan da ake taƙaddama a kai shi ne Kursk, in ji Putin, inda Ukraine ta ƙaddamar da hari a Agustan bata tare da karɓe iko da wasu yankuna.
Ya yi iƙirarin cewa Rasha ta ƙwace iko da Kursk sannan sojojin Ukraine da ke wurin tuni aka murƙushe su.
"Suna ƙoƙarin ficewa amma mu ne ke da iko. Sun watsar da makamansu." in ji Putin.
"Akwai zaɓi biyu ga ƴan Ukraine da ke Kursk - su miƙa wuya ko su mutu."
Babban Kwamandan Ukraine, Oleksandr Syrskyi ya ce kwana guda gabanin haka, dakarun Ukraine za su kasance a wasu yankunan Kursk "idan dai hakan ta zama dole" duk da ƙarin matsin lamba daga sojojin Rasha.
A taron manema labaran na ranar Alhamis, Putin ya kuma zayyana wasu daga cikin tambayoyinsa kan yadda yarjejeniyar za ta yi aiki. Ya tambaya: "Ta yaya waɗannan kwanaki 30 za su kasance? Ga Ukraine ta sake shiri? Ta sake ƙaro makamai? Ta horar da mutane? ko babu guda ciki? Sai wata tambaya - ta yaya za a tafiyar da hakan?
"Wane zai bayar da umarnin kawo ƙarshen yaƙin? Wane zai yanke wanda ya saɓa yarjejeniyar, idan aka zarce tsawon kilomita 2,000? Dole duka ɓangarorin su yi nazari sosai. Wane zai sa ido?
Putin "bai ce a a ba kai tsaye", kamar yadda Zelensky ya faɗa a jawabin da yake ta bidiyo, sai dai "a aikace, yana shirin ƙin amincewa da shawarar".
Ya ƙara da cewa: "Putin, na tsoron faɗa wa Shugaba Trump kai tsaye cewa yana son ya ci gaba da yaƙi, yana son kashe ƴan Ukraine."
Shugaban Rasha ya sanya sharuɗɗa da dama "cewa ba za a warware komai ba", in ji Zelensky.
Bayan jawabin Putin da martanin Zelensky, ta bayyana karara cewa akwai ɓaraka tsakanin ɓangarorin biyu.
Ukraine na son aiwatar da tsarin a matakai biyu: tsagaita wuta cikin hanzari sannan a cimma daidaito a yarjejeniya guda. Duka ɓangarorin biyu da alama sun gamsu su tattauna batutuwan da suke da saɓani a kai.
Ukraine na ganin za ta iya matsa lamba kan Rasha, tana bayyana ta a matsayin mai nuna ko oho ga buƙatar zaman lafiya. Rasha ita ma tana ganin a yanzu tana da dama ta bayyana damuwarta, game da faɗaɗa Nato da kuma ƴancin Ukraine.
Sai dai wannan matsala ce ga Donald Trump. Ya bayyana ƙarara cewa yana son sakamako cikin hanzari, a kawo ƙarshen yaƙin a ƴan kwanaki.
Kuma a yanzu, babu alamu Putin zai ba da haɗin kai.
A jawabinsa a Fadar White House bayan tsokacin Putin, Trump ya ce zai "so ya gana da shugaban Rasha kuma yana fatan Rasha za ta yi abin da ya dace ta kuma amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta wata ɗaya.
"Za mu so ganin Rasha ta tsagaita wuta," in ji Rasha.
A jawabin da ya yi tun farko a wani taro a ofishin shugaban ƙasa tare da babban sakataren ƙungiyar Nato Mark Rutte, Trump ya faɗa wa ƴanjarida cewa tuni ya tattauna wasu batutuwa da Ukraine.
"Muna ta tattauna wa da Ukraine da filayen da za a ajiye da waɗanda za a rasa kuma duk wasu batutuwa da suka shafi cimma yarjejeniya ta karshe," in ji Trump.
"Game da batun shigar Ukraine ƙungiyar ƙawance ta Nato, Trump ya ce "kowa ya san amsar hakan".
Sabbin takunkuman da aka ƙaƙaba kan mai da gas ɗin Rasha yayin da gwamnatin Trump ta ƙara taƙaita damar amfani da tsarin biyan kuɗi na Amurka, abin da ya ƙara sa sauran ƙasashe na shan wahaka wajen sayen man Rasha.
Tun farko a ranar, mashawarcin Kremlin Yuri Ushakov ya yi fatali da shawarar tsagaita wutar da Amurka ta gabatar.
A ranar Laraba, Kremlin ta saki wani bidiyo da ta ce ya nuna Putin ya kai ziyara yankin Kursk na Rasha, sanye cikin kakin soja. Daga bisa Rasha ta ce ta sake ƙwace muhimmin garin Sudzha.
A Fabarairun 2022 ne Rasha ta ƙaddamar da gagarumin hari inda ta mamaye Ukraine kuma a yanzu ta karɓe iko da kusan kashi 20 cikin 100 na yankunan Ukraine ɗin.
Fiye da mutum 95,000 da ke yi wa rundunar sojin Rasha aka kashe a yaƙin, a cewar wata ƙididdiga da aka yi nazari a kai wanda kuma BBC ta tabbatar da alkaluman. Ana tunanin yawan mutanen da suka mutu sun zarce adadin.
Rundunar sojin Rasha ba ta fito ta bayyana yawan dakarunta da aka kashe ba tun Satumban 2022 da ta ce sojoji 5,937 aka kashe.
Lokaci na karshe da Ukraine ta bayyana alƙaluman mutanenta da suka mutu a yaƙin shi ne Disamban 2024, lokacin da Zelesnky ya tabbatar da cewa sojoji da jami'an tsaro 43,000 ne suka mutu. Sai dai masu nazari daga ƙasashen yamma na ganin adadin ya zarce haka.