Me yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Gaza da Amurka ta tsara ta ƙunsa?

Lokacin karatu: Minti 5

Shugabannin Turai da na Gabas ta tsakiya sun yi maraba da yarjejeniyar da Amurka ta tsara na tabbatar da zaman lafiya a Gaza.

Shugaba Trump ya ja kunnen Hamas kan kada ta sake ta ƙi amincewa da yarjejeniyar.

Shawarwarin da shugaban Amurka Donald Trump da Firaiminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu suka amince da su sun buƙaci kawo ƙarshen yakin nan take da sakin ƴan Isra'ila 20 da har yanzu ke raye cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.

Sannan a mayar da gawarwakin sauran duka a cikin kwana uku, yayin da Isra'ila za ta saki ɗaruruwan Falasɗinawa da take riƙe da su a gidajen yarinta.

Yarjejeniyar ta kuma ce Hamas ba za ta taka wata rawa wajen tafiyar da mulkin Gaza ba, sai dai ta bar ƙofa a buɗe na yiwuwar kafa ƙasar Falasɗinu, kodayake Netanyahu ya yi fatali da wannan.

Cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta Axiou ranar Lahadi, Shugaba Trump ya ce ''Mutane da dama ne ke taruwa domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya, don haka ya kamata mu tabbatar da ita,''.

Ya ƙara da cewa yana sane da irin ƙoƙarin aiki tare da ƙasashen Larabawa ke yi wajen kawo ƙarshen yaƙin, sannan Hamas ta nuna alamun yin sulhu ta hanyar masu shiga tsakani.

''Ƙasashen Larabawa na son zaman lafiya, Isra'ila ma na so, Bibi (Netanyahu) na son zaman lafiya."

Shugaba Trump ya ce daftarin zaman lafiyar da ya gabatar, ba kawo ƙarshen yaƙin kawai zai yi ba, har ma da samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

"Idan muka cimma wannan nasara, zai zama babban abin tunawa ga Isra'ila da ma yankin Gabas ta Tsakiya, don haka dole a cimma hakan''.

Muhimman ƙudurorin yarjejeniyar

Kafar yaɗa labaran Axios ta ce shirin na Trump ya ƙunshi ƙudurori 21 da suka ƙunshi:

  • Sakin duka ISra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su cikin sa'o'i 48 na dakatar da wutar.
  • Dawwamammen dakatar da wuta da kuma janyewar dakarun Isra'ila daga zirin Gaza sannu a hankali.
  • Sakin fursunonin Falasɗinawa kusan 250 da ke zaman ɗaurin rai da rai a gidajen yarin Isra'ila, da kuma wasu kusan 2,000 da aka tsare bayan harin 7 ga watan Oktoba.
  • Kafa wani kwamitin gudanar da mulkin Gaza, wanda ba zai ƙunshi mambobin Hamas a ciki ba.
  • Kwamitin zai ƙunshi wasu shugabannin ƙasashen duniya da majalisar ƙungiyar ƙasashen Larabawa da wakilan hukumar Falasɗinawa tare da wasu ƙwararru a yankin.
  • Samar da jami'an tsaron hadin gwiwa da za su ƙunshi Falasɗinawa da sojoji daga wasu ƙasashen Larabawa da Musulmai.
  • Saka jari daga ƙasashen Larabawa domin sake gina Gaza.
  • Ƙwace makaman Hamas tare da lalata rumbunan ajiyar manyan makamansu.
  • Yin afuwa da mambobin ƙungiyar da suka tuba.
  • Dakatar da Isra'ila daga mamaye Gaɓar Yamma ko wani sashe na Gaza.
  • Alƙawarin buɗe ƙofar yiwuwar kafa ƙasar Falasɗinu bayan yin garambawul ga hukumar Falasɗinawa.
  • Alƙawarin kada Isra'ila ta sake kai wa Qatar hari a nan gaba.

Tuni dai aka miƙa wa Hamas daftarin yarjejeniya, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta tabbara.

