Arsenal na neman Sesko, Munich da Madrid da Milan na rububin Donnarumma

Lokacin karatu: Minti 3

Newcastle za ta dauko dan wasan Nottingham Forest Anthony Elanga, Arsenal na zawarcin Benjamin Sesko, yayin da Manchester United ta mika tayi na biyu kan dan wasan gaba Bryan Mbeumo.

Newcastle United ta yi yunkurin dauko dan wasan gefe dan kasar Sweden Anthony Elanga mai shekara 23 daga Nottingham Forest. (Mail)

Arsenal ta tuntubi RB Leipzig a hukumance domin sayen dan wasan gaba na Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 22. (Sky Sports)

Manchester United ta yi tayin fan miliyan 60 kan dan wasan Brentford da Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, bayan da aka ki amincewa da tayin farko da ya kai fam miliyan 55. (ESPN)

Inter Milan ta yi binciken bayan fage kan dan wasan Manchester United da Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22. (Teleghraph)

Lyon ta yi watsi da tayin farko da Manchester City ta yi kan dan wasan Faransa Rayan Cherki, mai shekara 21, yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu. (Florian Plettenberg)

Tottenham za ta biya sama da fam miliyan 10 idan har tana son kawo kocin Brentford Thomas Frank don maye gurbin Ange Postecoglou, wanda Spurs din ta kora. (Mirror)

Zakarun Seria A Napoli na duba yiwuwar zawarcin dan wasan baya na Ingila Trevoh Chalobah mai shekaru 25, wanda ya taimakawa Chelsea ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai da kuma lashe gasar Uefa Conference League bayan ya dawo daga matsayin aro a Crystal Palace a watan Janairu. (Telegraph)

Bayern Munich, da Real Madrid da AC Milan na zawarcin golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, idan ya kasa amincewa da sabuwar yarjejeniya a Paris St-Germain, yayin da Inter Milan da Juventus za su jira kwantiraginsa ya kare a shekara ta 2026, kafin ya koma. (Gazzetta dello Sport)

Arsenal na cikin kungiyoyin da ke zawarcin golan Spain Kepa Arrizabalaga, mai shekara 30, wanda farashinsa ya kai fam miliyan 5 (Evening Standard)

Dan wasan tsakiya na Ingila Angel Gomes, wanda ke shirin barin Lille a karshen kwantiraginsa a wannan bazarar, ya kulla yarjejeniya da Marseille, wacce ta doke Tottenham da West Ham wajen siyan dan wasan mai shekaru 24. (RMC Sport)

Crystal Palace ta nemi dan wasan bayan Sporting da Ivory Coast Ousmane Diomande, wanda zai kai kusan fam miliyan 45. (Telegraph)

Sunderland ta yi watsi da tayin da Borussia Dortmund ta yi mata na sayen dan wasan tsakiyar Ingila Jobe Bellingham, amma kungiyoyin na ci gaba da tattaunawa kan cinikin dan wasan mai shekaru 19. (Sky Sports Germany)

AC Milan ta nuna sha'awarta ta zawarcin dan wasan Bayer Leverkusen dan kasar Switzerland Granit Xhaka, mai shekara 32, yayin da kulob din na Bundesliga ke ganin yana son dauko dan wasan baya na Jamus Malick Thiaw, mai shekara 23, daga kulob din Seria A. (Kicker in German)