Matakai biyar da Tinubu ya ce ya ɗauka don kyautata rayuwar 'yan Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Wannan ne karo na uku da Tinubu ke yin bikin Ranar 'Yanci tun bayan da ya hau mulki a watan Mayun 2023
    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatinsa ke aiwatarwa zuwa yanzu sun "kori tsanani" a rayuwar 'yan ƙasar.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Laraba cikin jawabin Ranar 'Yancin Kai karo na 65 da ya gabatar a Abuja.

"Gwamnatinmu na saita al'amura. Ina mai farin cikin shaida muku cewa a ƙarshe dai mun ɗauki saiti. Manyan wahalhalu sun ƙare," in ji shi cikin jawabin da aka yaɗa a kafofin yaɗa labarai na gwamnati kai-tsaye.

Wannan ne karo na uku da shugaban ke yin bikin Ranar 'Yancin tun bayan da ya hau mulki a watan Mayun 2023, inda shi da shugabannin da suka gabace shi suka saba bayyana nasarorin da suka samu a mulkinsu ba tare da bayyana gazawa ba.

Sai dai bikin na bana ya ɗan sha bamban da saura ganin yadda gwamnatin tarayya ta sanar da soke faretin soji da aka saba yi ba tare da bayyana wani takamaiman dalili ba.

Bikin 'yancin ya faɗo a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke fama da tsadar kayayyaki, da matsalolin tsaro, da kuma ƙarancin abinci a wasu yankuna.

Yayin jawabin nasa, Tinubu ya ce gwamnatinsa na aiki tuƙuru domin kyautata rayuwar 'yan ƙasar ta hanyar magance matsalolin, waɗanda muka duba biyar daga cikinsu kamar yadda ya zayyana.

Raba wa magidanta N25,000

Bayan zayyano wasu nasarorin da Najeriya a matsayinta na ƙasa ta samu tun daga samun 'yanci a shekarar 1960, ya shiga bayyana nasarorin da shi ma ya samu a matsayin shugaban ƙasa.

Cikinsu nasarorin kuwa har da shirye-shiryen da ya ce gwamnatinsa ta ɓullo da su domin kyautatawa da sauƙaƙa rayuwar al'umma, wanda ya ƙunshi shirin nan na bai wa iyalai kuɗi.

A cewarsa, zuwa yanzu sun raba wa iyalai jimillar kuɗi naira biliyan 330.

"A ƙarƙashin shirin inganta rayuwar al'umma domin tallafa wa iyalai da raunana a Najeriya, an raba wa iyalai miliyan takwas naira biliyan 330, waɗanda da yawansu suka samu naira 25,000 sau ɗaya ko biyu cikin uku da muka bayar," a cewarsa.

Bashin sayen gida da mota

Tinubu na jam'iyyar APC ya sha yin alƙawarin bayar da bashi tun lokacin da yake yawon yaƙin neman zaɓe a fannoni da dama.

A jawabin nasa, ya ce gwamnatinsa zuwa yanzu ta yi nasarar bai wa 'yan Najeriya 153,000 bashin sayen gida da mota ta cikin shirin Credicorp.

"Credicorp shiri ne na gwamnatinmu da ya bai wa 'yan Najeriya 153,000 bashin naira biliyan 30 mai sauƙi domin sayen ababen hawa, da samar da lantarki daga hasken rana, da gyara gidajensu, da sayen na'urorin latironi, da sauransu," kamar yadda ya bayyana.

Kyautata hanyoyin sufuri

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɗaya daga cikin abubuwan da 'yan Najeriya za su dinga tuna gwamnatin Tinubu da shi shi cire tallafin man fetur da ta yi tun kafin shugaban ya shiga gidan gwamnati ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Hakan ya jawo hauhawar farashin litar man fetur daga kimain N200 zuwa fiye da N500 nan take.

A lokacin, gwamnatin Tinubu ta ce za ta ɓullo da hanyoyin rage raɗaɗin, ciki har da kawo motoci masu amfani da gas, da kuma kakkafa tashoshin da 'yan Najeriya za su sauya motocinsu zuwa masu amfani da gas ɗin, da kuma gina layukan jirgin ƙasa.

"Gwamnatinmu na ƙara faɗaɗa ayyukan sufuri a faɗin ƙasa," in ji shi. "Sun ƙunshi gina layukan dogo, da tituna, da filayen jirgin sama, da kuma tashoshi a gaɓar ruwa.

Tinubu ya yi iƙirarin cewa zirga-zirga a fannin jiragen ƙasa tsakanin 'yan Najeriya ta ƙaru da kashi 40 cikin 100 a ƙarƙashin gwamnatinsa.

"Aikin titin jirgin ƙasa na Kano-Kastina-Maradi mai nisan kilomita 284, da kuma na Kaduna zuwa Kano sun kusa kammaluwa.

"Aiki na tafiya yadda ya kamata a kan hanyar gagarumar hanyar Legas zuwa Calabar, da kuma ta Sokoto zuwa Badagry."

Bashin kuɗin karatu

Wani abu da gwamnatin take alfahari da shi tun kafin yanzu shi ne ɓullo da bashin kuɗin karatu da ta fara bai wa ɗaliban makarantun gaba da sakandare.

Shirin wanda ake kira Nigeria Education Loan Fund (Nelfund), yana bayar da bashin ne ga ɗaliban ba tare da kuɗin ruwa ba, kamar yadda gwamnati ta bayyana.

A cewar Tinubu, zuwa yanzu sama da ɗalibai 500,000 suka amfana a faɗin Najeriya.

"Mun ƙirƙiri Nelfund domin tallafa wa ɗalibai da bashi kan karatunsu. Kusan ɗalibai 510,000 ne a jihohi 36 ƙari da Abuja suka amfana daga shirin, wanda ya ƙunshi manyan makarantu 228," in ji shugaban.

"Zuwa 10 ga watan Satumba, jimillar bashin kuɗin makaranta da aka bayar ya kai naira biliyan 99.5, yayin da kuɗin gudanar da rayuwa ya kai biliyan 44.7."

Bai wa masu hidimar ƙasa jari

Wani shirin da shugaban ya bayyana a jawabin na ranar Laraba shi ne na bai wa matasan Najeriya, musamman masu yi wa ƙasa hidima wato NYSC, bashi mai suna YouthCred.

Shafin intanet na shirin ya ce aikinsu shi ne "sauya rayuwa ta hanyar samar da jarin da zai bai wa mutum dama, ba yi masa tarko ba".

Tinubu ya ce: "Shirin YouthCred da na yi muku alƙawari a watan Yuni, ya fara aiki, inda dubban 'yan NYSC ke samun jari."

Sai dai bai faɗi adadin kuɗi ko takamaiman adadin 'yan Najeriyar da suka amfana ba zuwa yanzu.