Ko matakin gwamnatin Najeriya na shigar da hatsi daga waje zai yi illa ga manoma?

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da alkaluma ke nuna ana samun faduwar farashin kayan abinci a Najeriya, shugabannin manoma sun bayyana damuwa game da illar shigar da kayan abinci da ake yi zuwa kasar daga kasashen waje.
Manoman na kokawa kan cewa hakan zai kara dulmuya su cikin wata sabuwar matsala ta gasa da kayan abinci masu araha da ake shigar da su kasar, baya ga fama da suke yi da tashin gwauron zabo na tsadar man fetur da takin zamani da dai sauran kayan aikin gona.
Wasu manoman ma har sun fara bayyana fargabar, cewa wannan hali da aka shiga da wuya ya bari su iya noma ko da abin da za su ci a damina mai zuwa, sai fa idan gwamnati ta dauki matakan da suka kamata
Honarabul Muhammad Magaji, sakataren watsa labarai na kungiyar manoman kasar, wato AFAN, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya samo asali ne daga izinin da gwamnatin tarayya ta bayar a cikin watan Yunin bara na shigo da abinci, don sassauta wa jama'a tsadar kayan abincin.
‘Amma kuma sai ga shi an shigo da kayan abinci a lokacin da bai dace ba’:
"Lokacin da ya kamata a shigo da abinci shi ne lokacin da abincin manoma ya ƙare sannan abincin ya yi tsada musamman watan bakwai da takwas da tara, a lokacin shi kanshi manomin yana neman abincin da zai samu ya saya da sauki," in ji Muhammad Magaji.
Masana na ganin cewa hakan ka iya zama tarnaƙi ga harkar noma a ƙasar.
Shu'aibu Idris, mai sharhi kan tattalin arziki da al'amuran yau da kullum, ya shaida wa BBC cewa yana ganin shigar da kayan abinci Najeriya daga waje a lokacin kakar kayan amfanin gona, wani babban kuskure ne:
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Idan aka yi la'akari da inda aka baro, an sayar da buhun taki da tsada, wasu sun sayar da awakinsu, wasu sun sayar da ƙadarorinsu sun sayi taki sun kuma yi noma, kamata ya yi sai gwamnati ta saye kayayyakin a farashin kasuwa, sai ta dawo ta sayar wa mutane da rangwame," in ji Mikati.
Kungiyar manoman ta Najeriya dai ta jaddada cewa, ba wai tana adawa ne da shigo da kayan abinci daga waje, don sassauta tasadar farashinsu ba ne, tana dai yin tsokaci ne, don a kauce wa ture kurtun alhaki garin neman lada.
Wasu matakan tattalin arziƙi da gwamnatin ƙasar ta fito da su - kamar cire tallafin man fetur da sauye-sauye a ɓangaren kuɗi - sun sanya kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya jefa al'umma cikin garari.
Sai dai masu hada-hadar kayan noma da BBC ta zanta da su sun nuna cewa yanzu (Watan Fabarairu) akan sayar da buhun masara kan farashin da ya kama daga 48,000 zuwa 50,000 a wasu kasuwanni da ke arewacin Najeriya.
Hakan na zuwa ne duk kuwa da cewa a farkon kaka an sayar da buhun masarar a farashin da ya kai kimanin naira 60,000.
Wani manomi ya shaida wa BBC cewa “na yi noma, kuma kowane buhun masara ya zo min gida a kan naira 45,000, idan zan kai ta kasuwa a yanzu ko kudina ba zan mayar ba”.
Sai dai duk da cewa al'umma da dama na nuna farin ciki kan lamarin, wasu na nuna shakku kan tasirin hakan a nan gaba.











