Barcelona na tattaunawa da Partey, Liverpool na harin Kerkez

Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta shiga tattaunawa da ɗan wasan tsakiya a Arsenal da Ghana, Thomas Partey, mai shekara 31, wanda kwantiraginsa ke ƙarewa cikin watan Yuni. (Sun)

Liverpool na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Bournemouth da Hungary, Milos Kerkez mai shekara 21, wanda ake kiyasin kuɗinsa kan £40m. (GiveMeSport)

Liverpool ta gaza bayan gabatar da tayi har biyu kan ɗan wasan Bayer Leverkusen da Jamus, Florian Wirtz mai shekara 22, yanzu dole su karkata kan Harvey Elliott na Ingila mai shekara 22 da Jarell Quansah mai shekara 22. (Kicker via Mirror)

Ɗan wasan Ipswich da Ingila, Liam Delap mai shekara 22, ya kammala binciken farko na lafiya a kokarin komawa Chelsea kan kwantiragin £30m. (Fabrizio Romano)

Everton na son ɗan wasan tsakiya a Brighton, Matt O'Riley mai shekara 24, amma ba ta da tabbacin za a sayar mata da shi. (Sky Sports)

Tsohon kocin Napoli da Chelsea da Juventus, Maurizio Sarri mai shekara 66, na iya kowa aikin horas wa a ƙunbgiyar Lazio. (Fabrizio Romano)

Bayer Leverkusen ta amince da yarjejeniyar yuro miliyan 10 kan mai tsaron raga a Netherlands, Mark Flekken daga Brentford. (Sky Germany)

Brentford ta amince da yarjejeniya £12.5m zuwa £18m da Liverpool kan mai tsaron ragarta, Caoimhin Kelleher, mai shekara 26 domin maye gurbin Flekken. (Sky Sports)

Kocin Inter Milan Simone Inzaghi mai shekara 49, zai yanke hukunci a ranar Laraba kan ko zai amince da yarjejeniyar horas da Al-Hilal a Saudiyya. (Rudy Galetti)

Daraktan wasanni a Barcelona Deco ya ce ba sa neman sabon ɗan wasan gaba bayan rahotanni na alakantasu da ɗan wasan Sweden, Viktor Gyokeres mai shekara 26, wanda dama Arsenal da Manchester United na bibiyarsa. (A Bola via Mirror)

Mai tsaron raga a Jamus, Marc-Andre Ter Stegen mai shekara 33, ya ce bai damu da matsayinsa a Barcelona ba, wanda ake alakantawa da Joan Garcia, mai shekara 24. (Forbes)