Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ivory Coast ta yanke hulɗar soji da Faransa
Sannu-sannu dai Faransa na ci gaba da rasa tasirin da take da shi a wannan yanki na Afirka ta Yamma, da irin wannan mataki da tsofaffin kasashen da ta yi wa mulkin mallaka ke kawo karshen yarjejeniyar zaman sojin Faransar a kasashen.
A wani jawabi na karshen shekara da Shugaba Alassane Ouattara ya gabatar ga kasar, ya ce matakin kuduri ne na neman zamanantar da dakarun kasar tasa.
Matakin ya kasance irin na Nijar da Mali da Burkina Faso, wadanda tuni suka raba gari da sojojin tsohuwar uwargijiyar tasu amma kuma bayan da sojoji suka yi juyin mulki a kasashen tare kuma da karuwar kyama da kin jinin Faransar da ake yi a kasashen.
Sai Chadi wadda babbar kawa ce ga kasashen yammacin duniya a kan yaki da kungiyoyin masu ikirarin jihadi a yankin wadda ita ma ta kwatsam a watan Nuwamba ta sanar da aniyarta ta raba gari da Faransar a yarjejeniyar sojin.
Senegal ma a wadda a wannan wata na Nuwambai ta sanar da kawo karshen zaman sojin Faransar, a karon farko ta bayar da wa'adin ficewar sojin na waje, zuwa nan da karshen wannan sabuwar shekara ta 2025.
Shugaban kasar ta Senegal Bassirou Dioumaye Faye, ya ce ya umarci ministan tsaron kasar da ya bullo da wani sabon daftari na alakar tsaro wanda zai kunshi abubuwan da suka hada da kawo karshen zaman duk wata tawaga ta sojin waje a Senegal daga wannan sabuwar shekara ta 2025.
A watan Maris aka zabi Faye a shugabancin kasar bisa alkawuran da suka kunshi tabbatar da cikakken 'yancin cin gashin kai da kawo karshen dogaro ga kasashen waje.
Yanzu dai Gabon ce kasar da Faransa za ta ci gaba da kasancewa da sansanin sojinta -wadda ita ma kadan ne a can.
Ivory Coast ta kasance kasar da ta rage da Faransa take da tawaga babba ta soji a Afirka ta Yamma, inda take da Dakaru har 600, sai kuma Senegal mai 350.
Sama da shekara 30 bayan samun 'yancin kai daga Faransa, Ivory Coast, wadda kuma ake kiranta da suntan na Faransanci, Côte d'Ivoire, ta yi fice a kan zaman lafiya da mutunta juna a tsakanin al'ummominta duk da bambancin addini da kabila, da kuma ingantaccen tattalin arziki.
Kasar ta kasance abar nuni da misali a zaman lafiya, kafin ta gamu da tawayen da ya raba kanta biyu a shekara ta 2002.
Sannu a hankali, bayan yarjeniyoyi na zaman lafiya da kan gamu da sabon rikici a kokarin samun mafita ta siyasa ga tashin tashinar.
Duk da wannan matsala ta rashin kwanciyar hankali, Ivory Coast ta kasance kasa ta daya da ta fi fitar da koko a duniya, kuma 'yan kasar akalla suna cin moriyar wannan arziki sosai idan aka kwatanta su da takwarorinsu na sauran kasashen yankin na Afirka ta Yamma.