Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce gaskiyar zuwan sojojin Faransa arewacin Najeriya?
Daga ƙarshen makon da ya fice zuwa farkon wannan mako, an riƙa yaɗa wani faifan bidiyo a Najeriya cikin harshen Hausa, wanda a ciki ake iya ganin wani jami'in sojin Najeriya tare da wani soja farar fata a bayansa.
Masu yaɗa bidiyon sun bayyana cewa baturen da ke cikin bidiyon ɗaya ne daga cikin sojojin Faransa da suka isa jihar Borno da ke Najeriya domin taimaka wa sojin Najeriya wajen yaƙi da mayaƙan Boko Haram a yankin.
Borno jiha ce da ta kasance cibiyar rikicin Boko Haram, wata ƙungiya da ta shafe sama da shekara 10 tana kai hare-hare kan jami'an tsaro da farar hula a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Rikicin wanda ya shafi ƙasashe masu maƙwaftaka, kamar Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru ya yi sanadin rasa rayukan mutum aƙalla 36,000 da kuma tarwatsa wasu mutanen fiye da miliyan ɗaya.
Duk da cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar rage kaifin hare-haren ƙungiyar, har ma a baya hukumomi suka ayyana 'yin galaba' a kanta, har yanzu mayaƙan ƙungiyar na kai hare-hare lokaci zuwa lokaci.
Ba dai sabon abu ba ne a ga ƙasashen da ke fama da irin waɗannan rikice-rikice na samun taimakon ƙasashen duniya a ƙoƙarin daƙile irin waɗannan ayyuka na masu ƙungiyoyin masu tayar da tarzoma.
Shi ya sanya kafin yanzu, wasu daga cikin ƙasashen yammacin Afirka da na Sahel suka bai wa manyan ƙasashen duniya damar kafa sansanonin soji a cikinsu da sunan yaƙi da ayyukan ta'addanci a yankin.
Sai dai bayan juyin mulki a Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkin Faso, ƙasashen uku sun raba gari da uwargijiyarsu Faransa da kuma Amurka da ma wasu ƙasashen Turai, ta hanyar katse yarjejeniyoyi na tsaro da su.
To amma mece ce gaskiyar bidiyon da ake yaɗawa na cewa sojojin Faransa sun isa Najeriya a wani yunƙuri na kafa sansani?
Martanin sojin Najeriya
A tattaunawarsa da BBC, daraktan yaɗa labaru na shalkwatar tsaro ta Najeriya, Birgediya-Janar Tukur Gusau ya musanta batun isar tawagar sojin Faransa a Najeriya.
Ya ce "idan za a iya tunawa, tun kafin ma a saki wannan bidiyo, CDS (Babban hafsan sojin Najeriya) ya faɗi cewa babu wata yarjejeniya domin kawo sojojin Faranshi a kowane yanki na faɗin Najeriya".
Janar Gusau ya bayyana cewa bidiyon da ake yaɗawa tsoho ne kuma ba sojojin Faransa ba ne a cikin bidiyon.
Tun farko, shalkwatar tsaro ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa da safiyar ranar Litinin tana musanta kasancewar sojin na Faransa a Najeriya.
Sanarwar, wadda ta samu sa hannu daraktan kula da sashen yaɗa labaru na shalkwatar tsaron, Manjo-Janar Edward Buba, ta ce "an janyo hankalinta kan wasu rahotanni da ake yaɗawa a shafukan intanet da ke cewa wata tawagar sojin Faransa ta isa Maiduguri a wani yunƙuri na kafa sansanin sojin Faransa a arewa maso yammacin Najeriya".
"Wannan bayani ƙage ne, ƙarya ce kuma an yi ne da wata manufa," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Waɗanne sojoji ne a cikin bidiyon da ake yaɗawa?
Birgediya-Janar Tukur Gusau ya ce turawan da aka gani a cikin bidiyon da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta turawan Birtaniya ne ba na Faransa ba.
"Jami'an soja na Birtaniya ne, ana kiran su 'British Military Technical Training Team'", sojoji ne masu bayar da horaswa kan sarrafa makamai, in ji Gusau.
A cewarsa tawagar ta sojojin Birtaniya ta daɗe tana aiki a Najeriya, "kusan sun fi shekara 50 suna aiki a Najeriya," in ji daraktan yaɗa labaran na shalkwatar tsaron Najeriya.
"Sukan zo ne su yi wa mutanenmu training (bayar da horo) a kan kayan aiki da muke sayowa, kan yadda ake amfani da su, kuma su riƙa kula da su (kayan) domin tabbatar da cewa suna cikin yanayin da za a iya amfani da su a kodayaushe".
Haka nan Gusau ya bayyana cewa dakarun Najeriya ba su fita fagen yaƙi da irin waɗannan sojoji na ƙasashen waje masu bayar da horo ga dakarun Najeriya.
Ya ƙara da cewa idan aka lura za a ga cewa kayan sojin da ke jikin turawa "ba na sojin Faranshi be, na sojojin Ingila ne."
Ko a watan Fabarairun 2024, jami'an Najeriya da na Birtaniya sun gudanar da taro a ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro ƙarƙashin shirin haɗin gwiwa kan harkokin tsaro na Najeriya (Nigeria Security and Defense Partnership).
A lokacin taron, ɓangarorin biyu sun amince su ƙarfafa haɗin gwiwar da ke tsakanin su a ɓangarori da dama.
Sai dai korar da ƙasashen yankin Sahel suka yi wa sojojin Faransa da na Amurka da ma wasu ƙasashen Turai na haifar da raɗe-raɗi tsakanin ƴan Najeriya a kan cewa wasu daga cikin irin waɗannan ƙasashe za su iya yunƙurin neman wata ƙasa da za su jibge dakarunsu.
Amma rundunar sojin Najeriya ta sha musanta yiwuwar hakan.
Baya ga matsalar Boko Haram, Najeriya na fuskantar ayyukan ƴan bindiga a arewa maso yammacin ƙasar, waɗanda suka tarwatsa ƙauyuka da dama a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna da kuma Neja.