Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda na rasa hannayena a kamfanin sarrafa tayoyi a Kano'
A wani labari mai ban tausayi, wani matashi da ya rasa hannayensa biyu a wani mummunan hatsari a wani kamfani da ke jihar Kano, ya koka kan halin ko-in-kula da kamfanin ke nunawa a kansa.
Matashin mai suna Aliyu Ahmad, ɗan asalin jihar Katsina ya gamu da hatsarin ne kwanaki bayan fara aiki a kamfanin.
Aliyu mai shekara 25 ya buƙaci hukumomi da ƙungiyoyi su shiga lamarinsa wajen ganin kamfanin ya cika alƙawarin da ya ɗauka na biyansa diyya da ɗaukar ɗawiniyar wasu abubuwa.
Duk da kasancewar kamfanin ya kai shi asibiti, amma har yanzu bai samu kuɗin diyyar ba, sannan kamfanin ya gaza cika alƙawarin ɗaukar ɗawainiyar jinyarsa da ya yi a baya.
Yaya lamarin ya faru?
Cikin wani yanayi na ban tausayi Aliyu ya shaida wa BBC yadda al'amarin ya kasance da kuma yadda ya sauya rayuwarsa.
Ya ce ya gamu da iftila'in ne mako guda da soma aiki da kamfanin mai sarrafa tsoffin tayoyi domin mayar da su sabbi.
''Ina tsaka da aiki da wani katafaren injin niƙa tsoffin tayoyi, to da yake zuba tsoffin tayoyin ake yi cikin inji, shi kuma sai ya niƙe, to waɗanda ba su kammala niƙuwa ba, suka fito waje, mu kuma sai mu sake ɗaukar su mu sake turawa cikin injin'', in ji shi.
''Idan guntaye inji ya turo waje, mu kan yi amfani da itace wajen sake tura su, amma idan dogaye ne, mukan ɗauka da hannu mu saka cikin bakin injin, daga nan sai injin ya ja tayar domin niƙe ta'', kamar yadda ya bayyana wa BBC.
''To na saka tayar kawai sai ta naɗemin hannuna guda ɗaya, injin kuma nan take ya murje min hannu, na tsala ihu ta yadda sai da kowa da ke ɗakin ya jiyo ihuna, mutane sun taho domin kawo min ɗauki, amma ba yadda suka iya''.
Ya ƙara da cewa a lokacin da injin ke markaɗe masa hannu "ɗimuwar da na shiga" ya sa ya sanya ɗayan domin janyo shi, nan take shi ma injin ya kama shi, ya kuma markaɗa su duka.
Daga ƙarshe an samu nasarar zare duka hannayen matashin, aka kuma garzaya da shi asibiti domin yi masa magani.
'Sai da na kwana biyu a asibiti kafin a min aiki'
Matashin ya ce ko da aka kai shi asibitin bai samu kulawar gaggawa ba.
Domin kuwa ya ce sai da ya shafe tsawon kwana biyu a sibitin kafin ya samu a yi masa aiki.
Aliyu ya ce da farko kamfanin ya yi ƙoƙari wajen kula da lafiyarsa, domin duk abin da aka ce ana buƙata nan take za su saya.
''Har ma suka faɗa wa duniya cewa za su saya min hannu mai motsi (sensor), sannan za su ɗauki ɗawaniyar rayuwata, kuma za su biyani diyya'', in ji shi.
Ya ce bayan an sallame shi daga asibitin, sai mahaifiyarsa ta buƙaci su je kamfanin a yi komai a rubuce na alƙawuran da suka yi.
''Bayan mun je tare da mahaifiyata da wasu ƙannenta, wakilan kamfanin suka faɗa mana cewa hannun ma a naira miliyan15 za su yi min'', kamar yadda ya bayyana.
Yadda lamarin ya sauya
Matashin ya ce sun fara ganin sauyi ne bayan da suka sake komawa domin bin bahasin alƙawuran da kamfanin ya yi.
''Da muka je domin tambayar su makomata, sai suka riƙa yi mana magana a wulaƙance, har suna cewa makomar tawa ta wuce a bani miliyan ɗaya ko biyu, irin a wulaƙancen nan, magana dai maras daɗi'', in ji shi.
Haka dai ya ce suka taso daga kamfanin babu daɗi.
"Bayan mun dawo sai ga wayar wanda kamfanin ya wakilta game da lamarin nawa, ya kira mu yake ce mana oga ya ce an fasa yi min hannun, saboda yana da tsada, kawai miliyan huɗu za su ba mu, mu yi haƙuri'', kamar yadda ya ce.
''Muna son komawa asibiti domin su sake duba aikin da suka min, saboda sun ce min idan ma wurin bai [gama] haɗewa ba za su yanki naman cinya ta su dasa a wurin'', in ji shi.
Babban fatana shi ne a bi min haƙƙina
Yanzu haka dai matashin na kwance a gida, kuma a cewarsa kamfanin ya yi watsi da shi, duk da irin tarin ɗawainiyar da yake fama da ita.
Matashin ya ce yanzu yana cikin halin damuwa da takaici, domin komai na ɗawainiyar rayuwarsa mahaifiyarsa ce ke yi masa.
''Yanzu babban fatana shi ne a taimaka a bi min haƙƙina a wajen wannan kamfani'', kamar yadda ya ce.
Ƴan'uwan Aliyu dai sun ce a baya wasu mutane sun yi niyyar taimakonsa, amma da suka fara tattaunawa sai suka buƙaci kuɗi, sai suka faɗa musu cewa kuɗin komawa asibiti ma wahala ke yi musu, daga nan ba su sake ji daga gare su ba.
Me kamfanin ya ce?
BBC ta tuntuɓi kamfanin domin jin ta ɓangaren sa, kuma wani jami'in kamfanin da BBC ta tuntuɓa ta waya, ya ce yana kan hanyar zuwa Obajana, kuma da zarar ya isa zai tuntuɓe mu.
To sai dai har zuwa rubuta wannan rahoto, jami'in bai kira mu ba.
A lokuta da dama a Najeriya a kan zargi kamfanonin waje da ɗaukar ƴan ƙasar ba tare da biyansu abin da ya kamata ba.
Sannan ba sa kula da matakan kariya ga ma'aikatansu.