Hanyoyin da ake bi domin fara samun kuɗi a Facebook

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Daga cikin abubuwan da ke tashe a ƴan kwanakin nan a kafofin sadarwa a arewacin Najeriya, musamman a Facebook shi ne wani sabon salon da za ka ga matasa suna zuwa ƙarƙashin rubutu suna roƙon a fara bibiyar shafinsu.
Sukan rubuta 'ka bi ni, zan bi ka' wato 'Follow me I will follow you back,' ko kuma 'follow for follow' da Ingilishi, lamarin da ya sa wasu suke fushi, har a wasu lokutan suke zagin waɗanda suka buƙaci hakan.
Wannan abu ya fara tashe ne bayan mahukunta Facebook sun amince da Najeriya a cikin ƙasashen da za su fara biyan kuɗi, wato 'monetization', lamarin da ya sa matasa da dama suka tashi haiƙan wajen neman shiga cikin waɗanda za su fara cin moriyar kafar ta hanyar samun daloli.
Sai dai masana sun ce akwai wasu ƙa'idoji da sharuɗɗa da suka zama dole mutum ya cika kafin kafar Facebook ɗin ta fara biyan shi, lamarin da masu bibiyar lamarin suke ganin wasu matasa da suke neman kuɗin ba su ma kama hanyar ba, ballantana su fara cin moriya.
Shin waɗanne hanyoyi ake bi kafin a fara samun kuɗin? kuma ko hanya ɗaya ce ake bi domin samun kuɗi a Facebook da Instagram da sauran kafofin?
Hanyoyi fara samun kuɗi a Facebook
Domin sanin hanyoyin da suka kamata a bi, BBC ta tuntuɓi Abdullahi Salihu Abubukar, wanda aka fi sani da Baban Sadiq, wanda masanin fasahar zamani ne a Najeriya.
Ya ce a dandalin Facebook akwai hanyoyi da dama da za a iya bi don samun kuɗi, "musamman idan kana da mabiya masu yawa kuma ka wallafa bayanai masu jan hankali ga mabiyanka."
Baban Sadiq ya bayyana wasu fitattu daga cikin waɗannan hanyoyi dai sun haɗa da:
- Talla a cikin bidiyo (Facebook Ad Breaks): Idan kana da shafin da ke da bidiyo masu tsawo da mabiya da yawa, za ka iya samun kuɗi ta hanyar tallace-tallace da Facebook ke sakawa a cikin bidiyonka. A yayin da masu kallo ke bibiyar bidiyon, lokaci zuwa lokaci za a riƙa tallata hajoji a ciki, don bai wa masu kallo damar mu'amala da tallar.
- Tallar hadin gwiwa (Brand Partnerships): A ɗaya ɓangaren kuma, kamfanoni na iya biyanka don tallata musu hajojinsu idan kana da tasiri a Facebook, sanadiyyar mabiya masu yawa don ƙayatar da su da kake yi. Wannan shi ake kira: "Brand Partnership", ma'ana, haɗaka tsakaninka da kamfanoni don tallata musu wasu hajojinsu na musamman.
- Kamashon talla (Affiliate Marketing): Wannan tsari ne na tallata hajojin wasu kamfanoni ga mabiyanka a Facebook, ta yadda idan wani daga cikinsu ya bi adireshin da kake bayarwa, har ya je ya sayi kayan, to, kana da wani kamasho na musamman kan hakan.
- Kyautar live (Facebook Stars): Idan kana yin "Facebook live" ko "Instagram live", mabiya za su iya turo maka da tambarin taurari a matsayin kyaututtuka ("stars") wanda ke da ƙima ta kuɗi. Kuma kana musanya su da kuɗaɗe na haƙiƙa idan kana buƙata.
Ya ƙara da cewa akwai hanyar da ta shafi amfani da Facebook don tallata kayanka ko ayyukanka kai tsaye. "Wannan don amfanin kanka ne da kanka. Ba wanda zai biya ka, amma za ka samu abokan hulɗa, tunda kana tallata hajarka ne."
Bambancin Facebook da sauran kafofin sadarwa

