Duniya na ci gaba da alhini da addu'o'in rasuwar Fafaroma

Wata malamar coci rike da hoton Fafaroma
Lokacin karatu: Minti 3

Mabiya ɗariƙar katolika su kusan biliyan ɗaya da rabi a faɗin duniya na ci gaba da alhinin mutuwar Fafaaroma Francis, babban jagoran addininsu na tsawon shekara goma sha biyu.

Marigayin wanda ya yi shekara 88 a duniya ya rasu ne ranar Litinin sakamakon fama da cutar bugun jini da bugawar zuciya bayan jinyar da ya yi ta tsawon makonni.

Rasuwar Shugaban Cocin Katolikan na duniya Fafaroma Fafaroma Francis a ranar Litinin ta janyo alhini da addu'i da ake ta yi masa daga mabiya da ma wadanda ba mabiya ba, da Shugabannin duniya daga sassan daban-daban.

Fadarsa ta Vatican ta tabbatar da rasuwarsa ranar Litinin da karfe 07:35 agogon Vatican bayan an sallame shi daga asibiti kan jinyar cutar sanyin hakarkari ta nimoniya -inda daga bisani ya rasu sakamakon bugun jini da gazawar zuciya, a ranar Easter

Fafaroman ya kasance na farko daga yankin Latin Amurka da ya rike wannan mukami na duniya.

Yankin na Latin Amurka dai yana da kashi 40 cikin dari na mabiya darikar ta Katolika a duniya – yankin da ke alfahari da marigayin a matsayin shugaban Cocin na duniya.

'Papa Francisco', kamar yanda ake kiransa da Sifaniyanci, mutum ne da ya kasance abin kauna ga 'yan yankin hatta ga talakawa kan irin sakonninsa na nuna kauna da goyon bayana talakawa da ma sauran jama'a masu rauni.

A kasarsa Argentina shugaban kasar Javier Milei –mutumin da ke da banbancin akida sosai da Fafaroman ya ayyana zaman makomi na kwana bakwai a kasar baki daya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babban limamin Katolika na babban birnin Argentina- Buenos Aires, Jorge García Cuerva, ya gaya wa taron mabiya cewa babban sakon da 'yan kasar za su yi masa shi ne hada kai.

Za kuma a rika tunawa da Fafaroma Francis hatta a kasashen da ba su da mabiya darikar sosai misali a Cuba inda ya yi aiki tukuru wajen kokarin sasanta gwamnatin kasar da Amurka a 2014.

A wannan shekara ce dai ya ziyarci Mexico inda alkaluman yawan mabiya Cocin ke hawa da sauka.

Shugabar kasar ta Mexico Claudia Sheinbaum, ta aike da sakon ta'aziyyar marigayin kamar sauran shugabannin duniya - tana mai bayyana shi a matsayin mutum mai kaunar al'umma da ke da kusanci sosai ga hatta talakawa.

To amma kasa daya ta yankin na Latin – Argentina, kasarsa ta haihuwa bai ziyarta ba a lokacin shugabancinsa.

Hakan ta kasance ne duk kuwa da yadda 'yan kasar suka so ya ziyarta, duk da yadda take da rarrabuwar kai a siyasance bisa fargabar cewa bangarori biyu na siyasar kasar ka iya ribatar ziyarar wajen kara rabuwar.

Fafaroma Francis mutum ne da ya mayar da batun zaman lafiya a matsayin jigon addu'o'insa musamman bayan kutsen Rasha a Ukraine.

A lokuta da dama ya ya yi ta kira da a kawo karshen yakin kasashen biyu makwabtan juna – yana mai tausayawa ga al'ummar Ukraine tare da amfani da matsayi da tasirinsa wajen neman a tattauna domin sulhu.

Kazalika Fafaroma Francis din ya yi magaba da dama a kan rikicin Gaza, kuma a kai-a kai ya rika tuntubar wasu Falasdinawa Kiristoci a zirin Gaza.

Baya ga kokarin wanzar da zaman lafiya, Fafaroman ya kuma bayar da muhimmanci sosai kan batutuwan da suka shafi alkinta muhalli tare da yaki da matsalolin da ke haddasa dumamar yanayi.

Har ya aza ayar tambaya kan irin duniyar da al'ummar yau za ta bar wa 'yan baya gado.

Ba a dai bayyana ranar da za a yi jana'izarsa ba, amma za a ta kasance a tsakanin kwana hudu zuwa shida.

Kuma za a binne shi a wani kabari da ke cocin Basilica na St Mary Major a Roma a maimakon cikin Fadar Vatican.

Za a yi aƙalla kwana goma sha biyar kafin a soma taron manyan limaman da za su zaɓi magajinsa.

A ranar Talatar nan manyan limaman Cocin za su hadu domin bayyana ranar da za a yi jana'izarsa.