Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nasarorin da sojojin Najeriya suka ce sun samu kan ƴanbindiga cikin 2024
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da 'yanbindiga a ƙasar tsawon shekara guda da ta gabata.
Cikin wata sanarwa game da nasarorin da sojojin ƙasar suka samu, kakakin hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edwar Buba, ya ce rundunar sojin Najeriya ta kashe 'yanbidiga 8,034 tun daga watan Janairu zuwa Disamban shekarar 2024.
''An kuma kama 'yanbidiga 11,623 tare da kuɓutar da mutum 6,376 da aka yi garkuwa da su," in ji Janar Buba.
Ya ƙara da cewa: "Sannan dakarunmu sun samu nasarar ƙwato makamai 8,216, da harsasai 211,459, da kuma daƙile satar man fetur da kudinsu ya kai kimanin naira biliyan 57."
Sanarwar ta yi cikakken bayani game da nasarorin da rundunonin sojin ƙasar daban-daban da ke yaƙi da 'yanbidiga suka samu a tsawon watannin 11.
'Rundunar Operation Hadin Kai ce kan gaba'
Sanarwar sojojin ta nuna cewa rundunar 'Operation Hadin Kai' mai yaƙi da Boko Haram da ƙungiyar ISWAP a yankin arewa maso gabashin ƙasar ce ke kan gaba a wannan nasara bayan da ta kashe adadin 'yanta'adda 2,918 a tsawon shekarar, yayin da 'yanbindigar tare da iyalansu kimanin 15, 950 suka miƙa wuyansu ga rundunar.
Sannan kuma rundunar ta Haɗin Kai ta samu nasarar kama 'yanbindigar su 2,285, suka kuma kuɓutar da mutum 1,496 da aka yi garkuwa da su.
Rundunar mai yaƙi da Boko Haram ta kuma samu nasarar ƙwato makamai 2,787 tare da harsasai 67,129 a tsawon wannan lokaci, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
Daga nan sai rundunar 'Operation Hadarin Daji' mai yaƙi da 'yanbindiga masu garkuwa da matane a yankin arewa maso yammacin ƙasar da wasu sassan Arewa ta Tsakiya, wadda ita ma ta kashe adadin 'yanbindiga 2,646 a tsawon shekarar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa rundunar 'Operation Punch Whirl' mai yaƙi da 'yan bindiga a yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar ce ta uku a nasarar kashe 'yanbindiga a shekarar da muke ciki, bayan ta 'yanbindiga 732, tare da kama wasu 1,842.
''Operation Whirl Punch ta kuma kuɓutar da mutum 569 da aka yi garkuwa da su, ta kuma ƙwato makamai 640 da harsasai 23,836'', in ji Manjo Janar Edwar Buba.
Sanarwar ta nuna cewa rundunar 'Operation Delta Safe' da ke yaƙi da 'yanbindiga masu satar mai a yankin Naija Delta ce ta kashe adadi mafi ƙanƙanta na 'yan bindiga a cikin shekarar, bayan da ta kashe 'yanbingiga 78.
To sai dai rundunar ta samu nasarar daƙile satar ɗanyen man fetur da kuɗinsa ya kai kimanin naira biliyan 54.
''Rundunar ta kuma samu nasarar lalata jiragen ruwa na satar mai kimanin 1,880 tare da gano haramtattun rijiyoyin mai 2,413 da ababen hawa 541 a tsawon shekarar'', in ji sanarwar.
Watan da aka fi samun nasara
Manjo Janar Edwar Buba ya ce watan da sojojin kasar suka fi samun nasara a yaƙi da 'yanbindiga a ƙasar cikin shekarar shi ne watan Mayu, inda aka kashe adadin 'yanbindiga 992.
''Sai kuma watan Fabrairu, wanda a cikinsa aka kashe 'yanbindiga 984, sai kuma watan Yuni da sojojinmu suka kashe 'yanbindiga 867'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
Sanarwar ta kuma nuna cewa watan da aka kashe adadi mafi ƙanƙanta na 'yanbindiga a cikin shekarar da ta gabatan shi ne watan Oktoba, wanda a cikinsa aka kashe 'yanbindiga 481.
AK-47 ce ta fi yawa a makaman da aka ƙwato
Manjo Janar Buba ya ce bindiga ƙirar AK 47 ce tafi yawa a cikin tarin makaman da aka ƙwato.
''Daga cikin makamai 8,216 da sojojinmu suka ƙwato daga hannun 'yanbindigar, 4,053 bindigogi ne ƙirar AK 47'', in ji sanarwar.
Daga nan kuma sai wasu bindigori ƙirar gida su 1,123, da ƙananan bindigogi 731 sai kuma harba-ruga 240.
Sojojin na Najeriya sun kuma ƙwato harsasai da yawansu ya kai 211,129, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
To sai dai duk da irin waɗannan nasarori da rundunar sojin ke ayyanawa, har yanzu Najeriya na ci gaba da fama da matsalar tsaro a yankuna daban-daban na ƙasar.
Ko a cikin kwanakin nan an samu ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ƴanbindiga a arewa maso yammacin ƙasar da ake kira Lakurawa. Kodayake masana na cewa ba sabuwa ba ce, amma sai a kwanan nan suka shahara.
Haka nan, a baya-bayan nan ƙungiyoyin ƴan bindiga sun riƙa dasa nakiyoyi a kan hanyoyin mota a jihar Zamfara, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.