Cikin wata sanarwa da kakain ma'aikatar ya fitar, Majed al-Ansari ya ce ''wakilan ƙungiyar sun alƙawarta yin nazari na tsanaki kan daftarin kafin sanar da matakin da za ta ɗauka a kai.

Majed al-Ansari ya ce Qatar ta shiya wata tattaunawa da masu shiga tsakani na kungiyar Hamas da jami'an Turkiyya a yau domin tattauna batun.

A baya dai ƙungiyar ta sha nanata cewa za ta martaba duk wata yarjejeniya da za ta ƙunshi kare al'ummar Falasɗinu.

'Abin da muke so shi ne dakatar da yaƙin'

Kwana guda bayan sanar da daftarin kawo ƙarshen yaƙin, al'ummar Gaza na ci gaba da bayyana fatansu game da yarjejeniyar.

Esraa mai shekara 23 ta ce ko bacci ba ta iya yi ba saboda samun labarin daftarin dakatar da yaƙin.

"A ɗauka an ƙulla yarjejeniyar dakatar da yaƙin ne, ashe gadftarin ne kawai'', kamar yadda ta bayyana ta wayar.

Esraa ta ce ta yi imanin cewa an tsara daftarin ne bisa "muradun Isra'ila" amma duk da haka al'ummar Gaza na son zaman lafiya, don haka za su amince da duk abin da zai sa yaƙin ya zo ƙarshe.

Can ma a kudancin Gaza, wata mahaifiyar yara huɗu ta faɗa mana cewa ba ta da wani zaɓi illa ta goyi bayan daftarin.

"Duk da rashin adalcin da aka yi wa mutanenmu, mu kawai abin da muke so shi ne kawo ƙarshen yaƙin'', kamar yadda ta bayyana mana sa WhatsApp.

"Muna matuƙar shan wahala, kuma bamu da damar ci gaba da rayuwa face amince da wannan daftarin, ko a wane yanayi, saboda muna cikin wahala.''

Matsayin hukumar Falasɗinawa kan daftarin

Hukumar kula da yankunan Falasɗinawa ta yi maraba da daftarin na Amurka.

Cikin wata sanarwa da ta kamfanin dillancin labarai na Wafa ya wallafa ya ce hukumar a shirye take wajen yin aiki da Amurka da sauran ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya domin kawo ƙarshen yakin Gaza.

Hukumar Falasdinawan ta ce a shirye take wajen tabbatar da zaman lafiyar yankin domin samun damar shigar da agaji zuwa Gaza tare da sakin isra'ialwan da ake garkuwa da su.

Sanarwar ta kuma ce hukumar na da muradin gudanar da sabbin zaɓuka a cikin shekara guda bayan ƙarear yaƙin tare da kafa tsaron yankin.

"Mun tabbatar da ƙudurinmu na son dimokradiyya da kafuwar ƙasarmu maras barazanar makamai da kuma miƙa mulki ga sabuwar zaɓaɓɓiyar gwamnati'', in ji sanarwa.

Hukumar Falasdinawa, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Mahmoud Abbas - da ke samun amincewa ƙasashen duniya ce - ke mulkin Gaɓar yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

Zaman lafiyar Gaza na hannun Hamas - Isra'ila

Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Sa'ar, ya ce ƙasarsa na fatan kawo ƙarshen yakin sai dai idan Hamas ce ba ta so hakan ba.

Yayain da yake zantawa da manema labarai a Belgrade, mista Sa'ar ya yi ikirarin cewa Hamas ce take kawo jan ƙafa a ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Gaza tun kafin yanzu.

''A yanzu ya rage nata ko za ta amince da daftarin ko kuma a a?'', in ji shi

Ya ce Isra'ila na son a sako mata duka ƴanƙasarta da Hamas ke garkuwa da su tare da karbe duka makaman Hamas ta yadda ba za ta sake zama barazana ga Isra'ila a nan gaba ba.