Yadda ƴan bindiga suka halaka Uban ƙasar Kanya a Kebbi

Lokacin karatu: Minti 3

Al'ummar masarautar Zuru a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, na ci gaba da alhini, bayan mummunan kisan gillar da ƴan fashin daji suka yi wa Uban ƙasar Kanya, Alhaji Isah Daya, a yunƙurin kuɓutar da shi da jami'an tsaro suka yi.

Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da ceto mutum takwas a ranar Talatar da ta gabata a wani sumame da aka kaddamar da nufin ceto mutanen ciki har da marigayi uban kasar.

Ƴan bindigar dai sun kai hari ne garin Kanya da ke ƙaramar hukumar Danko-Wassagu ta Jihar Kebbin inda suka yi awon gaba da marigayin a daren Asabar zuwa safiyar Lahadi da ta gabata.

Babban ɗan marigayin Bilal Isah ya shaida wa BBC Hausa cewa mahaifinsa ya rasu ne a lokacin da jami'an tsaro suka shiga daji don ganin sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da mahaifinsa, wanda kuma a nan ne ya gamu da ajalinsa.

"Abun ya faru shine a lokacin da jami'an soji suka kewaye dajin, suna harbe harbe tsakaninsu da yan bidigar sai kowa ya watse, saura shi kadan, don haka da yan bindigar suka ga basu da wata dama ta tsira, sai suka harbe shi'' inji dan marigayin.

Haka kuma ya ce ƴan bindigar tun bayan sace mahaifin nasa ba su kira waya ba, kuma ba su nemi kudin fansa ba, sai dai ya ce wannan ba shi ne karon farko ba, da yan bindigar ke yunkurin daukar mahaifin nasu ba.

"Sun sha yunƙurin zuwa ɗaukar uban ƙasar, wannan shi ne karo na 5 suna zuwa don ɗaukarsa, wanda kuma na biyar ɗin ya zo da ƙarar kwana''

Har ila yau ɗan marigayin ya ce basu tabbatar da mutuwar mahaifin nasu ba, "sai bayan da aka ga sauran mutanen, sun dawo amma shi ba a ganshi ba, anan ne aka fara zargin ko an halaka shi, inda suka shiga nemansa, daga bisani aka ga gawarsa.

Sun ce mutuwar mahaifin nasu giɓi ne da ba wai iya ga iyali ko al'ummar su ta Zuru, da jihar Kebbi ba, rashi ne ga Najeriya baki daya, sakamakon irin alhinin da mutane ke nunawa kan kisan da aka yi wa mahaifin na su.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokaicn da shelkwatar tsaro na Najeriya ke cewar ta na samun nasara kan ƴan bindigar da suka addabi jihohin Zamfara, da Sokoto, da Kebbi, da Kastina, da Kaduna.

Ko a cikin watan Agustan 2024, sai da wasu ƴan bindiga suka kashe Sarkin Gobir na garin Gatawa, Alhaji Isa Bawa, bayan shafe kusan makkoni uku a hannusu.

Ƴan bindigar sun yi garkuwa da Sarkin Gobir ɗin ne, a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida bayan halartar wani taro a cikin garin Sokoto.

Jihar Kebbi dai na cikin jihohin arewacin Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar tsaro inda ƴan bindiga ke kai hare-hare akai-akai tare da sace mutane domin karɓar kuɗin fansa.