Ɗan Najeriya da hukumar tsaron FBI ta Amurka ke nema ruwa a jallo

Asalin hoton, FBI
Hukumar Bincike ta FBI a Amurka ta sanar da tukwicin kuɗi dala 10,000 (kimanin naira miliyan 14) ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kama an Najeriya Olumide Adebiyi wanda ke ta wasan ɓuya da hukumomi tsawon shekara 20.
Hukumar FBI ta bayyana haka ne a wani bayani da ta wallafa a shafinta na intanet a ranar Laraba 24 ga watan Satumba, inda ta ce mutumin ya tsere daga yankin tsakiyar gundumar Illinois a watan Disamban 2001, gab da gurfanar da shi a kotu.
Ana zargin ɗan Najeriyar ne da aikata laifuka da suka haɗa da damfarar banki, damfara wajen haɗa takardun shaida da kuma damfara ta amfani da katin banki.
"Ana neman Olumide Adebiyi Adediran ne kan karya ƙa'idojin beli. A watan Agustan 2001, an zargi Adederian da shiga wani banki a yankin Champaign na Illinois inda ya yi yunƙurin cire kuɗi daga wata ajiya da aka yi a bankin ta hanyar damfara.
"Haka nan ana zargin shi da satar bayanan wasu Amurkawa sannan ya yi amfani da bayanan wajen buɗe asusun ajiya a banki. Inda Adediran ya tsere daga gundumar tsakiyar Illinois a ƙarshen watan Disamban 2001, gab da fara shari'arsa bayan hukumomi sun tuhume shi da ayyukan damfara na banki, da bayanan sata da kuma amfani da katin cirar kuɗi ta hanyar damfara," in ji bayanin.
Hukumar FBI ta ce a watan a ranar 2 ga watan Janairun 2002 wata kotu da ke gundumar Illinois ta bayar da takardar kama Adediran bayan an tuhume shi da karya ƙa'idar beli.
Wannan ba shi ne karon farko da FBI take ayyana cewa tana neman wani ɗan Najeriya ruwa a jallo ba bisa zargin damfara.
Bayan ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a watan Disamban 2024, an samu nasarar kama wani ɗan Najeriya Abiola Kayode inda aka kai shi jihar Nebraska da ke Amurka domin fuskantar hukunci kan laifin zamba ta intanet.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
FBI ta zargi Kayode da laifin kasancewa cikin ƙungiyar masu damfarar da ake wa laƙabi da yahoo-yahoo, wadanda suka damfari mutane a Nebraska da kuma wasu wuraren da dama na kuɗi sama da dala miliyan shida (kimanin naira miliyan 8.9).
"Kayode, wanda ake zargi da laifin damfara, wanda ke cikin jerin mutanen da hukumar bincike ta FBI ke nema ruwa a jallo, na cikin waɗanda suka yi damfarar saƙon email daga watan Janairun 2015 zuwa Satumban 2016.."
A watan Afrilun 2025, FBI ta ce ta kama mutane 22 da take zargi da damfara ta intanet, wadanda suke amfani da wata dama wajen tatsar kuɗi daga yara Amurkawa ta hanyar damfara da tsoratarwa.
Hukumar ta sanar a shafinta na intanet cewa kamen na daga cikin aikinta na musamman da ta yi wa laƙabi da "Operation Artemis", wanda aka ƙaddamar a shekarar 2023 domin yaƙi da yawaitar ayyukan ƙungiyoyi masu amfani da barazana da hotunan tsiraici a matsayin makami wajen yin damfara.
Hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ce tare da hadin gwiwar hukumar binciken ta FBI da ke Amurka suka gudanar da binciken, wanda ya haifar da kamen mutanen da ake zargi.
Hukumar ta ce kimanin rabi daga cikin mutum 22 da ake zargi, na da alaƙa kai-tsaye da mutanen da suka kashe kansu sanadiyyar irin wannan damfara.
"Wannan aiki wani mataki ne a ƙoƙarin da ake yi wajen yaƙi da matsalar tatsar kudi daga yara, da tabbatar da adalci a kan mutanen da ke ɓoyewa a ƙasashen waje suna aikata laifi," in ji hukumar FBI.











