Waɗanne kayan abinci ne suka sauko bayan farfaɗowar Naira?

...

Asalin hoton, getty images

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Duk da farfaɗowar darajar Naira cikin makonnin baya-bayan nan, 'yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa da tashin farashin kayan abinci. A baya dai, an riƙa zargin 'yan kasuwa da azarɓaɓin ƙara farashin kaya a duk lokacin da darajar naira ta sake faɗuwa.

Takardar kuɗin Najeriya ta yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba a tsakiyar watan Fabrairu, inda aka canji dalar Amurka ɗaya a kan sama da naira 1,900.

Lamarin ya sa farashin kayan abinci da sauran muhimman buƙatun rayuwa sun ci gaba da ta'azzara. Rayuwa ta yi tsanani. Magidanta da yawa a ƙasar ba sa iya ko ciyar da iyalansu a rana.

Sai dai masharhanta sun ce matakan da hukumomin Najeriya ke ɗauka don farfaɗo da darajar naira, ga dukkan alamu sun fara tasiri, inda a baya-bayan nan, ake canzar da naira a kan kimanin 1,300 ga dalar Amurka ɗaya.

Duk da haka, farashin kayan masarufi da dama bai nuna alamun ranƙwafowa ba.

Wasu 'yan kasuwa da muka zanta da su, sun ɗora alhakin hakan a kan masana'antu da kamfanoni.

Shugaban kasuwar Singa da ke jihar Kano, Musa Ibrahim Nabanki ya shaida wa BBC cewa yawancin kayan abinci, farashinsu duk bai sauko ba, wasu ma ƙaruwa suka yi.

Musa Ibrahim ya ƙara da cewa fulawa a makon da ya gabata, ana sayar da buhunta a kan naira 50,500 amma yanzu ta ƙaru zuwa 52,000.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Wani gurin ma, suna sayar da buhun fulawar a kan 52,200, amma kuma farashin sukari ya sauka, a baya abin da ake sayar da shi a kan naira 80,500, yanzu kuma ya koma naira 78,200" in ji shugaban.

"Kwalin taliya kuma, sati biyu da ya wuce, ana sayar da ita a kan naira 12,650, amma yanzu kuma ana samun ta a kan farashin naira 12,600 ko 12,550, bambancin farashin kaɗan ne." in ji Nabanki.

Ya ci gaba da cewa farashin shinkafa bai ragu ba, saɓanin haka a wasu wuraren ma ƙaruwa farashin ya yi.

"Ita da ma shinkafa, farashinta gaskiyar magana bai sauka ba, saboda yawancin kamfanonin da aka samu, irin na mutanen waje ne da suka zo suka kafa."

Ya kuma ce "Waɗannan mutane suna wani salon kasuwanci ne maras daɗi, saboda a yanzu, shinkafar gida ta wasu kamfanoni, akwai waɗanda suka kai naira 75,000 a kan duk buhu ɗaya, kuma haka suke ba da ita ga 'yan sari."

"Sauran kamfanoni na sayar da shinkafar a kan naira 65,000 ko 66,000 har ma da 67,000."

Shugaban 'yan kasuwar ya ce ko a makon da ya wuce, haka farashin shinkafar yake, babu abin da ya canza, har yanzu farashintayana nan kamar a baya.

"Farashin jarkan man gyaɗa lita 25 kuma ya sauko, tun da a satin da ya gabata, ana sayar da shi a kan naira 60,000, amma yanzu ya koma naira 52,500, wasu wuraren ma 52,000 ake sayarwa."

Ya ƙara da cewa ya kamata a ce yanzu kayan abinci sun sauka tun da ana ta kurin cewa dalar Amurka ce ta yi tsada amma kuma darajar naira ta fara farfaɗowa a kan dala.

Shinkafa 'yar gida ta yi wahala a Kebbi

....

Asalin hoton, bbc

A jihar Kebbi ma, ƴan kasuwa sun ce an ɗan samu canji a farashin shinkafar waje, amma farashin sauran kayan abinci suna nan yadda suke a baya.

Wani ɗan kasuwa a garin Koko-Besse da ke Kebbi, Nura Abubakar Koko ya faɗa wa BBC cewa ba a cika samun shinkafar gida ba a Kebbi yanzu, a maimakon sun fi amfani da shinkafar waje.

"Yanzu gaskiya muna sayar da buhun shinkafa a kan farashin naira 60,000 ko 62,000 ko kuma 63,000 saboda canji ya ragu yanzu ba kamar satin da ya gabata ba da muka sayar a kan 75,000, wasu wuraren kuma dubu 70,000." in ji Abubakar.

"Farashin taliya kuma bai ragu ba, har yanzu a kan naira 13,500 muke sayar da ita."

Abubukar ya ce babu wani ragi da aka samu a kayan abinci na gida da suka haɗa da man gyaɗa da fulawa, amma buhun sukari ya ɗan sauka, inda ake samu yanzu a kan naira 77,000 bayan an sayar da shi a kan farashin 80,000 cikin makon jiya.

Abubakar shi ma ya ce rashin saukowar farashin kayan abinci na da nasaba da kamfononin da ke bayar da sarin kayan a Najeriya.

"Idan da a ce lokacin da dala ta hau ne, kawai ji za ka yi farashin kaya ya ƙaru ba tare da jin dalilin hakan ba, amma yanzu ga dala na sauka amma kayanmu na masarufi babu abin da ya ragu." Abubakar ya ƙara da cewa.

Farashin hatsi a Maigatari ya ɗan sauka

A jihar Jigawa kuma, ƴan kasuwa sun ce farashin kayan abinci na sauka da kuma tashi.

Kabiru Aminu Nada, mai harkoki ne a kasuwar mako-mako ta Maigatari da ke jihar kuma ya ce farashin hatsi ya karye sosai lokacin da aka buɗe kan iyaka, amma yanzu ya ɗan sake hawa.

"Wannan satin, abin da ake sayar da buhun gero da na dawo shi ne naira 55,000 zuwa 56,000 har da ma 57,000.

"A baya, an sayar da su a kan farashin 62,000 amma kuma a daidai lokacin da aka buɗe boda, an sayar a kan farashin 42,000, 43,000 har da 44,000 ma."

"Farashin buhun masara kuma a yanzu ya koma 57,000, bayan an sayar da ita a kan farashin naira 70,000 cikin makonnin baya."

"Farashin buhun wake a baya ya kai naira 100,000 a kan buhu ɗaya, amma a yanzu ya sauka zuwa 90,000 ko 93,000 haka."

Nada ya ƙara da cewa saukar kayan abinci a ɓangarensu babu wuya haka ma tashin su saboda suna kusa da kan iyaka ne kuma ya ce saukar kayan abincin na da ɗangantaka da kuɗin najeriya da ya fara farfaɗowa.