Asalin hoton, Getty Images
Ganin cewa ba a Facebook ba ne kaɗai ake iya samun kuɗi, wannan ya sa Baban Saɗiq ya ce akwai kamanceceniya a tsakanin kafofin, sannan ya ce akwai kuma bamban-bambance.
Ga wasu daga cikin bambance-bambancen da ke tsakani kamar yadda ya yi ƙarin bayani:
Facebook: Tallace-tallace da kyautuka (Ad Breaks, Stars, Brand Deals)
Yana buƙatar mabiya masu yawa, kuma ya zama suna ta'ammali da bayanan da kake wallafawa. Wannan shi ake kira: "engagement". Sun haɗa da yin ta'aliƙi (comment) kan abin da kake wallafawa, jinjinawa, wato latsa alamar "like" da dai sauransu.
YouTube: Tallace-tallace da zama mamba (Ads, Memberships, Super Chat)
Yana buƙatar adadin kallo ("views" da "watch time") mai yawa.
TikTok: Tukwicin kamfani da tallace-tallace (Creator Fund, Brand Deals)
Yana buƙatar wallafa saƙonni masu saurin yaɗuwa (viral content).
Instagram: Ɗaukar nauyi (Sponsored Posts, Affiliate)
Tasiri da kyawun hotuna yana da muhimmanci.
Shin matasan Arewa suna samun kuɗi a Facebook?
A daidai lokacin da wasu ke murna da fara samun kuɗin, a gefe guda kuma wasu na ganin babu wani abin a zo a gani, domin a cewarsu, babu wani kuɗin da za a samu na kirki.
A game da wannan, masanin na kimiyya ya ce lallai ana samun kuɗi, sannan ya ƙara da cewa matasan arewa ma sun fara samun tagomashi.
"Matasa da dama daga Arewacin Najeriya suna samun kuɗi ta wannan tsari na Facebook Monetization. Yayin da wasu ke amfani da shafukansu wajen tallata hajojin kasuwanci, wasu kuma suna wallafa bidiyo ne masu ban dariya, ilimantarwa da nishaɗantarwa," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, "A ɗaya ɓangaren kuma, wasu na samun kuɗi ta hanyar yaɗa saƙonnin addini da ke jan hankalin jama'a su ma suna samun kuɗi."
Sai dai ya ce samun alƙaluman matasan arewacin Najeriya da ke amfani da wannan tsari yana da wahala, "domin bayanai ne da kamfanin Meta ba ya bayyanawa, saboda dalilan kasuwanci da tsaro."
Akwai sauƙi?
Wasu matasa sun ƙara ƙaimi ne a Facebook da tunanin an fara samun kuɗi, inda suke ganin za su shiga, su samu maƙudan kuɗaɗe.
Saboda masu irin wannan tunanin ne Baban Sadiq ya ce duk da cewa ana samun kuɗin, lallai akwai aiki ja.
"Samun kuɗi a kafar Facebook ba abu ba ne mai sauƙi, amma abu ne mai yiwuwa. Wasu na samun dubban nairori har zuwa miliyoyi idan sun samu mabiya da yawa da kuma wallafa abun da ke jan hankali. A taƙaice dai, samun kuɗaɗe ta wannan tsari ya danganci abubuwa ne masu yawa."
A ƙarshe Baban Sadiq ya bayar da wasu shawarwari da yake tunanin idan aka yi amfani da su za a ci moriyar lamarin:
- Lokaci da juriyar mutum wajen dagewa da jajircewa
- Ingantattun bayanan da ake wallafawa
- Fahimtar yadda lissafin dandalin Facebook (Facebook algorithm) ke aiki
- Yawan mu'amala da mabiya shafin
Amfani da 'follow for follow'

Asalin hoton, Getty Images
A game da abin da ke tashe a arewacin Najeriya da matasa suke amfani da kalmar 'bi ni, in bi ka' domin tara mabiya a ƙoƙarin da suke yi na fara samun kuɗi a Facebook, Baban Sadiq ya ce babu laifi.
A cewarsa, "Wannan dabara tana da tasiri na ɗan lokaci ne kaɗan; tasirinta ba mai ɗorewa ba ne. Mabiyan da ake samu ta hanyar "follow for follow" ba lallai ba ne su riƙa kallon abun da kake wallafawa.
Lissafin Facebook ya fi ba da muhimmanci ga yawan tu'ammali da saƙonni da mabiyanka ke, wato "engagement" (irin su "likes", da "comments", da "shares" da sauran makamantansu) fiye da yawan mabiyanka. Don haka, abin da ya dace mai shafi ya yawaita yi su ne kamar haka:
- Mayar da hankali kan abubuwa masu jan hankali
- Tabbatar da lumana wajen ma'amala da mabiyanka
- Yawaita wallafa saƙonni masu amfani da sanya nishaɗi.











